NADAMA 5

12 2 0
                                    

Na: Reedahmz
5

Zara tana dawowa tawuce dakinsu tasa Lock tafara hawaye jinta takeyi kamar batada Lafiya saboda rashin Sarham a kusa da ita kokadan takasa samun sukuni daga zuciar ta, sannan batada wani kuzari tadauki waya tadauko hoton Sarham tasa a gaba tana kallo har bacci barawo ya saceta...

Suhaima takira Ummy suka gaisa tace da ita yaya abin naku tace Alhamdulillah Allah ya miki Albarka yakareki Amin Ummy na, Ummy tace kwana nawa zakiyi? Suhaima tace sati dayane.. Allah ya kaimu Amin Ummy idan Hayat yadawo ace ina gaishe dashi. Zaiji in sha Allah kidinga kula saina kira.

Hajia Zahira tace da Hajia Zuwaira nifa gaskiya dabarar dakika yi yamin dadi don nakasa gane wata alaqa ce ke tsakanin Sarham da Zara, shiyasa da aikin yazo na rabasu saboda ingane, Hajia Zuwaira tace ai kinsan Sarham da wayo da fahimta intaso baxata baki haske ba, zagane a hankali.....

"Imo state"
Nafisa in charge din aikin suna sauka mota yazo daukar su a airport zuwa gida Mr Charles dukkan su bakin gilashi ke manne a idon su da face mask gudun lalacewar hanya a haka suka har masaukin baki suka huta sukayi zaman jiran Mr Charles a gidan nashi.. yana shigowa suka mike bayan sun gaishe shi, Nafisa tabude mashi kaya yaduba sosai sannan yace komi yazo dai dai kuma yanzu zasu wuce hotel su kwana, don gobe zasu fita da kayan Sarham ta zaro ido tace Boss bamuyi haka da Mamie ba niban shiryawa fita ba gaskiya.... Nafisa tace scorp aikinan fa ba karamin riba zamu samu ba, dayake sunan Sarham na kungiya kenan scorpion , Sarham tace Ko ma Yaya ne kinsan ai is risk wannan layinki ne da goga. Nafisa tayi text wa Hajia Zahira yadda ake ciki , daganan Hajia Zahira takira tace a hada ta Sarham Nafisa tabata waya sukayi magana tace toh sukayi sallama.. Ashe Hajia Zahira cewa tayi matukar tabata aiki ko taki zuwa a bakin rayuwar Zara! Shiyasa ta Amince bayan haka Zara ce kadai ta rage Mata. Dauko wayarta tayi don tura text.

Hi girlfriend! munzo lafiya wayata ce nasa flight mood kuma muna ta discussing. Please Ina fata bakiyi kuka ba kuma kinci abinci ko, ok please kisani cikin addu'a Ina kaunarki fiyeda yadda nike son kaina Rayuwata ce ke, Ashe aikin mu ba iya wurin Mr Charles kawai ya tsaya ba sai munfita, banda mafita kisani a addu'a kawai nace Mamie banzuwa Amma tamin bayani yadda aiki zai kasance (Sarham ta boyewa Zara barazana irinta Hajia Zahira) please kikulamin da kanki zankira ki in the next 30min in sha Allah Love you xoxoxo ️🤍❤️❤️🤍
{Sarham}

Suhaima ta kalli dakin tace lallai duniya ta mutu anan Amman duk da wannan tarin dukiya mataranan take bin wani hanya don tara kudi? Toh mitake nema ne wanda batasamu ba? Allah kara bamu da son zucia irin namu na yan Adam can Text yashigo daga Hajia Zahira akan tashirya anjima zasu fita aiki da Zara ...Tayi shiru tace Allah kacireni..

Zara kwance tana ta tunanin Sarham sai juyi take bisa bed rungume da pillow idonta duk yayi red gashi tayi ta kiran Sarham akashe, tabude text din farko na Hajia Zahira ne tayi tsaki tafita tabude dayan tana ganin text din Sarham ta tashi tamike zaune tayi murmushi tafara karanta sakon tana gamawa tamike tsaye, "Tace nasan za'a yi a haka shiyasa gabana ke faduwa ohhh my God nan tafara dialing number din Sarham amma is not reachable tana ta kai gwauro takai Mari Girlfy kibude wayar ki minti talatin yamin yawa cikin wannan safa da marwa kiran Sarham yashigo, murna tafara yi dasauri tadaga.....
Sarham: Girlfriend I so much Miss you!
Zara: ajiyan zucia tayi tace Girlfy cikin karamar murya jiajia kika tafi amma inaji kamar shekara
Sarham: Am sorry Yan Mata ya komi ina Mamie?
Zara: Hummmmm tafita amman Kinsan haryanzu ban yarda, da tafiyar ki ba...
Sarham: Please calm down bakomi kimin addua kuma kiyaye aiki ta inda kike
Zara:ok Girlfy i will
Sukayi Shiru na wasu lokacin kafin Sarham tace: Girlfriend kikulamin da kanki sosai idan lfy koda rai zakiji.
Zara:Don Allah fadamin kinji my besty
Sarham tayi Daria tace Ina Kaunarki kimin alkawari babu sabuwar kawa dazakiyi banso musamu 3rd party.. zamuyi wata daya
Zara: tace toh Girlfy Allah yatsareki yakareminke Amma wata daya yayi yawa anyway Becareful please! Sarham tace I will and you too sukayi sallama...

Mr Charles yahada komi yabasu suka wuce ko Ina na airport din sai kasar America Bayan sun sauka a airport Sarham da Nafisa aka fara checking kayan su dasu kansu bayan anzo kan Sarham jakar hannunta ashe sun samata cocaine bata sani aikuwa ana kamawa akayi ram da ita tace ita batasan dashi ba tace ga abokiyar tafiyarta Nafisa tace ita ba tafiyarsu daya bane saboda ta tuna kashedin Hajia Zahira idan suka sake suka bari aka kama mutum daya, nan Sarham tayi mamaki aka wuce da ita don bincike tana zubar hawaye. Tarasa sukuni gabaya...

NADAMAWhere stories live. Discover now