Talatin Da Bakwai

Start from the beginning
                                    

Bata ida magana ba taji ya kira waya, "Lubnah, ta yarda. Ranar saturday su Baba zasu zo sai ki fadawa Mama." Wata irin fara'a ce kwance kan fuskarshi, ji yakeyi yanda kikasan ya tashi ya rungumi Ramlah haka yakeji.

Zaro ido yayi waje, "Na bani, kai wai dama da gaske kake?" Dariya ma ta bashi yanda ta wani zaro ido kamar mugun abu, "Ji yanda kikeyi kamar wani mugun abu, to da wasa nake?" Shiru tayi har yanzu tana binshi da kallon mamaki, komai yazo mata lokaci daya batasan ma me zataji ba. "Ko dai baki sona ne?"

Shekeke ta tsaya tana kallonshi, "To kai din kana sona ne? Ba namiji ke fara cewa yana san mace ba in tace ta yarda to shikenan." Yanda tayi maganar sai ka rantse da Allah yarinya ce yar shekara irin sha shida sha biyar ma. "Sau nawa ina cewa ina sanki? kar dai baki taba ji ba?" Dauke kai tayi daga kallonshi, dan yanda idanunshi kesa gabanta na faduwa ita dai Ramlah bazata iya ba, "Ni ban taba ji ba. Kuma ma a haka ake auren babu tarairaya ba komai?"

Dariya yayi yana mika mata lemun daya zuba a kofi, "Karbi toh kisha, ai duk cikin tarairayar ne ko?" Hararar wasa ta bishi dashi da cup din sai shi yasha abunshi yana dariya. "Toh ina sanki Ramlah, sosai fa ba kadan ba, kinji?" Yanda zuciyarta ta narke kamar zatayi kuka, oh duniya, dama akwai wanda zai taba furta mata wannan kalmar a duniya? Oh ita duniya, haka akeji ashe?

Dariya abun ya bata ta dan murmusa, "Banji ba, ka kara fadi."

Saida yayi dariyar shima tukunna ya furta, "Toh Ramlah, ina sanki sosai da sosai."

Dariya ta karayi kamar wata karamar yarinya, "Da dadin ji, dan kara fada naji dan Allah."

"Zanta fada kullum in kinaso. Ina sanki, Ramlah, ina sanki sosai da sosai, matar likita." Wani kayataccen murmushi suka sakarwa juna. Fira suka cigaba dayi cikin kwanciyar hankali da soyayya tsabtatacciya. Tunda Ramlah take bata taba jin farin ciki irin na yau ba, koda zai tafi kamar ta bishi takeji.

Abu kamar wasa ya zama babba, yanda yace zasuzo din ranar asabar din bayan Mama ta kira yayye da kannen ta sai gasu sunzo din. Ba'a tsaya wani dogon zance ba aka saka bikin hade dana su Lubnah, ita dai kallonsu take suna shagalinsu, ga dadin a cikin ranta amma haka bai hana tsoron me zai faru ya dabaibaye mata zuciya ba. Ita tana gudun abunda ya taba faruwa da ita ya kara faruwa, dukda cewar tasan halin Dr Aliyu da wuya ace ya mata mugunta amma dukda haka.

Ranar Monday da sassafe Lubnah ta tafi wajen aiki, Ramlah ma ranar zata fara zuwa shago ance mata an gama komai da komai. Ita duk daukarta direba yana nan, saida ta fito tukunna ta lura baya nan da alamu Mama ta fita dashi. Kallon sauran motocin dake wajen tayi, gasu dai, ga kuma makullansu tasan inda suke amma har yau Allah bai bata ikon koyan mota ba. Gashi kuma wanda sukayi booking photosession sai kiranta sukeyi kaman ta tsinke.

Bata lura da motan Rayyan a wajen ba saida ta ganshi ya fito a hankali yana takawa wajen motar, da hanzari ta kira sunanshi, "Rayyan! Dan Allah tsaya." Rabon data ganshi kila tun ranar da suka dawo, kusan sati daya kenan. Ko cin abinci ya daina shigowa yanayi ko Lubnah ke kai mashi bangarenshi oho.

Tsayawa yayi yana kallonta kamar wanda ya shekara goma bai ganta ba, ko tunanin me yakeyi oho. Ita dai ba wannan bace damuwarta, damuwarta bata wuci ya taimaka ya ajeta ba, idan zata dawo Dr ya maido ta gida. Saida ta tsaya a gabanshi tukunna ya dauke idanshi daga kanta, "Dan Allah wajen aiki zaka? Ko zaka ajeni shago? Mama ta fita da drivern."

Bai ko kalleta ba yace "muje." Tunda suka fara tafiya babu wanda yayi maganar cikin motar, ita jin shirun yayi yawa yasa ta juyo ta kalleshi taga ya hade gaban da yamma, ita in aka tambayeta ma zata iya cewa yanda yayi kicin kicin da ido to bai ganin gabanshi. "Wani abu ya faru ne? Naga duk yanayin ka ya chanza, ko cikin gida na daina ganinka." Ita ba dan wani abu ta mashi magana ba, a tunaninta dai kawo yanzu ai sun zama abokai ko?

Bai bata amsa ba saima ya gangara gefen titi ya tsaida motar, waigawa tayi tukunna ta kara juyowa tana kallonshi, "Wani abu ya samu motar ne?" Dagowa yayi yana kallonta da idanunshi wanda sun rine sunyi ja kamar wanda ya kwana yana kuka. Cikin kidima ta yunkura, "Subhanallah, Rayyan baka lafiya ne? To ai da baka fito ba ko? Dana jira ko na kira uber tazo ta kaina." Sam hayyacinta baya jikinta neman riko hannunshi take domin taji lafiyarshi kawai ya buge hannunta, nan take wani kududu ya kafe mata zuciya.

Dagowa yayi da rinannun idanunshi ya saukesu a kanta, wato tambaya ma takeyi akan abunda yake damunshi ko? Tunda yaji wai an saka ranar aurenta da Dr duniyar gaba daya ta daina mashi dadi. A da ya dauka abun duk na wasa ne, zai iya jurewa ya auri Ramlah itama taje ta auri wanda takeso, amma yanzu ji yake kamar ya fiddo zuciyarshi waje tasha iska ko ya samu sukuni.

"Tambayata ma kike abunda ya sameni? To lafiya ta lau. Kinsan mi?" Waige waige ya farayi yaga idan wurin da suke is safe ya ajeta yayi tafiyarshi, dan shi ganinta kawai ma da yakeyi ba karain rura wutar azaba yake mashi ba. Wani irin tsakin takaici yaja ga kuma haushin kanshi ma da yakeji, abun haushin ma bata san yanayi ba. Tada motar yayi suka cigaba da tafiya, ita kuwa sai binshi takeyi da kallon tsoro da kuma mamaki har suka isa bakin shagon.

Koda ya tsaida motar babu wanda yayi magana a cikinsu. Shi baice ta sauka ba ita kuma bata sauka din ba, karshe ma tura ma mutanen text tayi akan traffic ne ya tsaida ta su bata minti biyar. Kallonshi kawai takeyi, ba tun yau ba tana lura da damuwa tattare da Rayyan. "Rayyan," ta kira sunanshi a sanyaye, duk yanda yaso ya shareta haka zalika ya mata hargagi akan ta fita ta bar mashi mota kasawa yayi, dagowa yayi a hankali yana kallonta itama ta saka idanunta cikin nashi. "Me yake damunka ne wai? Kasan dai zaka iya fadaman matsalarka kaman yanda nake fada maka tawa ko? Ba sai na tambaya ba kana da matsala, wani abu yana damunka, menene?"

Ji yake kamar ya fashe da kuka, wato tausayinshi ma takeji, danma batasan abunda yake faruwa ba kenan, kila dariya zata mashi ko? Tunda ita dai ai tanada wanda takeso. Shiru ne ya ratsa tsakaninsu, a hankali ya girgiza mata kai alamar bazai iya mata maganar ba.

"Wani abu ne ya samu Maryam? Ko yan biyu? Mommy ta maku wani abu? Ko Aasim yayi wani abun again?" Jin ya kara shirun yasa tayi magana da muryar wanda kesan yayi kuka, "Dan Allah kamun magana, ka fada man abunda ke damunka. Be zama lallai inada maganinta ba amma ko addua na maka ai ya wadatar ko?"

Wayarta data fara haske ya kalla, "Kije mutane na jiranki." Da kyar ma haruffan suke fitowa daga bakin, wani irin tausayinshi taji ya kamata, ko menene yake damunshi? Oho.

"Kayi alkawari idan na dawo zamuyi magana ko? Ko ka fadawa Lubnah inma ni bazaka iya fada man ba." Shidai daga mata kai kawai yayi, dukda bai gaji da ganinta ba amma so yake ta fita ya samu yaji sauki a ranshi.

Kaman bazata fita ba sai kuma ta fita. Tana shiga shagon da murmushin karfin hali saman fuskarta. "Kuyi hakuri dan Allah na sakaku jira ko?" Bata ida maganar ba taji kaman numfashinta zai tsaya. Yassar ne zaune sai matarshi gefe amma kuma yarinyar dake hannunshi ko duniya zata taru tace mata ba Hanan bace lokacin da tana yarinya bazata yarda ba. Wani irin baya baya tayi luuuu zata fadi, shigowar Rayyan kenan da jakarta data manta a hannu yayi hanzarin rikota yana kallon Yassar da alamar tuhuma. 

MIJINA NE! ✅ Where stories live. Discover now