Gyara zama tayi cike da kulawa tace kwantar da hankalin ka Yaya, zata canja ne nan bada dadewa ba. Idan ka lura lokacin daka dawo kasar nan baki dayan hankalin yar' uwata na kanka, dalilin canja wanta kuma sbd makaranta ne, inaso kayi mata uzuri sbd inada tabbaci akan yar' uwata zataci gabada baka kulawa fiye da wancan lokacin.

Murmushin jin dadi yayi kafin yace ina alfahari da samunki a matsayin kawata, na gode da shawararki kuma bazan taba mantawa dake ba har karshen rayuwata.

Murmushin itama tayi kafin sukaci gaba da firansu mai dadi sai daria suke.


%%%%%%%

Kai tsaye daki Umma ta nufa ta zauna bisa gado zuciyarta na mata kuna, jinjina lamarin Majeed da Mee'ad takeyi a zuciyarta" a fili take cewa dole na dauki mummunan mataki akan tarayyan wadan nan yara domin kuwa 'a yanzu bana bukatar kusanci tsakaninsu, hmm nasan yanda zan bullowa lamarin. girgiza kai tayi daga bisani ta dauki wayarta ta fara dialling wata number, ko number wa zata kira oho.

" Karfe 5 Amal suka tashi a school bata wani tsaya jiran Majeed ba tayi tafiyarta gida.

A matukar gajiye ta dawo gida, dakinta ta nufa kai tsaye, wanka kawai tayi, sannan ta nufi bedroom din Umma.

Zaune ta sameta bisa gado hannunta rike da waya. zama tayi a gefe kafin tace Umma barka da yammaci, kiyi hakuri yanzu na dawo.

Murmushin karfin hali Umma tayi kafin tace Amal kinsan dalilin daya sanya na kiraki ? girgiza kai Amal tayi kafin tace a'ah! gyara zama Umma ta karayi kafin tace dama inaso nasan gaskiya 'akan alakar waccar yarinyar Mee'ad da Majeed ne.

Murmushi Amal tayi kafin tace haba Umma wannan ne dalilin da yasa kika kirani tin ina school ? to ki kwantar da hankalin ki domin kuma babu komai tsakanin Bloody ta da Yaya Majeed, hasalima Yayan dani yake soyayya.

Dogon ajiyar zuciya Umma taja kafin tace Alhamdulillahi! dama 'abinda nake sonji kenan. Domin Abbanki ya shaida mini zai hadaki aure da Majeed din nan bada dadewa ba.

Tsalle Amal tayi kafin tace da gaske za'a hadani aure da kyakkyawan miji kamar Yaya ? Allah na gode maka! Umma kema kinsan ina matukar son auren kyakkyawan miji ko ? pls Umma ki mara min baya na cika burina na auren Yaya Majeed.

Murmushin jin dadi Umma tayi kafin tace kwantar da hankalin ki d'iyata insha Allahu zanyi dukkan kokarina wajen ganin kin auri Majeed, domin Majeed kyakkyawane kuma babban attajiri sbd jiya Daddy shi yake shaidama Alhaji ya dora Majeed din akan dukkan kasuwancin sa, bayan haka kuma ya gina masa katafaren asibiti a garinsu in takaita miki bayani ma da zarar an sanya ranar aurenku nan da sati 2 Majeed din zai koma gaban iyayensa domin karasa shirye ~ shiryen auren.

Wow Umma da gaske kike koda wasa ? gaskiya idan da gaske kike naji dadin wannan maganar sosai.

Shafa kan y'ar tata tayi kafin tace insha Allahu nayi miki alkawarin dukkan abinda kikeso zan baki, idan kuma banada shi zanyi iya bakin kokarina domin naga na mallaka miki abun koma minene.

Naji dadin jin haka daga gareki Umma. amma kinsan mi yake damuna kuwa ? a'ah Umma tace Amal tace Umma Allah banijin dadin abinda kk yima Mommy a y'an kwanakin nan.

Had'e rai Umma tayi kafin tace kinga banison shishshigi kuma bazan taba daina 'abinda kikaga na farayi mata ba, sbd a wannan lokacin babu wacce na tsana idan Fateema ba, domin ta 'batamin rai kuma ta nuna mini ban isa da ita ba, domin ta biyema Hajiya Hindu sun hada baki sun dauki twins sun fitar dasu kasar waje karatu don son zuciya, sbd wancan lokacin naso a barki kije kiyi karatu acan amma suka hana suka yimin bakin ciki akanki ke d'aya tilo da Allah ya 'azurtani dake.

Kiyi hakuri Umma. Banga wani abun aibu a hanaki kaini outside nayi karatu ba, amma ina kara baki hakuri dai sbd komai ya wuce a yanzu. Kuma gaskiya baniso kina shawara da Aunty safiyya sbd bata baki shawara mai kyau kwata ~ kwata.

Umma ta ce ke banison tsageranci tashi ki fice min daga gani kina jinako ?

Ba musu Amal ta nufi kofar fita sbd ganin ran Umma ya 'baci sosai.

Kai tsaye dakinta ta nufa, bayan taci abinci ta kira Amrah ta shaida mata yadda sukayi da Umma, jimm Amrah tayi kafin tace na tayaki murna sosai, tnx Amal tace tana murmushi.

Dogon numfashi Amrah taja kafin tace Kawata kinsan mi nake tinani ? a'ah Amal tace! gyara zama Amrah tayi cike da salon kissa da munafurci tace kawata da cewa kikayi baki yarda 'a sanya ranar auren nan kusa ba, sbd kar a sanya ranar auren kuma kiyi sabon guy. idan baki manta ba duk cikin mu kece ta musamman din da kk yin sabbin guys akan time. kuma za'a iya sanya miki rana da Majeed daga baya ki hadu da gayen daya fishi komai ma.

Shiru Amal tayi zuciyarta cike da sake ~ sake tace karki damu kawata zanyi tinani akan shawararki sbd nasan bazaki bani shawara mara kyau ba.

Murmushin mugunta Amrah tayi kafin tace ina jiran jin shawarar da kika yanke. bye sai na jiki, katse wayar tayi ba tare da sunyi sallama ba.

Ajiye wayar tayi zuciyarta cike da farin ciki take cewa insha Allahu bazan taba barin wannan auren ya kasance ba, sbd bazan jure ganin tarayya tsakanin Majeed da Amal ba. Allah ka kawo mini karamar hanyar da zan ruguza wannan auren.


Mai karatu biyoni kasha lbr 💯

Pls vote, comments and share Fisabilillah 🙏🙏🙏🙏🙏.

MEE'ADWhere stories live. Discover now