DARE DUBU

Per PrincessAmrah

11.5K 1.5K 68

Kaddara! Mece ce ita? Yaya rayuwar yarinya mai karancin shekaru za ta kasance a lokacin da ta tsinci kanta ci... Més

PROLOGUE
Page 01- Khairi
Page 02- Damuwa
Page 03- Fargaba
Page 04- Mafarin Komai
Page 05- Masauki
Page 06- From God We Are...
Page 07- Tushiya...
Page 08- Zalunci
Page 09- Dream
Page 10- Fushin Masoyi...
Page 11- Kewa
Page 12- Samu da Rashi
Page 13- Mafita
Page 14- Assignment
Page 15- Kudin Fansa
Page 16- Daren Farko
Page 17- Headmaster
Page 18- Tarko
Page 19- Kura Da Fatar Akuya
Page 20- Plan
Page 21- Suspect
Page 22- A Week To Go
Page 23- Informers
Page 24- Bankwana
Page 25- Kiran Sirri
Page 26- Arrest
Page 27- Dare Dubu
Page 28- Next Assignment
Page 29- Soyayya
Page 30- Visiting
Page 31- Alkalamin Kaddara
Page 32- Nusaiba
Page 33- Baby Boy
Page 34- Matar Haidar
Page 35- Award Morning
Page 36- I Love You
Page 37- Kambun Baka
Page 38- Kai Amarya
Page 39- Kukan Zuci
Page 40- Reconciliation
Page 41- Karshen Munafuki...
Page 42- Ruwan Zuma
Page 44- Happy Birthday
Page 45- WTTW
Page 46- Barrista Khairi
Page 47- Rama Sharri da Alheri
Page 48- Kauyawa
Page 49- Court
Page 50- Luck
Page 51- Babbar Kotu
Page 52- Medical Report
Page 53- Doctor Marzuq
Page 54- Shaidar Zur
Page 55- Confess 1
Page 56- Confess 2
Page 57- Wata Sabuwa...
Page 58- Women Leader
Page 59- Bakar Manufa
Page 60- Komai Ya Yi Farko...

Page 43- Class Rep.

155 26 3
Per PrincessAmrah

Page 43

Mun jima a asibitin, don har goma ta wuce ba mu tafi ba sai da Mami ta ce wai ba za mu tashi mu wuce ba saboda dare. Sannan ne muka yi musu sallama muka kama hanyar gida.

Ko a cikin motar ma hannuna yana makale cikin nashi haka ake tukin. Na dai fahimci sosai yake son in kasance a cikin jikinsa, kamar hakan yana yi masa dadi. Na kuwa kuduri aniyyar zama cikin jikinsa tunda yana so, babban burina shi ne ganin shi cikin farinciki, yayin da na tsani ganin kunci komai kankantarsa a saman fuskarsa.

Washegari Umma ta je ganin Mami a asibiti, sun ji dadin ganin juna, cike da nishadi suka rabu, na raka Umma har bakin keke napep din da ta sa ya kawo ta ya jira ta. Haidar ya ba shi kudinsa sannan muka koma cikin asibitin zuciyata fal da farincikin yanayin haduwar ta iyayena guda biyu.

Bayan kwana biyu aka sallami Mami bayan ta ji sauki sosai.
Haka dai kwanaki suka ci gaba da shudewa har zuwa lokacin fara lectures dinmu. Ranar farko Haidar da kansa ya kai ni makarantar kuma lokacin tashi ma ya je ya dauko ni. Haka rana ta biyu ma. Daga nan kuma sai ya dinga sanyawa a kai ni a dauko ni. Ganin duk hakan ba zai yi ba ya sanya shi fara koya min tukin. Cikin sati uku hannuna ya goge.
Ranar ina dawowa daga makaranta sai ga dalleliyar mota kirar vibe kalar ruwan siminti girke a parking space. Shi da kansa ya janyo hannuna daga cikin motarsa ya kawo ni har gaban motar, ya yi min albishirin cewa tawa ce halak malak.
Ai ban san sadda na yi masa kyakkyawan runguma ba hade da sumbatarsa.
"Thank you so much sweat heart, Allah Ya saka maka da alkhairi."
Na ma rasa inda zan tsoma raina saboda murna.
A take na kira Umma na shaida mata, ita ma din ta yi murna sosai ta ce in ba shi wayar ta yi masa godiya kafin mu je kai mata motar har gida ta gani, don ba za ta iya zuwa gidana da sunan ganin motata ba.
Daga nan na kira Mami, cikin nishadi nake shaida mata an saya min mota, kamar ma ta so ta fi Umman murna, ta sanya mana albarka sosai tare da fatan alkhairi.

