21

56 3 0
                                    

Ansar ya ci gaba da tafiya akan babur ɗinsa cikin lokuna yana godiya ga Allah da ya tsare shi daga sharrin wannan mota, har ya ƙarasa inda zai koma babbar hanya, bisa ga mamakinsa sai yaga wannan mota ta gifta, don haka ya ɗan jira sai da tayi nisa sannan ya fito ya bi bayanta nesa kaɗan da ita don kada su fahimci yana biye da su.

Sai a lokacin ya kula a jikin gilashin bayan motar an rubuta Junior don haka sai Ansar yayi ajiyar zuciya sannan yayi murmushin ƙarfin hali kawai.

Haka dai Allah ya kiyaye shi ba su ganshi ba har yaje inda zai je.

Da daddare ya kwanta gaba ɗaya jikinsa a mace sabo da ya sha zirga zirga ga gajiyar azumi.

"Yaya, ɗazu wannan yar ajin taku maryam ta zo, ta zo ta gaishe da umma kuma har ma tsaraba ta kawo min ta wata atampa mai kyau da takalmi da mayafi, dukansu kalar pink, my best colour, sannan ta bawa umma wata sarƙa mai kyau... Gaskiya tana da mutunci, tare da mamansu ma suka zo..." Khadija ƙanwar Ansar ta faɗa wadda shi kansa bai san lokacin da ta shigo ɗakin nasa ba.

"Allah sarki maryam, could you imagine ko a makaranta mun kwana biyu ba muyi magana ba, sabo da mostly bana zama indai ba lokacin da ake lecture ba..."

"Ayya, amma baka kyauta ba, tana da mutunci ni ba don Hafsa ta riga ta ba aida ka aureta wallahi na san ba za ta yi maka musu ba"

"To tashi ki je ki kwanta, bacci kike ji."

"Lallai yaya Ansar, daga faɗar gaskiya?"

"Khadija, kije ki kwanta please."

"An gama!"

Khadija ta juya tana mai murmushi.

"Okay kinga wannan shi ma pink ne ki haɗa da shi."
Ansar ya faɗa lokacin da yake miƙa hannunsa daga kwance ya buɗe dirowa ya sanya hannunsa yana lalube daga bisani ya ɗauko wani ƙasaitaccen agogo na mata.

Saboda murna sai kawai Khadija ta fashe da kuka ta sumbaci hannun yayan nata, ta fita tana rawa tana mai nufar ɗakin ummansu da gudu tana nuna mata.

Ansar ya lumshe ido yayi murmushi, ya tuna cewa wannan agogon don Hafsa ya siya amma ga shi ya bawa ƙanwarsa kuma tayi murna sosai fiye da yanda yake tsammani.

Sai kawai ya ɗauko wayarsa da zummar kiran Hafsa, bisa ga mamakinsa sai yaga 3 missed call dubawar da zaiyi sai yaga Maryam ce ta kira shi.

Ya kirata ya ji wayar tasa babu kuɗi, kamar ya ranto a katinsa na waya, amma kawai sai ya ga babu buƙatar hakan, ya ɗan yi jim yana tunanin ina kuɗin wayar suka tafi, amma dai bai iya tunowa ba, sai kawai ya mantar da tunanin ya lumshe ido yana mai saƙe-saƙen abin da ya kamata yayi.

★      ★       ★

Yan uwa muna bada haƙurin rashin yin rubutu tsawon lokaci, ayi haƙuri hakan ya faru ne sabo da uzurai da yawa amma insha Allah wannan matsalar ta kau.

Sai kun ji mu a rubutu na gaba.

Naku mai son faranta muku..
Naseeb Auwal

Me za ka iya cewa dangane da wannan labari?

Me za ka iya cewa dangane da wannan labari?

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now