Chapter 15

73 1 0
                                    


💫💫💫💫
          _*MEE'AD*_
                   💫💫💫💫
*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*THE BOOK IS WRITTEN*

*BY*

*_HAUWA IBRAHIM MISAU_*

%% wattpad__@hauwancyy44 %%

 

        JINJINA & SADAUKARWA

Na jinjina na kuma sadaukar da wannan littafin na gareki babbar aunty SAFNA ALIYU JAWABI Allah ya kara daukaka, basira da kuma fasaha ya kuma kareki da sharrin dukkan mai sharri. Ameeen .
                       
 

               
**** Pls don't forget to vote, share & comments 👌 love u fan's 💯%.
          
                         

                   

                   
  

                       25 ~ 26

_______ Zuciyarsa faal farinciki ya karasa gurin da suke tsaye fiskarsa na fitar da annuri, Amal ce ta dago kai gamida kura masa ido, wani kyakkyawan murmushi ya sakar mata kafin yakai dubansa ga Amrah wacce idonta ke kansa itama murmushi ya sakar mata, kafin ya bude baki cikin sassanyar murya yace barkanku da wannan lokacin yan tagwayen kannena,"

Cike da zumudi Amal tace barkan kadai Yaya Majeed, kura mata ido ya karayi kafin ya sauke wani sassanyar ajiyan zuciya, cikin murya mai kama da rada ya kira sunanta Amal! Dago kai tayi fiska a sake tace na'am Yaya, shiru yayi nadan wasu lokuta kafin yace nayi miss dinku sosai, Murmushi tayi a karo na 2 kafin tace Yaya muma munyi miss dinka sosai fiye da yanda kayi namu.

Amrah dake tsaye a gefensu sai yanzu tayi magana cewa take Yaya Majeed ka ganeni kuwa ? Majeed yadan sukuyar dakai gamida karema Amrah kallo kafin ya jijjiga kai yana fadin gaskiya ban wani ganeki sosai ba ai nayi tsammanin kawatace🙄 yatsina fiska Amrah tayi kafin tace wacece kuma kawarka kuma ?"

" Murmushi Majeed yayi cikin alamun ko in kula yace mata wacce kika sani din nan dai  Amrah ta dan bata fuska kafin tace ok na gane wai Mee'ad kake nufi kenan ?"

Ai nayi tsammanin baka ganeni bane, Ya bita da kallo kafin yace ai ban ganeki ba har sai da nazo kusa daku kafin na fahimci ba Mee'ad din bace, ya kai dubansa ga Amal wacce take ta faman murmushi kamar an bata kyautar kujeran Hajji, kafin yace Kanwata ban gane wacce kuke tare da itan ba, Amal tace haba Yaya baka gane Amrah Aunty ba ?

" Ya jinjina kai da alamun ya tuna da wacece a gabansa cewa yake kai haka Amrah ta girma sosai ? Murmushi Amal tayi kafin tace ga 'alama a bayyane,"

"Twins ne suka karaso wajensu da gudu suka rungume Majeed cike da murna da zumudin ganinsa,"

Majeed yace wash na gaji ya kamata mu dauki hanyar gida faah, ya karasa maganar yana kallon Amal, cike da zumudi Amal din tace ya kamata kam gaskiya dan kuma naga kamar ka gaji, murmushi yayi kafin yace barina shiga moto sai kun isoni, Yana gama fadin haka ya nufi kofar moton dake gefensu.

"Baki dayansu moto suka shiga cike da farin cikin suka nufi gida.

                 %%%%%%%%%%

***** A jere motocin suka shigo harabar gidan bayan mai gadi ya bude get,"

"Parking din motocin sukai kafin su fito harabar gidan, Majeed ne ya fito fuskarsa dauke da murmushi yayinda Amal ke tsaye bisa gefen damanshi, sai murmushi itama take, tare suka shiga cikin gida, kallo daya zakayima fuskokinsu kasan suna cikin farin ciki baki dayansu.

Suna shiga cikin gidan Majeed part dinsa ya nufa domin ya watsa ruwa yadan huta,"

Bayan wasu mintoci baki dayansu sun hallara a darning Majeed da Mee'ad kawai suke jira, Majeed bai wani dauki lokaci ba ya karaso yana fadin sorry na bata muku lokaci ko ? Hajiya Hindu dake zaune cikin falo tace ka bata musu lokaci dai 🙄 bude ido Majeed yayi kafin ya kyalkyale da daria yana fadin ke Kuma wayace kisanya baki a wannan maganar 😜?

