3

101 7 2
                                    

Tun bayan dawowar Alhaji Sambo gida Nigeria sai zumuncin su ya sake ƙulluwa da Alhaji Nasir, duk da dai haɗuwar tasu tana wahala kasancewar shi Alhaji Sambo kusan koda yaushe yana cikin manya da ƙusoshin gwabnati a tunaninsa na cewa idan aka saje da su aka shiga jikinsu shi ne za'a iya kawo gyara, saɓanin tunani irin na Alhaji Nasir.

Kawo i wannan lokaci Hafsa da matar Alhaji Sambo Sadiya basu taba takowa sunzo gidan Alhaji Nasir ba, hakan yasa ƴaƴan juna basu san juna ba. Sai dai suna jin sunayensu.

Dalilin da yasa kuwa basu zo ba, ita Sadiya har yanzu bata gama sabawa da zaman kano bane, tun wata fita da sukai washe garin dawowarsu, inda suka kama hanyar zuwa gidan Alhaji Nasir a cikin mota, a hanya sai wani ɗan siyasa yazo wucewa inda take rigimar daba ta ɓalle, akaita zubda jini da kwace wayoyin jama'a. Su kansu banda suna cikin mota kuma Hajiya Sadiyar ta iya motar yadda ya dace da tuni an musu aika-aika...

Lokacin da aka fara sara-sukar, sai yan daba suka tare titin duka, kusan su hamsin, matasa masu ƙananun shekaru, suka rinƙa bin mutane ko ka basu kuɗi ko waya ko kuma su sari mutum, wani zubin su haɗa maka biyu, idan da tsautsayi mai yawa ma sai su haɗa maka uku...

Ganin haka yasa Hajiya Sadiya ta fara yiwa motar gabanta horn tana dakawa na ciki tsawa tana ce masa tunda yana cikin mota me zai hana yabi takan yan dabam kawai, to ashe wayannan yan daba sunji abin da take cewa, ai kuwa sai ji tayi tasssss, an fasa gilashin gaban motar. kafin tayi kyakkyawan yunkuri wani yazo yana ƙoƙarin bude ƙofar motar don ya fincikota daga ciki. Cikin hanzari ta kaɗa kan motar nata gefe da tsananin gudu tayi gefen kwaltar ta tsallake kwata, a wannan lokaci kusan mutum uku sun ɗane motar, ita kuwa saita nufi kududdufin dake gefen hanyar, ta taka birki, motar ta tirje wayanda suka ɗane motar da wannan mai ƙoƙarin buɗe ƙofar dukansu suka faɗa cikin kududdufin, sannan ta murza kan motar da matsanancin gudu ta fito daga gangaren kududdufin ta nufo tudun kwaltar, tana fitowa daga gangaren motar tayi sama, bata dira a ko'ina ba sai a tsakiyar yan daban nan, take suka fara guje guje suna zubar da abin da suka kwata. Ganin haka kuwa sai tayi maza ta juya ta nufi hanyar komawa gida, ita kuwa Hafsa gaba ɗaya tsoro yasa ta ɓuya a karkashin kujera.

Gudu take sosai musamman sabo da ganin wasu matasa a mota biye da ita, suka rinƙa tsere da su, a ƙarshe dai suka zo inda ake bada hannu inda dole su tsaya.

Tsayawarsu keda wuya sai wani matashi ya fito yazo gaban motar yana murmushi yace "Baiwar Allah mace bata taɓa burgeni ba irin yau..., Allah ya ƙara kiyayeki, mun gode don kece kika cecemu, a wajenmu kinfi Obasanjo..."

Hajiya Sadiya tayi dariyar yaƙe tace ta gode.

To tun daga wannan rana basa fita, indai ba fitar data zama dole ba, mafi yawan lokaci na sunfi ganewa suyi aike.


A safiyar wata Alhamis ne, Alhaji Nasir ya kirawo ɗansa yace da shi ya shirya zai aikeshi gidan Alhaji Sambo, saboda zai karɓo wani saƙo. Ansar ya shirya cikin matsakaiciyar shiga farin yadi da farar hula da farin takalmi, sai kuma ɗan littafi daya ɗauka domin ba'a rabashi da littafi. Ansar bai yarda ya ɓata koda minti goma ba a cikin abin hawa ba ba tare daya karanta wani abu ba.

Mahaifinsa ya bashi address da komai da komai na inda zaije, Ansar ya karɓi kudin mota ya kama hanya, cikin ƙasa da minti talatin abin hawa ya ajiyeshi a inda aka turashi. Da zuwansa sai ya nufi gidan, gida mai lamba ta 157.

Ƙatoton gida ne, kuma haɗaɗɗe, domin bama yan ƙasar nan ne suka gina gidan ba, lokacin da ake gina gidan mutane da yawa sun zuba ido suga wanne ɓarawon gwabnatine zai tare. Amma sai sukaga baƙuwar fuska, kuma akace musu daga England ya dawo, a wata majiyar ma ance gwabnatin can itace ta gina masa wannan gida saboda hidimar da yayi mata.

Kusan rabin ginin gilashi ne, yayinda wasu dogayen bishiyu suka ƙara ƙawata ginin. An masa fenti kore ba can ba, sannan yana da sirkin fari da shudi, hakan ya sanya mutane da yawa sukewa gidan wata inkiya wadda wasu suke inkari wato junior jannah, amma dai gidan yafi shuhura da gidan Alhaji Sambo. Gate ɗin gidan kansa abin kallo ne, domin kuwa ba'a saba ganin irinsa ba, domin da na'ura yake amfani.

BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now