"Amma kafin na tafi ina muyi wata 'yar magana ni da ke"

     "Dani dakai?"

     "Insha Allahu"

     "To ai ba matsala"
   
     "Yusrah ki san duk wata hidima da kika ga ina yi miki, tun ranar dana fara haduwa dake na tsinci kaina a cikin tsananin begenki, Yusrah ina kaunarki ki taimaki rayuwar wannan furs unable ki ceto shi daga cikin kangin sonki wanda yayi masa katutu kuma yake neman haddasa masa hawan jini da ciwon zuciya"

      "Yasir hakika kamar yadda ka tsinci kanka a fadamar kaunata, haka nima na tsinci kaina a tafkin kaunarka, ka sani tun ranar da muka fara haduwa da kai duk lokacin dana koma gida bani da wani aiki sai tunaninka, Yasir na fada kurkukun sonka a matsayin baiwa ka dauko ni ka 'yantani ka maidani sirrin zuciyarka"

      "Yusrah ki sani ina tsananin sonki fiye da yadda kike zato, ina rokonki da ke ma ki soni kamar yadda nake sonki, duk da dai ina ganin kamar ba za ki iya sona kamar yadda nake sonki ba"

      "Haba Yasir! kasan kuwa irin son da nake maka duk da dai ba zai misaltu ba, na tabbata son da nake maka yafi kuma ya ninka wanda kake yi min sau dubu saba'in"

      "Alhamdulillah na godewa kaliki da ya bani mai sona tsakaninta da Allah kuma take tsananin kaunata fiye dani kaina"

      "To Yasir na baka amanar zuciyata ka rike ta tsakaninka da Allah, zuciyata bakuwar soyayya ce ban taba soyayya da wani da ba sai kai, don haka na danka maka amanar zuciyata karka ci amanata karka yaudareni, nima zan rike maka amanar taka zuciyar tsakani da Allah!"

      "Yusrah ki sani bani da burin cutar dake, bani da burin cin amanarki, bani da burin yaudararki, ki kwantar da hankalinki kamar tsimma a randa babban burina shine naga na kyautata miki na faranta miki na saki farin ciki!"

       "To Yasir na gode"

       "Yusrah me yasa kika yi min wannan rokon?"

       "Dalili shine samari da yawa sun nuna suna sona saboda kyauna dake rudarsu amma da sun ji labarin cewa mu talakawa ne kuma mahaifina ya mutu to daga wannan rana basa sake dawowa ba, saboda suna ganin soyayya da irinmu kamar wani nauyi ne da zai hau kansu ba gaira ba sabar"
    
      "Duk wanda ki kaga yayi miki haka to  dama ba tsakani da Allah yake sonki ba, ni kuma zan rikeki tsakanina da Allah kuma a kaina zaki san soyayya wani babban lamari ce a rayuwa"

     "Ni kuma nayi maka alkawarin ladabi da biyayya, kyautatawa da mutuntawa da girmamawa da taimakawa har ma da tausayawa"
     
      "To Yusrah na gode"

      "Nima na gode, Allah ya taimakeka cikin duk lamuranka, Allah ya buda maka a duk harkokinka"

       Irin Wadannan  addu'oin da Yusrah take yi min itace take kara min sonta kullum idan muna tare bana son mu rabu ko da na dakika daya.

      Daga nan ban kara zuwa wajen Yusrah ba sai da nayi sati daya sannan naje makarantarsu wajen karfe hudu da arba'in da biyar, ina nan tsaye har kusan biyar da minti goma sai gata nan tazo, zata wuce kawai sai ta ganni sai ta tsaya tana murza ido tabbatar ni din ne ko kuwa gizo nake mata.

       "Ba sai kin murza idonki ba nine da gaske ba gizo nake miki ba"

       Ta karaso wajen da sauri cikin tsananin farin ciki da murna tace "Yaushe ka dawo?"

       "Dazu dazun nan na dawo shine nace gaskiya dole sai nazo na ganki sannan na hankalina zai kwanta"

        "Gaskiya nayi matukar jin dadi sosai da sosai"

         "Da tunda safe zan zo to amma ina dawowa sai kanwata Yasira tace a makarantarsu an bukaci ganina to shine sai muka tafi tare"
   
        "Yasir dama kana da kanwa?"

HAWA DA GANGARAWhere stories live. Discover now