Ai ranar ya ga yadda ake nuna farinciki, a jikinsa na karasa wunin, haka da dare ni na aikata duk abin da ya saba aikatawa a saman shimfidarmu. Da safe weekend ne babu makaranta, sai ga su Safra sun zo ganin mota. Haidar ya ce mu fita in dana su. Mu duka muka fice har shi, ni nake tuki yana zaune a gaba, sai Safra da Sadiya baya.
Mun sha yawo sosai kafin muka wuce gidan Mami. Nusaiba ta ce me ya sa ba mu fara zuwa mun dauke ta an yi yawon da ita ba. Na ce
"Ki sha kuruminki kanwata, naki ai na musamman ne. Sai mun zagaye kaf Katsina."
Aka sanya dariya har da Mami.
Ana cikin haka sai ga Hannatu ta zo. Cikin walwala muka gaisa ta ce ai har gidana da ma Nusaiba za ta raka ta. Na ce sai mu tafi tare tunda yanzu za mu tafi.

Da muka koma ma nishadin muka ci gaba da yi har dare. Haidar ya tafi da su duka har su Safra ya kai su gida sannan ya dawo.

Duk duniya babu wanda yake cikakken goma, amma zan iya cewa Haidar ya zarce goman da mutane ke fadin mutum tara yake bai cika goma ba. Bai taba nuna min bacin ransa ba duk zaman mu, abu daya da na fahimta shi ne yana da kishi, to sai na kiyaye duk wata kafa da za ta darsa masa kishin ballantana har bacin rai ya gitta a tsakaninmu.
Koyaushe ina kokarin ganin na faranta masa, kamar yadda burinsa a kullum bai wuce ganin murmushi shimfide a saman fuskata ba.

Ranar wata Asabar na tashi da matsanancin zazzabi, irin mai tsananin zafin nan. Bakidaya hankalinsa ya tashi, masallaci ma kasa fita sallar asuba ya yi, cikin jikinsa nake har gari ya karasa wayewa. Shi da kansa ya shiga kitchen ya soya min plantain da kwai, sannan ya hada min shayi mai kayan kamshi tunda ya san madara ba ta dame ni ba. Duk jikinsa babu walwala saboda ciwon nawa.
A hankali ya tasar da ni zaune, ya hau ba ni a baki. Sai dai a loma ta biyu, na wanke sa da amai tun daga kan kirjinsa har zuwa bisa cinya.
"Sannu..."
Kawai yake ce min. A fuskarsa babu ko alamar nuna jin haushin aman da na yi a jikinsa, duk da yadda nake jin cewa maza sun tsani amai.
Plantain din yake kara sa min a baki yana fadin,
"Daure ki ci ko ita kadai ce Buttercup. Saboda mu je asibiti ko?"
Na gyada masa kai. Don a yadda nake ji na ko na kara ci wani aman zan yi. Duk yadda ya dage a kan sai na ci ban cin ba, saboda ba na son na sake wanke shi da wani aman. Dole ya kama ni ya mikar muka nufi toilet.
Shi da kansa ya yi min wankan, da muka fito ma shi ya shafa min mai ya ciro min bakar abaya, khumra ya shafa a jikina sannan ya zura doguwar abayar ko inners bai tsaya nema ba. Ni ma kuma saboda zafin jikina, ga rashin kwari ya sanya ban koma ta kan sai na sa inners din ba.
Ya kama ni ya kwantar, ya ce,
"Ki jira ni yanzu in yi wanka sai mu tafi asibiti."
Har ya juya na kama hannunsa, cikin sanyin murya, hade da kyarmar zazzabi na ce,
"Kai fa...ba ka ci komai ba."
Ya gyada min kai.
"Ke ma ba ki ci komai ba babydoll. How do you expect me to eat something alhali ke ma babu komai a cikinki?"
Ya fice kawai.

Babu jimawa sai ga shi ya dawo da makullin mota a hannunsa. Dauka ta ya yi ya kai mota ya kwantar sannan ya dawo ya rufe gidan. Mai gadi ya bude mana gate tare da nufar Alheri clinic.

Abu na farko da aka yi min shi ne gwajin ciki. Sai ga shi baro-baro ina da shi har na sati biyar. Da ma na yi tsammanin hakan, don tun satin da ya gabata ya kamata in yi period amma shiru bai zo ba. Sai kuma ga wannan zazzafan zazzabin mai hade da ganin jiri da tashin zuciya.

Doctor da kansa ya yi masa albishirin ina dauke da ciki na sati biyar. Kallo na ya yi ya saki murmushi, sannan ya juya ya kalli doctor din, yana ma rasa abin da zai yi.
"Wannan ciwon nata shi ake kira da laulayin ciki. Yana da wahala sosai amma in shaa Allahu da zarar cikin ya cika wata uku shi kenan duk wata wahala ta kare. Allah Ya inganta."

