Washegari ranar da za'a kai kowacce amarya dakin mijinta, duk amaren suna dakin Badrah tana ta dada yi musu nasiha akan zaman aure da girman miji da sanin hakkokin miji da kula da duk abinda zai kawo bacin aure ko lalacewarsa ko tsokano fushin ubangiji.

       Badrah ta fara da cewa "Yaku 'ya'yana ina so na tunasar daku wasu nasihohi wadanda sune zasu sa ku sami nasarar zaman gidan aure a duniya har dama lahira, yaku 'ya'yana a yau zaku bar gidan da ku ka saba ku koma gidan da baku saba dashi ba, watakila ma ki fita daga garin da kika saba dashi ki koma garin da baki saba ba, yaku 'ya'yana zaku zauna da abokin zaman da baku saba dashi ba, za kuma ku wayi gari a karkashin mulkinsa to kuyi kokari ku zama bayi ku ringa jin kamar siyanku yayi, ku kuma dinga kaffa kaffa dashi don gudun saba masa, kunga in ku kai haka shi zai zama bawa gareku har sai kiji ana cewa ya zama mijin tace, kuma ba haka bane abinda mutane basu sani ba shine kyautata masa da kike yi ne zai sa ya zama haka, Annabi {SAW} yace "Dukkanin matar da take munanawa mijinta, to matansa na aljanna addu'ar Allah ya nesantata daga rahamarsa, domin shi wannan miji nata bako ne a wajenta, su suna can suna jira domin ya kusa komawa garesu" ki sani a yanzu mijinki yafi mu iyayenki da muka haifeki iko dake, wannan hukunci ne na ubangiji kuma haka yake a shari'a, domin a yanzu a ce kina zaune a gidan mijinki sai mahaifinki ko mahaifiyarki su aika ki fito daga gidan mijinki idan mijinki yace kada kije ke kuma kika je sai Allah ya tsine miki. Sannan ki guji fushin mijinki ko ki fusata shi ko ki bata masa rai kina sane, yazo a cikin wani hadisin jabir da yaji Annabi {SAW} yace "Mutane uku Allah ba ya karbar sallarsu kuma ba'a daga wani aiki nasu na alkairi izuwa sama, na daya shine gudajjen bawa har sai ya koma wajen masu gidansa, kuma ya mika kansa garesu, na biyu wanda yake cikin maye har sai ya wattsake, na uku itace matar da mijinta yayi fushi da ita, har sai ya yafe mata, kuma ya yarje mata" Don haka yin biyayya a gareshi wajibi ne in dai ba cikin sabon Allah ba, Annabi {SAW} yace "Da akwai wani mutum da za'a yiwa sujjada bayan Allah da nasa mace ta yiwa mijinta sujjada don biyayya" ku sani yaku 'ya'yana aljannarku tana kasan tafin kafar mijinku, don haka kuyi biyayya a gareshi domin ku samu aljanna, shi kuma zai yarda dake idan kuwa har haka ta faru to kin dace domin Annabi {SAW} yace "Duk matar data mutu alhalin mijinta yana mai yarda da ita, zata shiga aljanna" ku guji sabawa mijinku ta kowacce hanya kamar mijinki ya kiraki zuwa shimfidarsa amma kiki amsawa, to ki sani Annabi {SAW} tace "Duk matar da mijinta ya nemeta ita kuma taki yarda dashi to kwana zata yi mala'iku suna tsine mata har sai gari ya waye" kuma ku guji fita daga gidan aurenku ba tare da izinin mijinki ba, ku guji leke da yawon banza ko fakewa da siyayyar wani kaya ko shiga hira makwabta gidan wata mata, haka zaka ga mata sun taru a gidan wata mata duk su baro gidajen aurensu, to Annabi {SAW} yace "Duk matar data fita ba tare da izinin mijinta ba to duk wata halittar data hadu da ita sai ta tsine mata" A cikin alkur'ani mai girma Allah yana cewa "ku mata, ku lazimci zama a gidajenku, kada ku fita sai da wani uzuri mai karfi, kuma idan fitar ta zama dole, to kada kuyi tabarruj irin tabarruj din nan na mutanen jahiliyya" saboda muhimmancin zaman mace a gidan mijinta Allah yayi hani ga matar da aka saki ta fita daga