2

163 7 4
                                    

Alhaji Nasir tsohon ma'aikaci ne, wanda duk wanda ya sanshi ya sanshi da tsantseni gami da gudun duniya. Mutum ne mai mutuƙar kamun kai da kuma kawar da kai daga dukkanin abubuwan da basu da amfani a rayuwa, ya kasance ba ya ɗaukar komai da wasa, komai nasa da gaske yake yi. Duk inda aka faɗi Alhaji Nasir a yarintarsa ba za'a rufe baki ba tare da ambaton Sambo ba, tun suna yara suka taso tare kuma iyayensu aminai ne, harma mutane da dama suna tsammanin cewa Alhaji Sambo ɗan'uwan Alhaji Nasir ne na jini. Mutane da dama suna ƙara shiga cikin ruɗani domin hatta mahaifin Alhaji Sambo a gidansu Alhaji Nasir ya taso.

Lokacin da suke makaranta tabbas har wata inkiya ake musu da ƴan biyun Angelina. Sunan wata baturiyar malamarsu kenan wadda take koyar da su a wannan lokaci. Ana kiransu da ƴan biyunta kuwa saboda kaf ajinta koma duka makarantar babu ɗaliban da take ji da su irin wayannan guda biyun, hakan kuwa ya samo asali ne sabo da ƙoƙarinsu da jajircewarsu wajen karatu...

Bayan sun kammala karatu ne gwabnati ta ɗauki nauyin su ta fitar da su waje zuwa ƙasar da take mulkin mallaka wato Biritaniya (England). Inda acan sukai karatu a jami'ar Oxford kuma suka fita da sakamako mai mutuƙar kyau.

Ganin haka yasa gwabnatin England ta ƙudiri aniyar riƙesu, amma sai aka samu saɓanin fahimta, inda shi Alhaji Nasir ya tubure yace zai dawo gida Nigeria don hidimtawa ƙasarsa, musamman sabo da ƙasar bata jima da samun ƴanci ba, shi kuma Alhaji Sambo yace bazai dawo ba, domin kuwa babu komai a cikin Nigeria sai tarin matsaloli, don haka bazai dawo ba sai lokacin da Ƙasar ta gyaru.

Haka Alhaji Nasir yayi ta jan hankalinsa har ya yarda cewa shima zai dawo gida Nigeria.

Ya rage dawowarsu saura wata guda sai aka wayi gari da wani mummunan labari. Na wasu sojoji da suka kashe Sir Ahmadu Bello, Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa da wasu jiga-jigai a Nigeria, a shekarar 1966 Sha biyar ga Watan January. Tabbas wannan labari ya tayar da hankalin Alhaji Nasir da Alhaji Sambo fiye da tsammani. Domin shi Alhaji Nasir ma sai a asibiti ya tsinci kansa.

Wannan labari shi ne musabbin rabuwar kan Alhaji Nasir da Alhaji Sambo, inda shi Alhaji Sambo yace babu dalilin da zai sa ya dawo gida Nigeria, shi kuma Alhaji Nasir yace babu dalilin da zai hanashi komawa gida Nigeria.

Abu kamar wasa sai wannan dalili da kuma wasu dalilai dabam suka sanya Alhaji Nasir ya daina kula Alhaji Sambo. Dalilin sun haɗa da ganin hotunan Alhaji Sambo da yayi da wasu Yammata a club da kuma gidan giya. A wannan rana Alhaji Nasir yayi kuka kamar ransa zai fita, kuma sai ya zartar da cewa lallai wannan shi ne dalilin da yasa Alhaji Sambo yake son zama a ƙasar England. Bai ƙara koda kula Alhaji Sambo ba, sai ranar da jirginsu zai tashi. Lokacin Alhaji Sambo yazo idonsa cike da kwalla, ya tsaya a gaban Alhaji Nasir wanda dama tunda ya hango Alhaji Sambo daga nesa sai kawai ya sunkuyar da kansa ƙasa. Alhaji Sambo yazo kan Alhaji Nasir ya tsaya, sannan ya nisa yace "Kaf duniya, bani da wanda ya wuceka, ka sani tun lokacin da iyayena sukai hatsari suka mutu na komo gidanku, tare muke ci muke sha, muke kwana... Amma ace yau baka da abin ƙyamata kamata, tabbas hakan akwai ciwo, shin idan ka guje ni wazai riƙe ni? Shin idan na rasaka wa zan kalla a matsayin jini na? Ko kuwa kaima ka ɗauki maganar da mutane suke akan cewa bani da dangi? Haba Nasir idan wani abu nayi ka gaya min mana... Sannan..."
Sai kawai Alhaji Sambo ya fashe da kuka. Har yanzu kan Alhaji Nasir yana ƙasa, wani abu ya turnuƙe masa zuciya, idanuwansa suka ciko da kwalla, bugun zuciyarsa ya ƙaru, wani tunani ya rinƙa zarya a cikin ƙwaƙwalwarsa. Yana ɗago kai suka haɗa ido da Alhaji Sambo sai ya kasa jurewa yayi jifa da jaridar hannunsa ya mike ya rungume ɗan'uwansa Alhaji Sambo. Suka daɗe a haka suna koke-koke suna ƙoƙarin lallashin junansu. A haka har lokacin tashinsu yayi. Da kyar jami'an filin jirgin suka lallashe su suka rabasu.

