Arba'in Da Shida

Depuis le début
                                    

Wanka ta shiga tayi, riga da skirt ta samu wanda suka hau jikinta sosai, har dan jambaki ta saka saboda dukdan ta nuna mashi ita babu abunda yake damunta duniya. Gyale ta saka ta fita bayan ta dauki jakarta, a ranta tana ayyanawa dukma yanda za'ayi sai ta tafi gida ta gaji bazata iya ba. Falo ta iske shi ya daura daya kan daya yana kallo alamar shi hankalishi ma kwance kamar bashi bane jiya ya marairaice ya zama abun tausayi. Wato Allah ya biya mashi bukatunshi yanzu sai wulakanci ko?

Tsaye ta mashi a kai tana gyalen jikinta, "Na shirya, ka tashi mu tafi."

Dagowa yayi a hankali yana kallonta, kasa magana yayi kawai yana tsaye yana kallonta kamar kar ta motsa. Wayarshi ya dauko a hankali ya daga ya mata hoto. "Masha Allah, kinyi kyau sosai Ramlah. Allah ya miki albarka." Dukda yanda take jin yan rashin kunyarta saida kalamanshi suka mata dadi cikin rai amma ta maze kamar ma bataji me yace ba. Neman hanyar fita take yayi hanzarin kamo hannunta batayi aune ba ta fado saman jikinshi. Neman kwacewa takeyi ya riketa a hankali yana saita mata zamanta saman cinyarshi.

Dagowa tayi taga yana kallonta hankalinshi kwance, "Ka sakeni, na fada maka gida zanje."

Dan guntun murmushi ya saki, "Wane sakin kike nufi? In sakeki na auren gaba daya ko yanzu in kyaleki? Kuma nace ai bazakije gida ba Ramlah. Yan biki ko gama tafiya basuyi ba kawai sai a ganki kice kinje me to?"

"Rayyan ka bar ganin ina maka sanyi sanyi. Ka kyaleni, sakin ma daga baya ai zakayi. Gida zan tafi dan nidai bazan iya zama dakai ba. Zance masu ban sanka a raba auren, shikenan." Har yanzu saman cinyarshi take, ji take kamar kasa ta tsage ta shiga. So take ma ta mashi masifar amma batasan me zatace mashi ba.

"To aini inasan matata, kuma ko duniya zata taru tace na sakeki babu wanda ya isa ya sakeki. Maganar zuwa gida kuma..."A hankali ya zare gyalen da taketa kara gyarawa, saida ya cireshi ya aje gefe, ya karbi jakar ma ya aje gefe, "Babu inda zaki, muna tare dake daga yau har sati. Kuma dai kinsan hukuncin macen data fita gida bada izinin mijinta ba."

Wani irin mugun kallo take mashi, kuma tana jin yanda yake binta da kallo kamar ta kurma ihu. "Wai dama haka rigar take? Kuma da a haka zaki fita, Ramlah?" Ita batasan ya wuyan rigar yake ba saida ta saka, saida tace ma Lubnah da zasu kai kayan dinki akan zata zabi style amma tace Aa, wai za'ayi masu me kyau. Ita batasan yanda akayi wannan budadden gaba haka ba, kuma koda ta saka sai taki cirewa.

"Me rigar tayi? Naga dai ai ba jikina bane waje ko? Kuma ga gyale can ka ansa ka aje dashi zan tafi ba haka kawai zan fita ba." Sai wasu yan fizge fizge take tana dage kai sama ita ala dole haushinshi takeji. Ita yanzu burinta bai wuce ya gyaleta ko kan kujerar bane ma ta zauna, ga wannan kallon da yake mata kamar zuciyarta ta fito takeji.

"Rashin kunya ko? Idan nace zan fara hukunta ki kan wannan rashin kunyar taki Ramlah duk a wahale zamu kwana." Hararshi kawai tayi, "Naji, ka kyaleni bacci nakeji zan tafi daki." Ta fasa zuwa gidan kenan, a hankali ya furta hakan a ranshi, a fili kuma ya sakar mata da guntun murmushi. "Kiyi baccin anan, idan na tashi sai na ajeki daki."

"Tunda ga kayan wanki ka samu ko? Dan Allah ni ka rabu dani." Fizgewa tayi daga rikon daya mata tana mikewa tsaye, gyalenta ta dauka da jakarta ta koma daki. Koda ta rufe dakin saida ta jingina da kofar ta daura hannu saman zuciyarta. Wani irin harbawa take da sauri, wancan mutumin kafin ya kasheta ita saita kasheshi.

••

Kwankwasawa Lubnah taji anayi, a hankali ta bude ido. Jiya da taimakon Allah ne kawai tayi bacci, dan bayan sun gama cin abincin nan sukawa juna saida safe kowa ya shiga nashi dakin. A hankali ta taka taje bakin kofar ta bude, ganinshi tayi ya shigo da alamar damuwa kan fuskarshi ya maida kofar ya rufe, ko dankwali bata saka ba.

Juyowa yayi da niyar yi mata magana sai kuma ya tsaya yana kallonta ga murmushi kan fuskarshi. "Kinyi kyau." Yar dariya tayi tadan daki hannunshi cikin wasa, "A hakan? naga ka shigo kamar a rude. Ina kwana?"

Jan hannun ta yayi suka zauna bakin gadon tukunna yayi ajiyar zuciya, "Hajia ta aiko mana da breakfast, to shine fa Hafsah ta nace sai ta biyo wai taga Ammin ta. Ban samu lokaci ba na mata bayani kinga yanda abun yazo, bansan ya zamuyi ba." Saida gabanta ya fadi, dan bata taba ma tunanin ya zasuyi da Hafsah ba tunda ita dai Ramlah ta sani.

Jin tayi shiru tana tunani yasa ya dan girgiza hannunta, "Lubnah!" firgigi ta dago tana kallonshi, "Na'am? Sorry ina can ina tunanin mafita. Yanzu me kace mata?"

Dukansu babu wanda ya lura hannayensu a hade suke waje daya har yanzu, "Nace mata bari nazo na tadaki kina bacci kuma zakiyi wanka kafin ki fito. Ko na mata bayani kafin lokacin?" Dan girgiza kai Lubnah tayi, dukansu sunsan irin kaunar da Hafsah takewa Ramlah, "Ko zakace mata ba a nan gidan Ammin take ba? Sai ka kaita can gidan su Ramlar, ni bansan ya zanyi ba." Ko da can dakyar Hafsah ke yarda da ita, sai Ramlah ta roketa da wasa da wasa tukunna, balle yanzu tana saka ran ganinta kuma ace mata ba ita bace ai da matsala.

"Idan na mata haka yau gobe fah? Wata rana dole ta gane, banso kuma taga na mata karya kinsan yaro, Lubnah..." Ajiyar zuciya ta saki, "Dole wata rana ta dawo tana zama tare damu, nan kusa ma. Kawai kace mata bari nayi wankan na fito."

Mikewa sukayi a tare, sai a lokacin ya saki hannunta. "If you're not ready zan iya ce mata baki lafiya kina bacci, kafin nan zansan yanda zan mata." Girgiza mashi kai tayi, gara tayi komai lokaci daya ta wuce wurin, "Aa fah, ai yarinya ce me fahimta. Kawai kace mata gani nan, kuma ka daina yin abu kamar mara gaskia, duk hankalinka ya tashi." Dariya tayi ganin yanda yabi ya rude duk ya damu, sai yanzu take tunanin abubuwan da zasu fuskanta ba kadan ba, ko mahaifiyarshi batasan an chanza Ramlah ba, babanshi kawai ya sani. Ita kam ta debo ruwan dafa kanta.

"Kaje kar taga ka dade," dan turashi tayi a hankali ya rike hannunta kuma. "Komai zaiyi daidai, kinji?" Daga mashi kai tayi tana dan guntun murmushi. "Bari nayi sauri kar tace Ammin tata yar wulakanci ce." Dariya yayi a hankali, "Ko nazo na tayaki wankan?" Wani irin kallo ta mashi kafin cikin hanzari ta shiga toilet din, sautin dariyarshi taji kafin ya fita daga dakin a hankali ta saki wani irin murmushi. It wasn't so bad afterall.

😁😁😁

MIJINA NE! ✅ Où les histoires vivent. Découvrez maintenant