gidan mijinta ko kuma shi mijin ya fidda ita har sai ta gama iddah sannan ta iya fita, amma kafin haka zata zauna a gidan miji har iddarta ta kammalu, idan kuwa aka fidda ita ko ita ta fita to tabbas an sabawa Allah kuma za'a iya haduwa da fushin Allah. Amma sai kaga mace ta fita daga gidan mijinta da niyyar zuwa unguwa ko kasuwa ko wani guri sai ka ganta ba hijabi sai mayafi shima mayafin an yafashi a kafada anbar kan a waje sai ka kasa bambance matar aure da budurwa a shigar suttura a yanzu, duk wannan yana daga cikin tabarruj ko kaga mace ta dinga tafiya babu tsari babu nutsuwa tana wurga kafafuwa kamar yadda maza suke yi, yana daga cikin tabarruj mace ta dinga kallon mijin da ba nata ba. Yazo a wani hadisi cewa wata rana Nana A'isha da Nana Hafsat suna zaune tare da Annabi {SAW} Sai wani makaho sahabin Annabi mai suna Ibni Ummi Maktum yazo, sai Annabi yace da Nana A'isha da Nana Hafsat "Ku tashi ku kauce daga gareshi" sai suka ce "Ya rasulillahi makaho ne fa ba garinmu yake ba, kuma ba ganemu zai yi ba" sai Annabi {SAW} yace "Idan shi makaho ne, ku makafi ne? idan shi baya ganinku ai ku kuna ganinsa" wannan hadisi yana nuna mana hadarin kallon wanda ba muharrami ba ga mace, ya haramta gareta ta kurawa mutumin da ba mijinta ba ido, domin yin haka yana jawo fushin Allah. Sannan ku guji kawaye domin ku matan wannan zamani kuna fifita kawaye akan mazajenku da iyayenku, shi yasa mutuwar aure tayi yawa, fadace fadace yayi yawa a gidan aure, duk ba komai bane illa daukar shawarar kawayen banza, sai kaga kawa tasan sirrin mace amma iyayenta ko mijinta basu sani ba. Kuma ku guji kari a tambayar fita unguwa ma'ana ku tambayi zuwa wani guri ku kara da wani gurin, koda kuwa kusa da gidan daku kaje ne, domin hakan cin amanar aure ne kuma hakan yana jawowa miji mummunan talauci. Haka Nana fadima {R.A.} tace "Mafificin alkairi ga mata shine kada mace ta kalli mazajen da ba muharramanta ba kuma kada ta bari mazaje su dinga kallonta, kada ta dinga yawan fice fice sai idan ya zama dole shima sai da izinin mijinta, idan kuwa ta fita ba izinin mijinta to ta tabbatar cewa tana cikin fushin Allah har sai mijin ya yafe mata" sai nasihata ta karshe a gareku itace ku guji bayyana adonku ko kwalliyarku ga wanda ba muharraminku ba, bare kuma a ce nuna tsiraici wannan abu yayi muni hakika matar da take nuna tsiraici ga wanda ba mijinta ba tana cikin fushin ubangiji, kuma idan ba'a tuba ba har aka mutu akan haka za'a shiga wuta. An karbo wani hadisi daga Abu huraira {RA} yace Annabi {SAW} yace "Nau'i biyu na mutane suna cikin 'yan wuta, ban gansu ba. Nau'i na farko sune wasu mutane masu yawo da bulalai kamar jelar shanu suna dukan mutane dasu, wato azzalumai masu zaluntar mutane ba tare da wani dalili ba. Nau'i na biyu sune mata masu yawo suna nuna tsiraicinsu, suna sanya kaya matsatstsu wadanda ke nuna tsiraicinsu a fili, suna yin nadi a kansu kamar rawani, suna karin gashi a kawunansu su fito dashi cako cako suna kaucewa hanyar Allah, suna kuma jan hankalin mazaje izuwa fitina suna kuma koyawa sauran mata irin wannan mummunan dabi'a Annabi yace "wadannan nau'i na mutane ba zasu shiga aljanna ba, bama zasu ji kamshinta ba, kuma hakika ana jin kamshinta daga tafiyar kaza wa kaza" don haka ku rike wadannan nasihohi ko kwa samu dace a nan gidan duniya dama can lahira gidan gaskiya...... "

HAWA DA GANGARATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang