TKK 019

145 30 6
                                        

Assalamu Alaikum beautiful people...
I think I'll be updating once or twice a week In Shaa Allah.

The votes and comments are getting fewer why na? 💔😭😭
I'm  just heartbroken 😂.

Dan Allah kuyi voting da comment ko na samu kwarin gwuiwa.

Jazakumullahu khair ❤️


"Mai wayar nake nema, ya na ina?".
Ta fada cikin karfin hali, tana ambaton Allah a cikin ranta. Don ba irin tunanin da bai fado ma ta ba a cikin yan dakiku.

"Amaryarmu, ayi hakuri mun rike ma ki ango amma gashi nan zuwa wani aiki ne ya tsaida shi".

Ta sauke ajiyar zuciya, duk da yamutsewar da ta ji zuciyar ta yi sakamakon jin muryar mace da tayi.

"Okay, thanks".
Ta fada ranta a dugule, tana cika tana batsewa ta zauna kan sofa.

Ganin har karfe tara ta gota, ta tashi ta nufi daki, ta cire kayan jikinta ta saka pajamas dinta masu zanen Mickey Mouse a jiki.
Ta ja bargo ta shige ciki tare da yin addu'ar bacci, zuciyarta na suya haka bacci ya dauke ta.

Tunda ya kwankwasa kofar falon ya ji shiru yasan ba ta falon, yasa mukullinshi ya bude tare da kunna wuta. Sassanyan kamshi ya bugi hancinsa. Ya hau wurga idanunshi ko zai ganta bai ga ko burbushinta ba. Sai candles da ke kunne saman teburin cin abinci, suna ta bada haske.

Ya bude warmer ya debi abincinsa ya zauna ya ci ya yi kat! Sannan ya kwashe komi ya kai kicin, ya zuba sauran a freezer.

Dakinshi ya shiga ya tarar da ba ta nan, wanka yayi sannan ya wuce dakinta, baccinta take hankali kwance, numfashinta na sauka a hankali.

Murmushi yayi tare da gyara ma ta bargonta, ya kwanta tare da jawo ta jikinshi.

Ya furta "Goodnight Precious" a hankali.

***
Ba ta farka ba sai asuba saboda gajiyar da ta yi, ta ji ta kankame a jikin mutum, ta ware idanunta tsab a kanshi, a hankali abinda ya faru jiya ya fara dawo ma ta.

Fuu ta dire daga gadon ta fada bandaki ta yi alwala. Ba ta ko tada shi ba, ta zauna tana karatun Al-Qur'ani har aka kira sallah ta gabatar da raka'atanil fajr.

Sai da ta ji an fara tada sallah ta ja yatsun kafarshi, sannan ta tada ta ta sallar.
Ya yi saurin tashi ya nufi dakinshi, saboda makarar da yayi.

Bacci ta koma ta saita alarm dinta karfe bakwai.

Tana kicin tana hada karin safe ya shigo sai baza kamshi yake, ya yi masifar kyau cikin bakin wandon chinos da farar shirt mai ratsin bakin zane a jikinta ta Armani.
Kan nan sai kyalli yake yasha gyara, ta kalle shi tare da hidiye wani yawu makwat!

Ta yi saurin kauda kai, ta juye ma shi coffee a kofi ta ajiye saman island na kicin.

Sam abincin ma ba ta da appetite , coffee kawai ta kurba ta zuke sannan ta dauraye kofin ba ta ko kalli she ba, amma jikinta ya ba ta kallonta yake yi.

Ta duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta ta ga har tara saura, ta yi saurin gyara dankwalin abayarta ta sa pin, tare da daukar jakar kwamfutarta da makullin motarta.
Da kyar ta iya furta "Sai na dawo". Shi ma ciki-ciki ba don ya kasance cikin masu kyakkyawan ji ba ba zai gane abinda tace ba.

Murmushi ya yi tare da girgiza kai, ya bi bayanta. Za ta shiga mota kenan ya shammace ta, sai ji tayi an rungumo ta ta baya.

Sam cold treatment da take ba shi bai ma shi ba, ya gwammace ko ihu za ta yi ta yi, idan cizo da yakushi ne duk tayi, amma ba zai iya jure rashin jin muryarta ba da iskar kare da take yi da shi.

TA WA KADDARAR KENAN! Onde histórias criam vida. Descubra agora