14

33 4 3
                                    

Kamar kullum yau ma tare suka tafi makarantar tare da yaya Ansar, sai dai kuma ba kamar kullum ba domin babu wanda ya cewa wani uffan.

Bayan sun sauka daga motar ne driver ya juya ya tafi ya barsu a tsaye a harabar makaranta. Suka kalli juna kowannensu yayi murmushi sannan kamar kowanne yana son yin magana amma sai suka ɗagawa juna hannu alamun sai an jima.

Kowanne ya kama hanyar tafiyar da zata sadar da shi zuwa ga inda zasuyi nasu darasin.

Kasancewar yanayi ne na damina don haka zaka iske cewa garin ya ɗanyi duhu kaɗan duk da cewa safiya ce, hakan yana da nasaba da gagarumin hadarin dake sararin samaniya.

Bayan Ansar ya shiga aji ne sai maryam take masa inkiyar cewa yazo kusa da ita ya zauna ta ajiye masa guri a mazaunan farko.

Babu musu ya amsa kiranta, ya zauna kusa da ita, ta ɗauko wata chocolate ta miƙa masa tana murmushi tace "Wannan wata ce tace a baka."
"Wacece haka."
"Bana son faɗar sunanta."
"To nuna min ita."
"So kake in mutu? Ai ganinta yana nufin mutuwa ta."
"Hmm, idan kin gaji kya gaya min." Ansar ya faɗa lokacin da yake ajiye chocolate din a gefe tare da bude littafinsa don ganin inda suka tsaya a wannan darasi da za ai musu yanzu.

"Zuciyata ce, kaga kuwa idan nace zan tsaga ƙirjina in nuna maka ita ai mutuwa zanyi." Maryam ta faɗa tana murmushi. Shi kuwa Ansar sai yayi kamar bai ji ta ba.

Ya ci gaba da karanta abin da ke gaban sa.

Suna tsaka da wannan yanayi sai malami ya shigo don haka duk sai hankalinsu ya koma gare shi. Bayan gama darasin ne fa sai kawai wasu matasa suka shigo kamar dama jira suke malamin ya fita.

Basu wuce ko ina ba sai inda Ansar yake zaune, cikin su babu wanda Ansar ya sani. Amma sai duka ɗaya bayan ɗaya suka miƙa masa hannu, shi kuwa ya caccafke da su.

Wani daga cikinsu ya miƙawa Maryam hannu amma sai kawai ta kauda kai tace bata gaisawa da maza. Matashin ya kalleta yayi murmushin mugunta kawai.

"Sunana Junior," matashin ya faɗa yana kallon Ansar ta cikin baƙin gilashin da ya mamaye yanki mai yawa na fuskarsa. "Ina so in yanka maka kashedi, daga yau kada ka ƙara shiga harkar gimbiyata..."
"Kin sanshi ne?" Ansar ya juya yana mai kallon Maryam cike da mamaki.
"Yau na fara ganinsa." Ta bada amsa tana mai keɓe baki.
"Bata sanka ba ta yaya ta zama gimbiyarka?" Ansar ya tambayi matashin yana murmushin ƙarfin hali.
"Wannan nake nufi." Matashin ya faɗa lokacin da yake nunawa Ansar Hafsa a cikin wayarsa sanye da wasu ƙananun kaya kalar blue masu kama jiki ta dasa wani baƙin glass a fuskarta.

Wani bugu zuciyar Ansar tayi, yayi zumbur ya miƙe yana kallon cikin ƙwayar idon junior, tunani kala-kala ya rinƙa zarya a cikin ƙwaƙwalwarsa yaji wani abu ya turnuke masa zuciyar sa.

"Na dai gaya maka, babu kai babu ita idan ba haka ba..." Saurayin yana magana wani tutturna daga yan rakiyar tasa ya toshe masa baki yace "kada ka gaya masa yanzu, indai yana son yaga me zamuyi kawai ya ci gaba da kulata."

Ansar ya bude baki zai yi magana amma sai Maryam tayi masa inkiya yayi shiru tace da shi "Idan karnuka sukai haushi kaima kayi haushi mutane zasu yi tunanin kaima kare ne..."
"Ba zaki tabbayar da cewa mu karnukan bane har sai wannan koɗaɗɗen ya sake shiga gonar mu." Wani dabam ya bada amsa.

Suka juya suka fice Ansar ya bi su da kallo, bayan sun fice sai kawai yayi ajiyar zuciya ya kifa kansa akan bencin da suke zaune. Maryam ta nuna masa kada ya wani damu barazana ce kawai irinta ɗalibai.

Ko kaɗan Ansar bai taɓa gayawa Hafsa abin da ya faru tsakaninsa da wayannan matasa ba, sai dai wasu lokutan idan suna hira tana yawan gaya masa junior yayi kaza da kaza. Shi kuma sai ya nuna mata bai ma san wanene Junior ɗin ba.

Haka suka ci gaba da rayuwa koda yaushe yana ƙoƙarin ya nuna mata cewa Junior da wannan gayyar tasa ba ababen yarda ba ne kuma zasu iya ruguza tarbiyyar ta, ita kuwa ko yaushe tana nuna masa cewa ita tana da wayewar da babu wanda ya isa ya canja mata tunani, sannan kuma tana nuna masa cewa wannan itace ƙuruciyarta don haka tana buƙatar tayi rayuwa ta jin daɗi da morewa.

