*** *** *** ***

A raina naji ina so na auri Yusrah don haka sai na yanke shawarar neman aiki, amma ban gayawa Mas'ud ba kuma ban yanke kamfanin da zanje ba kawai na bar komai a zuciyata.

Wata rana naje gidan su Yusrah da rana sai na tarar da Bushrah a falo a zaune ita kadai bayan mun gaisa.

"Yasir nace kawo min Yasira mu gaisa amma ka ki ko?"

"Mama ba ki nayi ba kawai lokaci ne ban samu ba"

"Amma ai kai yanzu ka samu lokacin zuwa, ita baka samu lokacin kawota ba!"

"A'a mama ba haka bane, yanzu ba daga gida nake ba daga wata unguwa nake, ban zaci zan biyo ba sai kuma gashi na biyo"

"Ai shikenan duk sanda kaga dama ka kawo ta na ganta"

"zan ma kawota a cikin makon nan insha Allahu."

"To Allah ya yarda ka cika alkawari"

"Mama, Yusrah bata nan ne ban ganta ba"

"Tana ciki tana wanki"

Na shiga na sameta tana ta jibgar wanki, bata san na shigo ba sai na lallaba ta bayanta bata sani ba na cire mata dankwali, sai tayi saurin waiwayowa tana ganina sai ta saka dariya.

"Har ka ban tsoro wallahi!"

"Haba, tsoro sai kace farar kura ai nayi zaton ke jaruma ce?"

"A'a ni ba jaruma bace, zabuwa ce"

"Wato dai ke damisar takarda ce ban sani ba ko?"

Ta kyalkyale da dariya tace "Wallahi itace kuwa"

Nima nayi dariya sannan na kalli kayan wankin dake gabanta nace "Yanzu ke kadai zakayi duk wannan wankin?"

"Eh mana wannan ma ai bashi da yawa akan na wataran"

"Gaskiya bana son ki dinga wahala Yusrah, tashi ni nayi"

"Tabdijan! ba gwara ni na wahala ba da kai ka sha wahala"

"Ban haka ba, ai ya kamata duk wani da namiji ya ringa tausayawa 'ya'ya mata, tashi nayi kinji"

"Yasir don Allah ka barni nayi abina"

"Oho! na gano ki bakya so ne in taba muku kaya saboda kina tsantsami na, ba komai"

"Wallahi Yasir ba haka bane"

"To in dai ba haka bane ki tashi ki barni nayi mana"

"Ai bana so ka sha wuya ne tunda kaga kai baka saba ba"

"Tsaya kiji Yusrah wallahi sai kin tashi nayi!"

"Yasir! har da rantsuwa?"

"So nake gana za ki tashi ko kuwa, in kin tashi shikenan in kuma baki tashi ba kinga sai nayi kaffarar rantsuwar da nayi, zan ga irin son da kike min"

Sai ta tashi ta bani wurin ya zauna na fara wanki nan da nan kuwa cikin kankanin lokaci na gama muka dauka tare muna shanyawa, sai ga Bushrah tana ganina ina shanya sai ta fara yiwa Yusrah fada.

"Yanzu Yusrah don rashin kunya wanki kika bashi yayi miki?"

"Mama bani na bashi ba shi ya takura sai na bashi, har da yi min wayo don na tashi shi ya zauna yayi wankin!"

"Mama to meye aibu a ciki don nayi muku wanki, ai kun cancanta ne"

"Haka ne Yasir, Allah ya saka maka da gidan aljanna, kuma Allah ya baka abinda kake so duniya da lahira."

Mama ta juya ta tafi ta barmu muna shanya kayan wankin.

Na kalli Yusrah nayi mata gwalo nace "Wo! an shi min albarka ita ba'a shi mata ba"

"Ai in dai an shima albarka kuma albarkar ta bika, to nima albarkar zata nasheni"

"Ta yaya kenan?"

"Saboda ni taka ce, kai nawa ne, dole ne duk abinda ya shafeka nima ya shafeni, abin dadi ko akasinsa"

"Wannan gaskiya ne sarauniyar 'yammata"

"Kai ka daina fada kada sauran 'yammatan gari su ji ka!"