Sai da jirginsu ya daɗe da tashi sannan Alhaji Sambo ya iya barin wannan filin tashin jirgi.

Bayan rabuwarsu sun ci gaba da zumunci ta hanyar rubutun wasiƙa, domin wancan lokacin babu wayar hannu. Har sukai aure inda shi Alhaji Nasir lokacin yana Ɗan Sanda ya auri wata ƴar'uwarsa mai suna Juwaira yar asalin jihar Maiduguri, shi kuma Alhaji Sambo suka haɗu da wata yar asalin jihar Kaduna mai suna Sadiya a can England wadda ita haifaffiyar ƙasar ce amma iyayenta dukansu yan kaduna ne.

Bayan aurensu da shekara bakwai sai Alhaji Nasir ya samu ƙaruwa da yaro namiji, aka sanya masa suna Ansar. A wannan lokaci Alhaji Sambo ya taso takanas ta kano yazo har Nigeria shida uwar gidansa Sadiya, suka zo da sha tara ta arziki kuwa. A lokacin Alhaji Nasir yake gaya masa cewa ya gaji da abubuwan Nigeria domin yaga alamar babu ranar da za'a kawo gyara, inda Alhaji Sambo ya bashi shawarwari amma ko ɗaya Alhaji Nasir bai ɗauka ba, domin sun saɓa da nasa ƙa'idojin.

Bayan shekara huɗu da haihuwar Ansar shima Alhaji Sambo sai ya samu haihuwa, inda ya haifi santaleliyar ƴarsa aka sanya mata sunan mahaifiyar Alhaji Nasir wato Hafsa. Alhaji Nasir bai samu damar zuwa ba, sai dai ya aika da kyaututtuka wayanda basu ƙarasa ba, sun haɗu da halin wasu yan Nigeria kafin su fita daga ƙasar.

Alhaji Nasir a matsayin ɗan sanda an sha yi masa barazana da rayuwarsa sabo da gaskiyarsa amma bai taɓa tunanin chanja shawara ba, a ƙarshe da yaga abin yafi ƙarfinsa sai ya haƙura inda ya ajiye aikin ya koma koyarwa a wata makarantar gaba da sakandire (Higher institution), itama daga ƙarshe ya ajiyeta ya koma harkar kasuwanci da rubuce rubuce a jaridu don wayar da kan mutane da kuma yaƙi don neman ƙwatowa kai ƴanci daga mulkin kama karya. Ai kuwa take sunansa ya bazu a ko'ina bama a iyakar Nigeria ba, har a ƙasashen ƙetare. Hakan yasa ya rinƙa samun kyaututtuka mabanbanta a matakai dabam dabam na duniya, musamman daga ƙungiyoyin sa kai.

Bayan tsawon shekaru yana wannan aiki ɗif sai aka nemi rubutunsa aka rasa, mutane sukai ta cigiya inda a ƙarshe ya bayyanawa duniya cewa ya gaji da wannan aiki, domin baiga alamar duniya ta shirya taimakawa talakawa ba, kuma yanzu shekaru sun ja don haka abin da yafi dacewa da shi, shi ne ya koma ga Allah ya ci gaba da bauta har zuwa lokacin da zai koma ga mahaliccinSa.

Wannan rubutu nasa ya yiwa wasu daɗi kwarai musamman waƴanda ya takurawa da caccaka. Wasu kuwa da suke ɗaukarsa a matsayin madubin dubawar talaka kwata-kwata abin bai musu daɗi ba.

A wannan lokaci ne kuma Alhaji Sambo ya yanke shawarar dawowa gida bayan nemansa da turawan England sukai da cewa suna so ya cigaba da zama a can. Amma yaƙi amincewa domin an nuna masa wasu hotuna wayanda akace masa tun suna matasa wayannan hotunan aka nunawa Alhaji Nasir harma ya daina yi masa magana.

Kuma wadda ta haɗa hotunan da kanta ta bayyanawa Alhaji Sambo hakan tare da neman gafararsa. Haɗe da rubuto letter ta bayar da haƙuri tace a bawa Alhaji Nasir. Tabbas tana tsananin son Alhaji Sambo ta yanda ba zata iya rabuwa da shi ba, kuma duk da wannan tuggu da ta haɗa a ƙarshe buƙatarta bata biya ba, domin Alhaji Sambo bai aureta ba...

Alhaji Sambo ya sauka a Nigeria a shekarar 2005 a lokacin Olesagun Obasanjo ne shugaban ƙasa, yayin da Mallam Ibrahim Shekarau yake matakin gwabnan jihar kano yin sa na farko.

Tabbas manyan ƙasar sunyi maraba da dawowar Alhaji Sambo, a wannan lokaci ƴarsa Hafsa ta kai shekara 14 inda shi kuma Ansar yake gab da cika shekara sha takwas. Saidai saboda girman jikin Hafsa tsaf mutum zai zaci ta zarce 18.

Zamu dakata anan.
Me zaku ce dangane da wannan shifida?
Ko akwai wani abu da kuke tunanin zai faru?

Sai kuma a rubutu na gaba.

BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now