"Shirune ya biyo bayan haƙurin da suka bama juna kafin daga bisani Majeed ya nisa sannan ya kira sunanta ' a hankali Amal haƙiƙa nasan na 'bata miki rai ina mai ƙara baki haƙuri akan hakan kuma inaso ki ƙara sanya ma ranki ni cikakken mai ƙaunar kine domin na ƙaunace ki tin bakisan kanki ba na ɗaukeki na goyaki a bayana duk saboda ƙaunar da nake miki" Amal yadda nakejin sonki da ƙaunarki yake gudana a cikin jinin jikina ina tinanin bazan ta'ba jure rashinki a tare daniba.

Yaja dogon numfashi yaci gaba da cewa Amal jiya Daddy yayi mini magana akan saka ranar Auren mu da yayi, wannan dalilin ne ya sanya nace zanzo na sameki na baki haƙuri kuma mu tattauna akan yadda hidiman namu zai kasance, Yanzu ke a son wadansu irin programs kikaga zakiyi kuma nawa kike buƙata ɗan yin programs ɗin ki faɗamin ko nawa kike buƙata na rubuta cheque na baki saboda zanyi dukkan shirye ~ shiryena a Yola ne.

"Gyara zama tayi fuskarta cike da murmushi ta ƙura masa ido karkaɗa ƙafa tayi sannan tace hmm Yaya Majeed kenan ai tuni na rufe shafi da babin soyayya da zancen aurenka a cikin rayuwa da zuciyata, Yaya tin lokacin dana fuskanci hankalinka baya kaina na cire soyayya da maganar aurenka na 'ajiyesu a gefe in taƙaita maka zancen ma na gama yanke igiyar baikonka a kaina kuma na haɗu da wanda nakeso, dan haka ina mai baka haƙuri a karona farko.

Tayi shiru fuskarta ɗauke da farin ciki   tace Yaya tin lokacin da Daddy yace ya yanke ranar Auren mu naso na faɗa masa bana ƙaunar aurenka 'amma na kasa faɗa masa sakamakon yadda ya sameni fuskarsa a ɗaure kuma naga a fusace yake," nasan kana cikin damuwa kayi haƙuri dajin wannan fira mara daɗin sauraren, tabbas nasan jinsa bazai ta'bayi maka daɗi ba ina roƙonka dakayi haƙuri ka janye auren nan naka ka barni na auri wanda nakeso. Tana gama faɗin haka ta nufi part ɗin Umma sai da taje bakin ƙofar shiga ta tsaye ta ƙyalƙyale da dariya Allah ya baka haƙuri.

Ya bita da kallo zuciyarsa cike da baƙin ciki dafe kai yayi ya jingina jikin kujera bakinsa na furta kalmar "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Allahumma 'ajirni fi musibati wa'aklifni kairan minha" ( wannan addu'ar tana ɗaya daga cikin addu'o'i masu falalar da akeso mutum ya rinƙa mai ~ mai tawa lokacin daya tsinci kansa cikin damuwa ko baƙin ciki ko abun 'bacin rai ya sameshi Allah ya datar damu baki ɗaya ).

Amal la'bewa tayi jikin ƙofa tana hango Majeed dariya takeyi masa ta ciki tana faɗin Allah na gode maka daka nuna mini tashin hankali da hawayen Majeeed dama haka Majeed yake ƙaunata ? Tabbas yayi kuskuren da bazaiso sake mai ~ maita wani irinsa ba.

"Daƙyar ya iya controling kansa ya lalla'ba ya tashi tsaye ya nufi part ɗinsa yana tangaɗi kamar zai faɗi.

A can gidan Hajiya Hindu kuma su Mee'ad manyan ƙawayen Amare shirin yadda bikin zai kasance kawai sukeyi, Mee'ad ta zama babbar ƙawar Ummee komai Ummee zatayi sai Mee'ad ɗin tasan da abun, Hajiya hindu babu abinda takeyi sai jin daɗi da godiya ma ubangiji domin babu wanda ya kaita jin daɗin sakewan da Mee'ad ɗin tayi.

Amal kai tsaye gefen Ummanta ta zauna ta ƙyalƙyale da dariya irin najin daɗin nan Hajiyata Albishirinki!   Goro fari tass Uwata, ta sake ƙyalƙyalewa da dariya kafin tace na sanarma Majeeed na sami mijin auren daya fishi..........ta kwashe yadda sukayi ta sanar da Umman nata.

Umma tayi shiru naɗan wasu seconds ta ce Mamana tabbas naji daɗin faɗa masa hakan da kikayi saboda baki rufe masa kin daina ƙaunarsa ba dan haka bakida haƙƙi akan hakan, amma kinaga Daddynku zai iya yarda da sabon zancen da kikazo dashi ? Ta ce Umma ki daina cewa bazai yarda ba ni nasan zai yarda Amma ki fara samun Hajiyar su ki sanar da ita abinda ke shirin faruwa, ni kuma zan sanar ma Areef ya turo Hajiyarsa ta sami Daddy da zarar an gama bikin Laila, Umma ta ce kirki sanarma Areef maganar ya turo kedai ki shaida masa kin fasa auren Majeeed sai kuci gaba da soyayya kinga da zarar na shawo kan problem ɗin saiki sanar masa ya turo cikin sauƙi,"  Ta buga tsalle wow kyakkyawan shawara hakan ma za'ayi bari na kira Areef ɗin na shaida masa komai.

Tin lokacin da Majeed ya koma part ɗinsa hankalinsa ya kasa kwanciya sai tinane ~ tinane yake ya ɗauko phone ɗinsa fuskarsa cike da tashin hankali number Hajiya Hindu ya kira bata ɗauka ba ya ƙara kira harya katse bata ɗauka ba, tsaki yaja sannan ya fara tinanin wazai kira ? Nan Mommyn Mee'ad ta faɗo masa a rai ya lali'bo number ta ya kira itama bata ɗauka ba, wayar Mommy yana katsewa kiran Hajiya Hindu na shigowa hannunsa na rawa ya kara wayar a kunnensa Sallama Hajiyar tayi murya ƙasa ~ ƙasa ya 'amsa yaja dogon numfashi ya gyara zama kafin ya ce Hajiya barka da wannan lokacin  ta ce yauwa barka dai ya baka da lafiyane naji muryarka haka a'ah lafiyata klau kawai wata matsalace ta kunno! A firgice tace matsala kuma ? Wacce irin matsala kenan ? Ka faɗamin koma wacce matsalace ina saurarenka, Yaja numfashi Hajiya dama Amal ne tace bata ƙaunata kuma tana roƙon a fasa auren mu domin akwai wanda takeso ya ƙarasa maganar muryarsa na sarƙewa.

A firgice Hajiya tace wani irin fasa aure kuma bangane ba ? shin ina ita Amal ɗin take ? Ina ita Suwaiban ma take ? Kuma waye ya ɗaure ma Amal gindin yi maka cin fuska da faɗa maka wannan zancen ? Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un!..









pls

Follow

Share

Vote

Comment

Fisabilillah 🙏🙏🙏.

MEE'ADOù les histoires vivent. Découvrez maintenant