"To in sun ji sai me?"

"Kada su ci tarata!"

"A haba! ai in dai ina numfashi kinfi karfin wani yayi miki wani abu"

RASHIN LAFIYAR YUSRAH

Wata rana naje gidan su Yusrah ina zuwa daidai bakin kofa ina shirin shiga sai ga Yusrah ta fito a kidime, kana ganinta kasan hankalinta ba'a jikinta yake ba da alama babu kwaciyar hankali a cikin gidan, tana ganina ta rikeni cikin yanayin tashin hankali.

"Yaya! Umma ce bata da lafiya, wallahi ta kusa mutuwa ka taimaka mu kaita asibiti!"

"To ki nutsu ki kwantar da hankalinki, koma wajenta bari na kira taxi"

Ta koma cikin gidan ni kuma naje na taro taxi na dawo nazo muka dauketa muka kaita asibiti ko motsi ba tayi. Bayan an gama mata gwaje gwaje, sai likita ya rubuta mana wasu magunguna da allurai yace muje pharmacy mu ciyo, da mu kaje sai ba'a samu abinda aka rubuta duka ba, don haka sai suka turamu wani pharmacy a tsallaken titi opposite da asibitin, muka tafi da sauri mu kaje muka siyo, a hanyar mu ta dawowa garin tsallaka titi wata babbar mota ta bankade Yusrah kanta ya bugi fitilar titi muka dauketa cikin tashin hankali muka kaita cikin asibitin aka wuce da ita cikin emergency, wani babban ibtila'i kuma ko maganin da muka siyo ban kaiwa likitan ba Bushrah ta mutu.

A wannan rana naga tashin hankali nayi kuka kamar raina zai fita, haka aka yiwa Bushrah suttura aka kaita gidanta na gaskiya duk ba tare da Yusrah ma tasan inda kanta yake ba. Tsawon sati biyu da mutuwar Bushrah kullum ina wajen Yusrah amma har lokacin bata farka ba, don haka sai babban likitan asibitin ya bani shawarar dauke ta daga can asibitin zuwa nan asibitin, domin bata kulawar da ta kamata na fara aiki a kamfanin su Mas'ud a matsayin mataimakin shugaba, sannan kamfani ya bani gida da mota. Wannan shine labarinmu."

Yasir yana gama bada labarin nasu sai Yasira ta taso daga inda take fuskarta cike da hawaye ta fada jikinsa tana rausa kuka mai ban tausayi, Yasir ya riketa yana rarrashin ta, Dr. Ra'is da Dr. Karim da Mas'ud babu wanda bai zubda hawaye ba. Suna nan zaune sai ga wata nurse ta shigo da sauri.

Dr. Ra'is ya kalleta yace "Ke lafiya!"

Nurse tace "Patient mai number 22 ta farka a cikin mummunan yanayi ta ki sauraron kowa sai kiran mamanta take"

Dr. Karim ya kallesu gaba daya yace "Patient mai number 22 ai Yusrah ce!"

Sai duk su kalleshi da sauri, ai tuni Yasir ya tashi ya nufi can, Sai Dr. Ra'is yayi musu izini dasu bi bayan Yasir, haka dukkansu suka tafi can suna zuwa suka sameta nurses suna rike da ita tana ta kokarin kwacewa, tana ganin Yasir sai ta tsaya cak ta daina ko motsi ta kurawa Yasir ido.

Yasir ya karasa kusa da ita Yasira tana biye dashi, Yasir ya zauna a kusa Yusrah yana kallonta cikin yanayin tausayawa, yace "Sannu Yusrah!"

Yusrah cikin mamaki take kallon Yasir, tace "Yaya me ya faru dani? ya na ganni anan? ina mama take? ka kaini wajenta!" sai ta fashe da kuka.

Yasir ya sunkuyar da kai kasa yana hawaye ya ka sa ce mata komai.


*Alkhamis KSA*

HAWA DA GANGARAWhere stories live. Discover now