A bangaren Amal ma abin haka yake zaune take bisa kujerar dake dakinta sai murmushi take tana fadin wai Yaya Majeed zai dawo ? Wani irin girma da kyau ya kara dai ? Ta dan kishingida kafin tace wai Majeed ya zama handsome guy! Huhhm za musha yawo dashi na rika nunashi ma kawayena sbd mijine na nuna ma sa'a duk dama ba soyayya muke ba zan fara koyar dashi yadda ake soyayya musamman soyayyata, ta kara gyara zama kafin tace saina sace zuciyarka lokaci daya MAJEED!.

" Yau wata 1 kenan gidansu Majeed sunata shirye2 dawowarsa cikin masu Shirin harda Amrah wacce yawancin lokuta tana gidansu Amal, abin yanata bama Amal mamaki sbd da can Amrah bata zuwa gidansu haka kawai sai da dalili Amma yanzu an wayi gari kusan kullum sai tazo ta6 🤔 akwai kura faah.

Ranar wata laraba Amal ce zaune a falo yayinda Mee'ad ke kicin tana taya Inna aiki, sallamar Amrah Amal ta jiyo tin daga bakin falo tashi tsaye tayi fiskarta dauke da murmushi tana fadin yar halak! Yanzu nake tinanin ki  a raina, murmushi Amrah tayi kafin tace shegiyar kawa! Yau faah ba zama nazo yiba yau nazo ki rakani shopping ne,"

"Ta kalleta fuskarta dauke da mamaki kafin tace me zakije ki sayo ? Amrah tace wannan ba damuwarki bane" tare mukazo da wani guy zai kaimu unguwar, Amal tadan zaro ido kafin tace kikace da guy dinki zamu tafi ? Amrah tace kwaraima kuwa, Amal cewa tayi rufamin asiri kada kijamin bacin rai a wajen Daddy kinsan Abba bayina yaje wajen mutuminki Majeed ranar Sunday zasu dawo tare,"

Amrah tace I know oo u forgot ne ? Jijiga kai Amal tayi kafin tace kinga bari na sami Umma 'a sama na tambayeta idan ta barni muje idan Kuma ta hana kya tafi ke kadai", tana gama fadin haka ta haura sama, tabar Amrah na jiranta.


***** Kinata ina kawata sa'adatu bappa itas inata zare ido ban ganki ba ko lpy ? 🤔🙄😜.



\\\\\\\\\\\\\\\"""" Rana bata karya wai inji bahaushe wayewar garin yau yayi dai2 da ranar lahadi wato ranar da Yaya Majeed zai juyo zuwa kasata, kasarka, kasarki, kasarku, kasarmu baki daya wato gida Nigeria,"

( Allah ka daukaka kasata Nigeria ka kuma bamu kara mana zaman lfy, kwanciyar hankali harma da tsaro, Allah ka jibanci dukkan nin al'amurammu baki daya 🤲🤲 Ameen. )

" Tin bayan sallah asuba da suka tashi ba Wanda ya kara rintsawa tsakanin su, ba'abinda suke sai gyare2 gida da kuma uwa uba murnar dawowan Majeed din baki daya gidan yadau gyara sai kamshi soye2 kawai kakeji malam,"

"Ni kuma 'a matsayina na bakuwa tsaye nake hannuna rike da littafi da biro ba abinda hancina ke jiyowa sai kamshi, cike da gulma na debi yan kafafuna na leka kitchen ina mai hadiyar miyau 😜 lekawan da zanyi idona yaci karo da kula cike makil da soyayyun dakwalen kaji na lashe busassun lebbana 😋  kafin na kara saka kai, ji nayi ance ke mi kikazoyi nan wajen dallah fita kibama mutane waje, domin kuwa ba'a gayyace kiba ba musu na debi takalmana na juya da dan guntun kunyata 😅😅😅🤪.

" Karfe hudu dai2 yayima mutanen gidan a airport kowa sai dokin ganin Majeed din yake a ciki hadda Amal da Amrah, yayinda ita kuma uwar gayyar ke zaune a gida wai a cewarta wai bata shirya ba,"

Karfe hudu da rabi dai2 jirgin su Majeed ya sauka 'a 'airport, bayan wadansu yan mintoci da saukan jirgin , fasinja suka fara sauka a hankali bayan bude wani kofa mai kama da windo a jikin jirgin 🙄.

" Abbane ya fara saukowa kafin Majeed dake sanye cikin wasu fararen boyel masu tsadar gaske kansa sanye yake da hula fara dinkin borno, yayi kyau sosai kamar wani sabon ango, tafiya yakeyi a nitse har yakaiga sauka bisa kan jirgin,"

Yana saukowa Daddy ya tareshi yana mai cewa My son ur welcome! Murmushi yayi kafin yace tnx u Dad 😊 kama hannunsa Daddy yayi ya nufi wajen su Umma kuma wajenda sukai parking motocinsu, da murmushi Abba ya biyosu a baya.

" Kai tsaye gurin da su Umma ke tsaye ya nufa da Majeed, yayinda shi Kuma idonunsa ke leke2 kozai hango Gimbiyar tasa duk dama sanin yarinta yayi mata.

Majeed yana kan leke2 idanunsa sukakai kallonsu ga yan mata 2 dake tsaye bisa gefen Umma, sunyi kyau sosai dan kuma kowacce su ta kure wanka, Amal dake tsaye a gefen daman Ummanta sanye take cikin shiga ta alfarma wata bakar doguwar Abaya ta saka yayinda tayi rolling gyale sky blue takalmin dake sanye a kafarta kalan mayafin ta ba 'abinda fuskarta keyi sai walwali, yayinda ita kuma Amrah ke sanye da riga da siket na atamfa sun kama jikinta kadan Amma itama tayi kyau sosai,"

Binsu da kallo kawai Majeed keyi har suka karasa kusa da Umma yadan risina yace Umma barka da wannan lokacin Umma ta amsa Masa fuska cike da farin ciki, Amrah ta jaa hanun Amal tana fadin zomu tsaya ta baya can, suka nufi bayan moto suka tsaya,"

" Yayinda shi kuma Majeed baki dayan hankalinsa ya tafi zuwa garesu domin kuwa yana gama gaisawa da Umma ya rufa musu baya, murmushi ne dauke a fiskarsa yayinda zuciyarsa ke bugawa da sauri2 sbd babu abinda take muradin gani a dai2 wannan lokacin sai abar kaunar tasa............





Mai karatu biyoni kasha lbr 💯







Pls vote, comments and share Fisabilillah 🙏🙏🙏🙏🙏.

MEE'ADWhere stories live. Discover now