Chapter 16

87 2 0
                                    

💫💫💫💫
          _*MEE'AD*_
                   💫💫💫💫
*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*THE BOOK IS WRITTEN*

*BY*

*_HAUWA IBRAHIM MISAU_*

%% wattpad__@hauwancyy44 %%

 

        JINJINA & SADAUKARWA

Na jinjina na kuma sadaukar da wannan littafin na gareki babbar aunty SAFNA ALIYU JAWABI Allah ya kara daukaka, basira da kuma fasaha ya kuma kareki da sharrin dukkan mai sharri. Ameeen .
 

√√√√√ MEE'AD fan's kuyi hakuri da rashin post akan time, sbd wasu dalilai. √√√√√√

         
     
**** Pls don't forget to vote, share & comments 👌 love u fan's 💯%.
          
                         

               

                   
  

                          27 ~ 28

Bayan sun kammala lunch baki dayansu a falo suka yada zango, sai hiran yaushe gamo suke tare da Majeed, haka suka kasance har lokacin sallah yayi anan kowa ya nufi bed dinsa yayinda su kuma mazan suka nufi masallaci.

" Bayan sun idar da sallah isha gida suka shigo baki dayansu dan yin hirar yaushe gamo a karo na biyu kafin suje ga darning saida suka sha hirarsu mai dadi sosai.

Amal na hango zaune kusa da Mee'ad sai murmusawa take, fuskarta cike da farin ciki ta dago fiska ta kalli Mee'ad din kafin tace Bloody ashe kin fini gaskiya dama haka Yaya Majeed ya hadu sosai babban gaye bashida makusa kota ina gaskiya, ihm! Ya burgeni har cikin zuciyata dalilin da yasa naji kamar zuciyar tawa ta fara kamuwa da kaunarsa marar adadi,"

Mee'ad ta dubi Yayartata hade da jan dogon numfashi gami da daura hannunta daya bisa kafadarta ta kuma kirkiro murmushi kafin tace ki kwantar da hankalinki sisina idan kina son Yaya Majeed ne kar kiji komai nima zan zamo mai mara miki baya kinga sai muyi yakin tare ko ?"

Amal tace sosai ma! naji dadi da kikai saurin fahimtata na kuma gode sosai, murmushi Mee'ad ta kuma yi kafin tace bari naje kitchen na dama tea kinji sistona, Amal tace to sarkin tea saikin dawo, bata tsaya cewa komai ba ta nufi kofar dazai sadata da kitchen din.

" Bayan sun kammala cin abincin dare, kowa part dinshi ya nufa dan shirin kwanciya, domin mutan gidan da wuri suke kwanciya,"

Amal ce zaune bisa kan gado tana faman chat da wayarta, Yaya Majeed ne yayi knocking kofar dakin ta ce waye ? Baiyi maganaba ya tura kofar ya kutsa kai cikin kawai, zaune ya sameta jikinta sanye da wata doguwar sleep mara nauyi shiga yayi da sallama kafin ya sami kujeran dake gefen gadon ya zauna ya zuba mata ido,"

" Yakai 15min da zama baice komai ba, itama shiru tayi batace komai din ba, yajaa dogon numfashi cike da kulawa ya dubeta kafin yace kanwata farin cikina kuma abar alfaharina dftn kin wuni cikin koshin lfy ? A yangace ta dagokai tana yamutsa fuska kafin tace lfy alhmdlh, ya gajiyar hanya kuma ? Murmushi yayi kafin yace alhmdlh,"

"Itama murmushin tayi kafin ta haye kan gado sosai ta fara gyara blanket tana shirin kwanciya Majeed ya mike tsaye yana fadin ah kwanciya zakiyi kenan ?

MEE'ADWhere stories live. Discover now