NADAMA (11)

6 1 0
                                    

***Na: Reedahmz**
**NADAMA 11**

Zara duk ranta yayi dubu yabaci Amman tace bazata biyewa Sarham ba wallahi project dinta zatayi kamar yadda tace tayi nata kawai haka zatayi kuma bazata nemeta a waya ba kokadan.... miyasa Sarham zata dinga fifita bukatar Hajia Zahira bayan tasan ga abinda ke gabansu Amman bakomai zatayi project dinta tagama, ta kwanta abinta tadauki tacigaba da latsawa takira wata course mate dinsu tana tambayar ta wasu abubuwa, Bayan sungama waya tamike don neman abinda zatasawa cikin kafin tashiga school taga mike tafiya. Tana kicin suhaima takirata a waya take shaida mata cewa zata wuce Abuja nan da 2days, Zara tace ohh kema takiraki kenan? Suhaima tace ehh ni nadauka kema kintafi ne? Zara tace Aa Girlfy kawai tace tazo, don ni ko dani a tafiyar bazan je ba gaskiya saboda ina kan gabar project. Suhaima tace toh nidai tace inbar komi, Zara tace yakamata sukayi sallama.

Sarham: Mamakin Zara ne ya cika mata zucia, wato yarinya wuyanta yayi kauri zatace wai nayi yadda nikeso, kodayake akan gaskiya take fa nice nabata mata inji wata zuciar kenan. Cikin jirgi tanata sake sake tarasa sukuni yau itace ke tafiya Babu rakiyar girlfriend dinta? Ga sakon Nadia namata yawo cikin kai, wayyo Allah tadafe kan bata Ankara ba taji announcement sun iso Abj.

Hajia Zahira: Cikin dakin barcinta Sarham tashiga tasameta tayi hugging dinta tace Mamie am back, H Zahira tace welcome back my dear ya Zara sarkin rikici? Sarham tace she's fine tana batun project May be idan tagama zatazo, Hajia Zahira tace ohh nagane badamuwa yanzu kije kici abinci kiyi wanka... Sarham cikin dakin su ta rungume blnkt tana shakar turaren Zara idon ta a rufe tace girlfriend I missed you so much nasan kinfini gaskiya cikin wannan tunanin kira yashigo, tana dubawa taga Nadeey!!! Dasauri tayi picking tace hello Cikin murya maidadi Nadeey tayi ajiyar zucia race sweet I missed you so much wallahi Ina wahala a can I think I'm coming back this week, Sarham tace Amour bake kadai ba ni all my thinking kinyi sabuwar catch ne, Nadeey tace no never ke kadai ce kika iya ni kece rayuwata! Sarham tace you know what? Ina tsoron Mamie tasani, Nadeey tace and so what Sweet Nice fa Zan iya komi akanki infact nazneen cemin take inda itace da tadade dayi maki umarnin zuwa. Sarham tayi murmushi tace nasani kinada muhimmanci a rayuwata nagode Amour. Nadeey tace hmmmmm Ina Zara? Sarham tace tana Yola Nadeey tace gaskiya idan nadawo zandauke ki muyi week tare fa, don nayi missing dinki. Sarham tace inasa rai gaskiya I love you so much muahhh! Take care sweet bye.

Manaf: Zaune yakira nazneen suka gaisa yace shifa zai dira Nigeria cikin satinan shida Sha'aban if zasuje su siya Masu ticket, Nazneen tace a siya gaskiya Ina Big bro din? Manaf yace yatafi siyayya wai ok no prob my greetings sai mun hadu Airport. Regards to Nadeeya ok I will bye.

Zara: Ta koma gida daga school tana kwance tafara tunanin shin wani irin muhimmanci aikin da Hajia Zahira take dashi harda zai sha gaban project din Sarham yadda taci buri wa karatun ta? Amman tabbas saita bincika don bazata bari ace tana zaune kamar hoto ba tagaji tana bukatar Girlfy kusada ita, nan tadauki waya bugu daya aka daga tace Jadore kana ina yace Ina birnin Tarayya akwai motsi ne? Aa fa wani bincike nikeso kayi min please! Yace akan miye tace yawaa... Wani aiki za'a yi soon a gidan mamie? Jadore yace Kuma aikin Babu Wanda zaiyi sai Sarham sannan naji kamar gidan Alh Umar yawuri ne, Zara tace godiya nike sosai Jadore inasonka saboda kanada Amana yace kinfi haka Zara ban manta yadda yakika cire ni a cikin tsumma ba. Zara tace please Jadore manta inason a bata aikin ne don Allah, yace Zara aikin Sarham fa baya baci kinsani, shiyasa Boss take sa ta duk aiki Mai hatsari saboda zata bulle... Zara tace nasani Amma ni zanyi yadda zanyi tayi failing a Wannan matakin don Allah, Jadore yace na amince Amman bibiyarta zanyi kenan takowani hali? Zara tace hakan nikeso, Kuma inaso kasamo min number din Alh Umar yawuri yau dinan! Jadore yace angama. Amma yaushe zaki shigo Abuja? Tace nanda jibi Amman bazanje gida ba saboda gudun bacin wannan aikin, yace bakida matsala in sha Allah.

