Yasir yana kallon su Shukrah, yace "My sister me ya faru daku ne haka?"

       Shukrah cikin yanayin damuwa tace "Tun lokacin daka sa kafa kabar gida ko bakin gate baku kai ba Ummi ta fadi take ta jiyya har zuwa yau bata warke ba, kuma kullum bata da wani aiki sai na cewa a nemo mata sauran ya'yanta wato Yasir da Yasira, kullum cikin sunanku take, yanzu haka ma ta kai wata uku a asibiti, shine likitanta ya umarcemu damu nemo ku a duk inda kuke ko za'a samu saukin ciwon nata, mun kai wata biyu kullum sai mun fita nemanka amma ko wanda yaga wanda yasan inda kuke bamu gani ba, sai jiya muna kallon labarai a asibitin naji an ambaci sunanka a matsayin mataimakin shugaban wani kamfani shine mukaje kamfanin, to da yake yau ba aiki sai mai gadin kamfani ya kwatanto mana nan don mu zo muga ko kaine"

         Yasir cikin yanayin tausayawa yace "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! yanzu Ummi tana kwance a asibiti tsawon wata uku? me yasa baku fita da ita kasar waje ba? Ina Zayyad da Dayyab suke?"

       Shukrah tace "Ita ta hana a fitar da ita ko ina tace idan har ta bar kasar nan to ta sake yin nesa daku, kullum sa ran ganinku take, su kuma su Zayyad da Dayyab tun lokacin da suka siyar da kamfani aka zauna aka sake rabon kudin aka bawa kowa nasa, to tun a ranar bamu sake ganinsu ba har zuwa yau"

        Yasir cikin jimami yace "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! to waye a wajen ita Ummin daku ka taho ku ka barta a asibiti"

       Shukrah tace "Zayyan ne a wajenta, mu kuma kullum ni da Rayyan sai mu fito nemanku"

        Yasir yace "To ku tashi mu muje wajenta"

        Sai suka tashi gaba dayansu su shirya su fita su hau motar Yasir su tafi, Yasira da Yusrah da Shukrah suna zaune a baya, Yasir da Rayyan kuma suna zaune a gaba yayin da Yasir yake tukawa. Sun isa babban asibitin dake kasar, Shukrah da Rayyan suka yi musu jagora zuwa dakin da aka kwantar da Badrah, suna shiga sai suka tarar da Zayyan yana rike da ita tana daga kwance tana fadin "Ku nemo min 'ya'yana Yasir da Yasira, ku nemo min su ban san a wane hali suke ciki ba!"

         Zayyan yana rarrashinta yana cewa "Ummi don Allah kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki yaya Shukrah da Rayyan sun fita nemo su kamar kullum......."

        Sai su karasa wajen da sauri, Yasir ya zauna a kujera Zayyan ya tashi ya bashi, yace "Ummi gamu, ga 'ya'yanki sun dawo gareki"

       Badrah ta bude ido ta kalli Yasir, tace "Yasir!"

       Yasir yace "Na'am"

       Badrah tace "Ina Yasira?"

       Yasira ta karasa kusa da ita tace "Gani  Ummi!"

       Kawai sai Badrah ta tashi zaune ta rungumesu tana kuka tana cewa "kada ku sake tafiya ku barni komai rintsi,"

       Shukrah da Rayyan da Zayyan sunyi matukar mamakin ganin mikewar Badrah a lokaci guda, domin ta dade a kwance bata iya komai sai anyi mata, magana da kallo da ido kawai ta iya. Da likita yazo ma yayi matukar mamakin ganinta a haka ta samu sauki cikin kankanin lokaci, haka ma da ya aunata sai yaga jininta da ya hau ya sauka don haka sai aka sake mata wasu magunguna, ba tare da bata lokaci ba aka sallamesu daga asibitin.

        Yasir ya kaita gidansa yace ta zauna anan kafin ta warke gaba daya, sai Badrah tace ai ko ta warke ba zata koma ba sai tare dashi, shi kuma sai yaji a ransa kamar ba zai iya komawa gidan ba, sai dai in su zasu zauna tare dashi.

       Da daddare Yasir yana zauna a dakinsa yana aikinsa da ya saba a computer, sai Yusrah ta shiga wajen sa.

       "Yaya sannu da aiki, ashe kaima baka yi barci ba?"

HAWA DA GANGARATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang