Rayuwa mafi hatsari Masu karatu sai kunyi hakuri donkuwa labarin yanada tsauri Sosai dakuma kalu bale mai tarin yawa..... Sarham marainiya ce haka Zara Kuma Allah ya jarabcesu da fadawa hannun hamshakiya Hajia Zahira Wanda takara gurbata rayuwarsu kaca kaca... Suhaima ma marainiya ce wacce bata da wani gata sai Allah haka itama Hajia Zahira tayi Mata barazana don samun amincewarta a cikin kungiyarta.... Sha'aban shine Babban da ga Hajia Zahira yanada matukar jinkai magana ma kamar a karba ayi mashi, Allah zai dora mashi soyayyar Sarham shin Kuna ganin Hajia Zahira zata Amince kuwa??? Wani hali Zara zata shiga? Sarham zata Amince da tayin Sha'aban? ya suhaima zata tsinci kanta? Wannan littafin ya kunshi soyayya kala biyu kuma muna fuskantar wannan al'amari a ko ina....