7

48 3 0
                                    

A kwana a tashi yau sati guda kenan da ganinta da yaya Ansar amma kusan koda yaushe hoton fuskarsa ne yake kaikawo a cikin zuciyarta, a ɓangare guda kuma tana tuhumar kanta, don me zata so mutumin da shi ga dukkan alamu bai damu da ita ba... Don ita a yanda take ji, idan har yana jin irin abin da take ji a kansa to tabbas zai nemeta, amma haka yazo ya tafi ko lambarta bai karɓa ba. Bama rashin karɓar lambar ne yafi bata haushi ba, har takarda ta rubuta masa mai ɗauke da lambarta a inda ya zauna amma sai bayan tafiyarsa taga wannan takardar a inda ta ajiye ko taɓata bai yi ba...

Tun ba'a gane cewar tana cikin wani hali ba, har aka fara fuskanta...

Wata ranar laraba tana zaune a lambun gidansu tana karanta wani littafi 'How Europe underdeveloped Africa' sai kawai taji anyi gyaran murya, juyawar da zatayi sai kawai ta saki littafin sabo da tsananin mamaki fuskarta ta faɗaɗa da murmushi... "Sannu da zuwa..." ta furta lokacin da take fuskantar abin da ta gani.
Sai ji tayi an kamata an jijjigata, "Waike yaushe za ki nutsu ne?"
Muryar mamanta taji tana daka mata tsawa cikin fada.

Sai a lokacin ta ankara ashe ba Ansar ne ya taho inda take ba, ashe mamanta ce.

"Ina sane fa, dama so nake inji me zaki ce..."
Hafsa ta faɗa tana murmushin yaƙe. Yayin da take ƙoƙarin fito da wayarta daga aljihun jeans din da take sanye da shi.

Mamanta ta ɗanyi jim kaɗan sannan tayi murmushi kawai ta cewa Hafsa, "Okay, Kije ku gaisa da Ansar, yana ɗaki yazo suyi magana akan karatunku... But please ko za'a kiraki a tambayeki akan ina kike so kuyi karatun kice a gidan nan. 'cause naji shi Ansar yana dagewa sai dai kije gidansu, kuma kinga keba wadda zan tsaya bawa labari bace..."

"Never mind mom."
Hafsa ta faɗa, daga bisani ta miƙe bayan ɗaukar littafin ta da yake ƙasa da tayi, ta gyara gashin kanta ta mayar da shi baya, sannan ta cire gilashin da yake a fuskarta. Ta ɗanyi murmushi ba tare da tace komai ba ta juya ta nufaci harabar gidan... Tabi wasu matattakala wayanda basu gaza guda huɗu wayanda zasu fitar da ita daga garden ɗin, za kuma su sadata da cikin gidansu...

Hafsa bata tsaya ko ina ba sai a ɗakin baƙi, inda ta iske Ansar a zaune a ƙasa, yayin da mahaifinta yake kan kujera yana ɗan duba jarida...

"Dad, I told you, these magazines are available online in softcopy..."
"Tun yaushe nace kizo ina kiranki?" Alhaji sambo ya tambayeta yana mai juyar da maganar da ta shigo da ita zuwa wata maganar dabam...

"Sorry Dad" ta faɗa tana wani murmushi wanda yasa Ansar da yake gefe yaji zuciyarsa ta buga da ƙarfi kamar ta fito ta risina gaban Hafsa...

"Yaya Ansar" Hafsa ta faɗa tana mai murmushi.

Shiru Ansar yayi kamar bai ji ba, ta kumayi masa a karo na biyu, amma sai yayi kamar bai jiba.

Idon Hafsa ya ciko da kwalla, domin idan akwai abin da tafi tsana a rayuwarta to shine wulaƙanci...

Mahaifinta yayi mata inkiya ta zauna, shi kansa alamun rashin jin daɗin haka ya bayyana a fuskarsa.

"Gata nan, kai yayanta ne, kuma ɗan'uwanta sannan malami... Bayan karatu na makaranta, inaso ka ɗora da koya mata ilmin addini..." Alhaji Sambo ya faɗa.

"Nasan aminina, mahaifinka, ya sanar da kai cewa ina so ku shiga makarantar share fagen shiga jami'a don yin karatun shekara guda wato IJMB anan College of Art and Science dake kano, mun yanke wannan shawarar ne saboda ganin yanda ilmin secondary ya taɓarɓare ta yanda ba'a iya koyawa ɗalibai abin da ya dace a koyar dasu..."

"But Dad I..." Hafsa ta katse shi tana yatsine fuska cikin alamun shagwaɓa da nuna rashin yarda.

"I know," Mahaifinta ya katseta da sauti mai ɗan ƙarfi, sannan yaci gaba da cewa "Karatunki a waje ki kai, don haka directly idan kika shiga jami'a yau may end up seeing everything upside down... But atleast idan kikaje Cas kano zaki zama familiar da karatun Nigeria... and please dont interrupt again, mun riga mun yanke shawarar komai..." Alhaji sambo ya muskuta ya zira hannunsa a cikin aljihun farar yar sharar da take jikinsa ya fiddo da wasu scratch cards guda biyu yana murmushi sannan ya miƙawa Ansar duka guda biyun yana mai cewa "Ɗaya na ka, ɗaya na ta, sai ku cike yanzu, a wannan laptop ɗin taka." Ya faɗa lokacin da yake miƙo masa wata laptop da alama sabuwa ce.

Ansar yasa hannu bibbiyu ya karɓa yana godiya, juyawar da zai yi sai yaga Babu Hafsa a bayansa. Ansar ya shiga tunanin ina ta tafi.

"Me kake nema?" Yaji muryar Hafsan ta tambayeshi.
"Laa ashe kina nan, ai nazata kin fita". Ansar ya furta yana murmushi.
"Kai da wa?" Alhaji Sambo ya tambayi Ansar. "Naga kai kaɗai kana cewa "ka zaci ta fita ne..."
Ansar ya saki baki yana mamaki ya kuma kasa bada amsa...

Sallamar Hafsa ita ta katse shi daga tunanin da yake. Ya kasa amsawa sabo da kada yaje ko yanzun ma maganar gizo take masa...

"Laptop ɗita zata fi yi mana daɗi, tunda kaga ita komai a saiti yake, kai kuwa kaga yanzu sai anyita ƙoƙarin saita abubuwa, shiyasa ma naje na ɗauko tawa, sai muyi registration ɗin idan mun gama kai kuma idan kaje gida saika saita takan..." Hafsa data zauna kusa da shi ta faɗi hakan. A dai dai lokacin kuma mahaifinta ya tashi ya fice daga ɗakin.

Ansar yaji me tace amma sai ya kasa cewa komai, asali ma dai tsoro yake ji kada yaje ko ba ita bace kawai dai muryar ce tayi masa gizo.

Hafsa ta fusata mutuƙa ganin yanda yake shareta kamar bai san da mutum kusa da shi ba, sai kawai tayi wani motsi ta koma gabansa tana fukantarsa, ta sanya hannu ta ɗan daki kafadarsa. Firgigit ya dawo hayyacinsa.

Ta kalleshi tana mai zaro ido tace "Na tsani wulaƙanci, kuma ina so ka sani ustazanci dabam wulaƙanci dabam, tun ɗazu ina maka magana but it seems like i am talking to stone ko kallo ban isheka ba."

"Sorry" Ansar ya faɗa yana murmushi.
"Sorry?" Ta tambaya tana yatsine fuska.
"Okay, sorry for saying sorry" Ansar ya faɗa yana mai kallon gefe.
"Please stop, i hate this word..." Ta faɗa cikin wata ƙaramar tsawa.
"Okay na daina faɗa. Ban san ba kya so ba... I am very sorry."

Hafsa tai ƙwafa kawai ta bude laptop ɗinta ta fusge scratch cards ɗin daga hannunsa.

Ta fara sanya adireshin shafin makarantar don fara rijistar... Ansar dake zaune yana satar kallonta idan yaga alamar zata kallo shi sai yayi maza ya kauda fuskarsa. Ita kuwa tuni ta ankara da shi.

"Shigowata ta farko na kira sunanka, me yasa baka amsa ba?"
Hafsa ta katse shirun daya wanzu tsakaninsu.

"Bakiyi sallama ba, kuma hadisi ya tabbata cewa wanda ya fara da magana kafin sallama to kada ku kula shi, wani hadisin kuma cewa akai wanda ya fara da tambaya kafin sallama to kada ku amsa masa..."

"Ka kyauta, amma da ni ce kai tunda nasan wanda yayi hakan ya sha'afa ne ko kuma bai san ma hadisin ba, da gyara masa zanyi, ba wai in ɗauki hukunci ba."

"Naji wannan!" Ansar ya faɗa dai dai lokacin da suka haɗa ido da ita dukkaninsu sukai murmushi.

Kowannensu ji yayi kamar ya gayawa ɗan'uwansa irin yadda yake ji a zuciyarsa, amma kamar haɗin baki duk sai tsagin daya ke bada shawarar yin shiru yayi rinjaye a zuciyarsu.

"Kin san kuwa makarantar nan da zamu je tana da mutuƙar wahala" Ansar ya faɗa lokacin da yake wasa da yatsunsa akan sabuwar laptop ɗin da aka bashi.

"Tab, but dama indai karatu ne dole da wahala, you have to try your best..." Hafsa ta faɗa lokacin da take miƙo masa, katinsa.

"Baki san ta bane, Irin karatun nan da ake cewa the hard way the only way fa nake nufi"

"At the end of the day irin wannan karatun turns zero to hero." Hafsa ta faɗa.

Tana mai rufe laptop ɗinta tare da inkiya da hanneyenta guda biyu cewa ta gama.

Ansar ya jinjina mata.

Ƙarar da suka ji ta alamar faɗuwar wani abu mai nauyi da kuma salatin Alhajin Sambo da suka ji shi ne ya sanyasu suka miƙe zumbur suka nufi harabar gidan inda suka jiyo wannan ƙarar da matsanancin gudu.

Zamu dakata anan.

Sai kuma a rubutu na gaba idan Allah ya yarda.

Naseeb Auwal

Naseeb Auwal

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now