10

37 2 0
                                    

Tafiya take amma gaba ɗaya hankalinta ba ya jikinta, wani baƙin ciki ya dunƙule ya tattare a zuciyarta, idanunwanta suna kan hanya amma abin da take iya gani kawai shi ne abin da take tunani wato musayar murmushi data gani tsakanin Ansar da Maryam. Ji take kamar ta koma ta shararawa Maryam mari. Ranta kuma yana daɗa ɓaci idan ta tuno da cewar ta gabanta yazo ya wuce ba tare da ya ce mata komai ba.

Taja ta tsaya a gefen hanya, idanuwanta suka kai kan wata kujera, nan take taje ta zauna akan wannan kujerar, bata tsoron hadarin daya gangamo wanda hatta Ansar abin da ya sanya shi hanzarin tafiya gida kenan.

'Idan har da gaske kulawar yake bani, kuma idan kulawar ta soyayya ce ai kamata yayi yanda baya son wannan hadarin ya saukar da ruwan da zai taɓa shi nima ya so hakan a tare da ni, amma sai kawai ya tafi ya barni... Lallai akwai alamar tambaya a cikin soyayyar da yake ƙoƙarin cewa akwai ta.' Hafsa ce ta faɗa a zuciyarta.

A sannan ne ta ankara an fara ruwan sama, ilahirin kewayen da take a jike yake amma ko kaɗan ita ruwa bai taɓata ba, ta ɗaga kai sai taga kawai an saka mata lema. Bisa ga mamakinta kuma wanda ya sanya mata lemar don kareta daga ruwa shi ɗin ya jiƙe sharkaf...

"Junior, ya akai ka bari ruwa ya jiƙa ka haka?" Hafsa ta tambaya tana ƙoƙarin miƙewa, "Please let us have a better place." Ta faɗa lokacin data gama miƙewa.

Suka tafi tare a ƙarƙashin wannan lemar kafaɗar su tana gogar ta juna, suka nufi wata theatre wadda take a bude suka shiga ciki.

"Allah zai kamani idan har ina kallo na bari ruwa ya zane wannan kyakkyawar halittar..." Junior ya fada yana murmushi. Baƙi ne amma ba can can ba, sannan yana da dogon hanci gami da dara-daran idanu wayanda sukai dai dai da fuskarsa domin itama tana ɗan faɗi. Kana ganinsa kasan ɗan gayu ne, gashin kansa kuwa yasha aski irin na ƴan zamani, an rage gefe da gefen gashin kan.

"Yau ina yayan naki?" Junior ya tambayi Hafsa ganin cewa bata kula maganarsa ta farko ba.

"Hmm, ya tafi."
"Ai ni ban taɓa ganin mutum irinsa ba, kawai kabi ka takurawa yarinya kullum kana tare da ita, ko ƙawaye kaƙi barinta tayi, yanzu haka da yawa daga yan ajin cewa suke kinada girman kai, ni kuma ina bayyana musu ba laifinki bane, laifin yayanki ne."
"Nima bana son hakan da yake min, amma abin da yasa ban damu ba shi ne tunda kulawa ce hakan babu komai."
"But as an adult, you need some space, kuma interaction with different people kansa zai baki gogewa a rayuwa, wannan gogewar ita take bambance wanda yayi jami'a da wanda bai yi ba."
"Kuma wallahi you are right... Kawai shi Yaya Ansar ne is kind of old modern person ɗin nan. Amma ai ya kamata ace yasan a generation ɗin da muke rayuwa..." Hafsah tayi shiru sakamakon hango driver ɗinta da tayi nesa kaɗan da ita yana waya cin ƙarfinsa. Tayi murmushi ta kalli Junior tace masa bye-bye, sannan ta wuce tana mai sassarfa bata ankara da cewa waje ruwa ake tafkawa ba...

Tun kafin ta ƙarasa bakin motar driver ya fito ya bude mata ƙofar. Ta shige sannan ya mayar ya rufe, daga bisani shima ya kewaya zuwa nasa ɓangaren ya shiga sannan ya ja motar sukai gaba.

Fara tafiyarsu kaɗan sai Hafsa taga baƙuwar lamba ta kirata, amma bata ɗauka ba, aka sake kira wannan karon kamar ta ɗaga amma bata ɗaga ɗin ba, aka sake wani kiran a karo na uku kuma duk da lambar amma abin da ya faru a karon farko dana biyu bai sauya ba. Tana ta faman nazartar lambar amma ta kasa gano mai lambar, sai kawai tayi tsaki tana shirin saka lambar a black list, sai ga saƙo ya shigo...

Amincin Allah zuwa ga sarauniyar da babu kamarta, madalla da ubangijin daya halicci wannan kyakykyawar halitta...
Junior

Hafsa tayi gajeran murmushi, amma ba tabi kiran ba, tayi saving ɗin lambar a zuciyarta kuma tana tunanin a ina ya samu lambarta...

BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now