"Hajiya Hindu tayi murmushi kafin tace Aminace tace na sanya baki domin na lura kafi ganin girmanta fiye da nawa girman 🤩 murmushi yayi kafin yace Allah yahuci zuciyarki Amaryata ya karasa maganar yana mai lankwashe kai, dariya sukayi baki dayansu kafin ya janyo kujera ya zauna ya fara binsu da kallo daki2,"

Sai da ya kare kallon da yake musu kafin ya nisa yace Mommy banga karamar Kanwata ba, murmushi Mom tayi kafin tace tana sama wai kantane ke ciyo, ya dafe kansa kafin yace wash! Tin yaushe ta fara ciyon kai din ? Umma ta amshe da cewa tin jiya batajin dadi sosai, Amma bari Amal ta dawo daga rakiyar da tayima Amrah take tayo kiranta".

Mee'ad kwance take bisa gado sai juyi take zuciyarta faal fargaba ba abinda takeyi sai tinani ta Kuma rasa abinda ke damun ta, tashi tayi ya zauna ta fara kiran sunayen Allah tana neman taimakonsa, bata wani dade da tashi ba taji dukkan damuwarta ta yaye, Alhamdulillahi tace kafin ta fara shirin fita falo jikinta 'a sanyaye.

Amal ce ta shigo cikin falon da sallama bayan ta raka Amrah, sallaman da tayine yaja hankali dukkan mutanen dake falon musamman Majeed daya mace cikin soyayyarta,"

"Amal ta sake wanka ta kuma canja shige domin kuma a yanzu sanye take cikin wasu riga da siket na atamfa yayinda ta daura karafin gyale bisa wuyanta sai murmushi take, idon Majeed kurr! A kanta baya ko kiftawa har ta karaso kujeran dake gefensa ta zauna, sai a lokacin ya sauke ajiyar zuciya yana mai kara binta da kallo a hankali ya furta kinyi kyau sosai Kanwata, tnx kawai Amal ta fadi kafin ta janyo plate din gabanta ta fara zuba abinci, damin naga 'alamar yuwa takeji sosai, wannan kenan!.

Sunyi kusan 10min zaune a kan darning kafin Mee'ad ta fito, hohohoho! Mee'ad kenan saurauniyar kwalliya, tana bude kofar room dinta wani kamshin sassanyan tiraren ya fara bin iska izuwa falon kasa, saukowa take cikin taku mai aji irinna mata masu aji,"

"Hancin Majeed ya jiyo wani daddadan kamshin tirare, daga kai yayi yabi wajen da yaji kamshin tiraren da kallo, masha Allah naji Majeed yana fadi fuskarsa sai annurin farin ciki da ganin yar uwar tasa yake",

Mee'ad dake saukowa bisa steps din banne dake shimfide tsakanin falo da bed's dinsu, sanye take cikin wata doguwar riga yar kanti mai launin black blue  kanta daure yake da wani lallausan white din kallabi gashin kanta yasha gyara kasancewa tayi daurin kallabin daya fito da gashin nata kafarta sanye take da white flat shoes, sai kamshi take zubawa abinta, ta kumayi kyau sosai abin ba kama kafar yaro.

Mee'ad tana karasawa falon kai tsaye wajen da Hajiya Hindu ke zaune ta nufa fiskarta dauke da murmushi take fadin an yini lfy Hajiyar mu ?  Murmushi Hajiya Hindu tayi kafin tace lfy klau diyar albarka ya jikin naki ?"

Da sauki tace kafin ta nufi darning, gaisar dasu Daddy tayi sukayi mata sannu da jiki kafin ta kai dubanta zuwaga Majeed dake zaune hannunsa rike da waya da alamar harya gama cin abincin kenan, tin daga kasan kafarsa ta fara kallonsa sanye yake da flat din bakin takalmi, yayinda jikinsa ke sanye da  wasu kananun kaya jeans da shirt sunyi masa kyau sosai,"

Sai da ta gama kallonsa a fakaice kafin tayi magana cikin sassanyar murya tace Yaya an yini lfy ? Ya hanya kuma ? Majeed ya amsa da Alhamdulillahi fuskarsa dauke da murmushi, daga wannan maganar Mee'ad bata Kara furta cewa komai ba, yayinda su kuma mutan gidan sai hirarsu sukesha.........







Mai karatu biyoni kasha lbr 💯










Pls vote, comments and share Fisabilillah 🙏🙏🙏🙏🙏.

MEE'ADWhere stories live. Discover now