"Tunda ki kaga musulunci ya buƙaci mace ta zama cikin kulawar namiji a kowane lokaci to ya kamata ki fahimci cewa lallai rashin wanda zai bata kulawar babbar matsala ce."
"Ni kaga ka ƙyaleni don Allah, na gaya maka ina da ilmin da mutum bai isa yayi wasa da tunani na ba, wai me yasa baka yarda da ni bane. Ka min maganar mutanen nan yafi sau miliyan kuma na baka tabbacin cewa zan kular maka da kaina to don me ba zaka yarda da ni ba?"
"Kin kasa fahimtar abin da nake son ki gane Hafsa, shi mutumin banza koda yaushe bama sai iyakar ke mace ba, hatta namiji ana so yayi nesa da mutunen banza, kin karanta Akhdari wanda iyayenmu suke kira ahalariy a ciki mallam me yake cewa? Cewa yayi bai halatta a gareshi (baligi) ba, yayi abota da fasiƙi ko zama tare da shi ba tare da wata lalura ba."
"To kuma anan kaga ai akwai lalurar ko? Tunda rayuwar makaranta ce ta haɗa mu. Ko kuwa za kace rayuwar makaranta ba lalura ba ce?"
"Tana zama lalura a zamanku a aji guda, ko maganar ku a whatsapp groups na aji, amma magana privately ko kuma keɓantacciyar mu'amala tsakaninki da su wannan ba lalura bace."
"Kaga kawai ni ka barni inyi abin da naga dama, tutiyarka ɗaya kace kai ne zaka aure ni, kuma hakan ma sai idan nice naga dama, idan na so sai ince ba na sonka, sai me? Kuma ina son ka sani everything man can do woman can do better..."
"Woman can do better?" Ansar ya tambaya yana yatsine fuska game da mamakin yanda take ɗaga mai murya. "Ba fa ina miki maganar haihuwa da zubda jini ba ne, ina miki maganar rayuwa ne gaba ɗaya."

Maganar ta yiwa Hafsa ciwo ta ɗaga hannunta kawai ta nuna shi kamar tana son faɗar wata magana amma sai kawai fushi ya hana ta. Kawai ta gƴaɗa kai.

Ansar ya ci gaba da cewa "Kuma ba zan bari ki bar hanyar da addini ya shimfiɗa miki ba, dole zan ci-gaba da nuna miki hanyar gaskiya koda kuwa hakan zai zama sanadin rabuwar mu ko mafi muni..."

Wannan tana ɗaya daga cikin tattaunawa da sukai da Hafsa, amma duk da haka alaƙarta da su bata sauya ba.

Hakan yasa Ansar ya shirya cewa lallai babu abin da yafi kamata da shi face ya dakatar da su. Tunda yayi iyakar ƙoƙarin ganar da ita amma son rayuwar turawa da kuma wayewa sun rufe mata ido.

A nata ɓangaren kuwa Hafsa, tana ganin kamar Ansar ya ɗauki addini da zafi ne, inba haka ba ita bata ga wani abin haramci da take aikatawa tare da su Junior ba, ko kuwa a wajen Ansar zama ayi hira ma yana cikin haramci?

Tabbas ta san cewa su Junior suna abubuwan da basu dace ba, amma tunda ta yarda da kanta tasan cewa babu wanda zai iya chanja mata tunani a cikin su. Domin itama tana ganin yanda wasu matan da basu kaita kyau, ilmi ko sanin rayuwa ba yadda suke fanɗarewa.

Abin da yasa kuma take tafiya tare da su shi ne, hakan yana bata nishaɗi kuma yana dawo mata da wasu kwanakin da tayi a ƙasar waje. Don haka idan tana tare da su sai taji tamkar tana can inda aka binne mahaifar ta wato ƙasar England.

Alaƙarta da su kuwa tana ta ƙara nisa, har ya zamana tayi joining sports din bangaren basket ball, sannan ta shiga wani club na koyon rawa duk ba tare da sanin gidan su ko Ansar ba. Kuma wannan duk sun nuna mata cewa a matsayinta na me yaƙi don ƙwatowa mata haƙƙinsu dole sai ana ganinta a irin wayannan gurare...

Bayan sun shiga level 200 sai alaƙarta da su ta ƙara yawaita ya zamana matan cikinsu ma sukan je gidansu, hakanan a ranakun da ba na makaranta ba sukan haɗa tarurruka don tattaunawa akan ƙwatowa mata haƙƙinsu. Da kuma ƙoƙarin daidaita tsakanin mata da maza a dukkanin wani abu da jami'ar zata aiwatar. Suna samun ƙwarin gwiwa musamman ganin yanda ƙungiyoyi daga ƙasashen ƙetare suke basu goyon baya.

Zamu dan huta a nan. Sai kuma a rubutu na gaba.
Mai karatu, shin kana bayan Ansar ko kana bayan Hafsa?

Mai karatu, shin kana bayan Ansar ko kana bayan Hafsa?

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
BAHAGUWAR SOYAYYAWhere stories live. Discover now