Hajia Zahira Zaune bayan takira Sarham saikuma Hajia zuwaira da uwani iyayen kankanba! Hajia Zahira tace Scorp basaina maki bayani akan irin aiki danike so kiyi ba, matukar kikaji nace zandora ki akan aiki ke daya, toh kisani banason wasa a ciki.. Sarham tace Alh Umar yawuri haifaffen Jahar Kebbi ne a yawuri,yanada Mata daya da Yara uku, Safina Ahmad da Hamid... Hajia uwani tace dakyau dota... Hajia Zahira tace sonake aiki yafada akan diyar shi tilo! Sarham tayi murmushi tace Wani irin aiki kikeso Mamie? A gurbata ta, kokuma a lalata gabadaya, Kokuma a yimata sharri? Hajia zuwaira tace Sarham nasanki akan aikin ki baki wasa. Hajia Zahira tace sonake a samata cocaine mai mugun nauyi cikin box dinta don zatayi tafiya zuwa kasar Amurka, wanda duk dukiya irinta Yawuri bazai iya kwatota ba!!! Sarham tace angama Mamie am, sannan shi kanshi Yawuri Inaso kifara soyayya dashi don samun damar bata mashi siyasar shi. Suka fashe da dariya duka, Hajia Zahira tadauki waya ta turawa Sarham sako , tana budewa taga alert din 3m tace ki rike wannan, Sarham tace Mamie Ina da kudi basai kinbiya ni ba. Hajia Zahira tace kyauta ce kawai Good luck!!! Bayan fitar ta Hajia zuwaira tace Amman Zara tasan wannan aikin dazaki sa masoyiyarta kuwa? Hajia uwani tace Anya kuwa don idan tasani zatayi tijara kinsani, Hajia Zahira tadubesu duka tace ai idan banda ku da ni sai ita Sarham Babu wanda yasan wannan aikin.... Hajia zuwaira tace toh shikenan Allah ya bamu sa'a. Duk wannan hirar sunayin shine a dakin sirri datake ganin baki already Jadore kuwa yasa recording ya nadamashi don turawa Zara..

Suhaima tagama shiryawa Ummy karya tsaf don tafiya Abuja, itakuwa ta amince don tunanin ta kudi da akesamu a aikin datace, wayarta tadauka takira Zara ta sanar mata akan zata bar gida yau dama flight dinta na Yamma ne so tunda gidan su na hanyar airport zatazo tajira time Kawai, Zara tace normal saitazo din. Suhaima tayi sallama da gida tawuce gidan Zara tasamu Zara kwance tana latsa wayarta. Bayan sun gaisa takawo mata abinci tana ci Suna hira... Zara tace suhaima kunyi magana da Mamie ne??? Aa bata kira ba Suna ciikin magana saiga call din Hajia Zahira, suhaima tadaga tace Ranki yadade Barka da warhaka suka gaisa tace karki Manta jirgin yamma zaki bi tace nasani toh Allah ya kawoki lfy Amin ta aje wayar.. Karfe 5 Zara tadauke ta zuwa airport a hanya Zara kece Mata kikula kuma ki kiyaye akan duk aikin dazakiyi. Tace nagode sosai sukayi sallama Zara tajuyo gida har magrib Yayi, tashiga gida Jadore yakirata yace da ita number tasamu sannan kihau WhatsApp inada haja tayi daria tace nasani banda ja akanka bana shakkar aikinka... Bayan tahau yatura mata voice tace shikenan yanzu za'a buga match dinan! Am sorry Girlfy dole indinga tunatar dake wataran matarnan zata barmu, nan tayi booking flights dinta na safe...

Jadore ne yadauko ta a airport zuwa boyayyen masaukinta. Bayan tayi wanka taci abinci saitayi dialing number din Safina Yawuri bugu biyu aka daga, yace hello Zara tace please ina magana da Safina Yawuri ce? Safina tace yeah nice wacece? Tace Sunana Zara munhadu dake weeks back in Yola a wani eatry. Safina tace wowwwww Ashe zaku neme ni? Zara tace yeah gashi kuwa na nemeki, Safina tace it was nice meeting you. Zara tace The pleasure is mine. Safina tace hope kina shigowa Abj? Zara tace of course yes yanzu ma ina cikin Abj.. Safina tace awwwwwwn gaskiya yakamata muhadu yau dinan Zara tayi murmushi tace bakida matsala. Just text me the address, Safina tace alright I will later thank you for calling. Bayan taje waya tace Jadore kaga aikin farko yayi koh? Jadore yace Sosai kuwa saura mataki na gaba wurin haduwa dole idan ta turo address ka ziyarci wurin kafin not! Yace bakida matsala.

H&H Continental by 9pm
      Feena Yawuri.

Zara tace Jadore wurin haduwa H da H lokaci 9 zakaje 7:30 zanzo 8:30 but bazan bayyana ba saina ga isowarta... By then zamu dora a VIP... Yace angama Boss tayi murmushi tace Girlfriend banaso kicigaba da biyewa Hajia Zahira ne am sorry am going to destroy your work!!!

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 22, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

NADAMAWhere stories live. Discover now