Tun daga nan sai wani irin lele da Haidar ke nuna min. Duk sadda ya fita idan zai dawo haka zai riko kayan kwalama kala-kala, dangin su gasasshiyar masara, dafaffiyar gyada, yalo, da sauransu. Wani bisa wani haka nake ajiyarsu.
Har Maminsa aiko min kayan kwalama take yi, haka Umma ma. Saboda duk sun gane ciwon mene ne a lokacin da ya fada musu ba ni da lafiya. Na so ya mayar da ni gida wurin Umma in yi jinyar, saboda ko kamshin gidana ba na so, amma firfir ya ce bai san da wannan zancen ba. Tare muke jinyar da shi, idan yana office rabin hankalinsa na kaina, ko dai muna waya ko kuma video call.
Sosai na kara shagwabe masa, hakan kuwa ba kadan din kara rikita shi yake yi ba. A karshe dai Nusaiba ce ta dawo gidan tana taya ni aikace-aikace. Mami kullum sai ta kira ta ji ya jikina. Anti Maryam ta zo ta kawo min wani magani Metoclopramide ta ce zai saukaka min amai sosai saboda shi ne abin da ya fi galabaitar da ni.
Hannatu ma tana zuwa sosai sai dai ta ce Mamanta ba ta taba sanin gidana take zuwa ba, wani lokacin ma daga makaranta take yowa nan. Idan ta tashi sai ta ce mata gidan Mami ta je.

Wannan maganin da na fara sha ya kawo min saukin amai har na ci gaba da zuwa makaranta. Sai dai wani lokacin a galabaice nake dawowa saboda zirga-zirga da gajiya. Kuma ko da zan dawo Nusaiba ta yi abinci sannan ta gyara gida tsaf. Zama na tare da Nusaiba ba karamar shakuwa ya kara mana ba, da a ce duk kannen miji haka suke tabbas da an ji dadi. Idan abu na dauko caraf za ta karba daga hannuna ta kai min har inda nake so. Haka muka ci gaba da rayuwa har cikina ya cika wata hudu ya shiga na biyar. A lokacin ne kuma Nusaiba ta koma gida saboda na ji sauki sosai ba ni da sauran wata matsala. Mun yi hutun first semester har mun koma.

Ina zaune tsakiyar parlor da takardun handouts barbaje ina dubawa saboda CA da za mu yi gobe, na duba agogon wayata na ga karfe goma har da rabi. Tuni Haidar ya kashe kallo ya shiga daki saboda da sassafe zai fita gobe.
Na ci gaba da dubawa ina yi ina hamma, yaron cikina sai motsi yake da alama shi kansa ya so kwanciya.
Motsin bude kofa na ji, na daga kai na ga Haidar ne. Fuskarsa babu walwala ya dube ni ya ce,
"Ki ajiye takardun nan ki zo ki kwanta, dare ya yi fa."
"Ka yi hakuri baby boy, na kusa gamawa da wannan shafin sai in taso."
Bai ce komai ba ya gyada kai kawai ya shigewar sa.

Fiye da minti talatin sai ga shi ya sake dawowa, kai tsaye ya iso gabana ya fara tattara takardun ba tare da ko ta kaina ya bi ba. Sai da ya gama hadawa sannan ya nufi wurin kashe wuta, daidai zai kashe na roke shi,
"Please sweatheart, ka taimaka in karasa da wannan shafin, wallahi na yi alkawari daga shi zan kwanta. Saura kiris, kuma daga na tashi dukkan wanda na karanta din zai fice daga kaina. Please baby boy."
"30 minutes, idan kika wuce hakan zan zo in dauke ki duk nauyin nan naku."
Ya saki guntun murmushi ya shige dakin.

Ina cikin dubawa sai ga kira ya shigo wayata, na duba na ga class rep ne, na yi mamaki kwarai, saboda dare ne har sha daya ta wuce, kuma ya san ni matar aure ce amma yake kira na. Ban san dalilinsa ba don haka sai na dauka da sallama a bakina.
"Ki yi hakuri na kira ki cikin dare UmmulKhairi, da ma an canja time na CA din gobe ne, karfe takwas malamin nan ya dawo da ita. Na tura a group tun dazu amma na ga kamar ba kya kusa, kuma ya ce in tabbatar da kowa ya sani, shi ya sa na kira ki."
Na sauke ajiyar zuciya jin dai lafiya. Na gode wa Allah da na nace wa karatun, don da har na ce sai da asuba in yi  kuma dai na daure nake yi din yanzu.
"Thank you so much class rep..."
Ban karasa rufe baki ba na gan shi, tsaye yake ya harde hannuwa, fuskarsa tamkar bai taba murmushi ba, idanuwansa a cikin nawa, babu alamun walwala a cikinsu.
Bakina ya dinke dif, na kasa ba shi amsar sai da safen da yake yi min na yanke wayar, hankalina na tashi saboda yanayinsa.

Takowa ya yi a hankali ya iso inda nake, ya karbi wayar ya ga sunan class rep, sannan ya dawo da kallon shi gare ni.
"Wannan ne karatun? Waya da class rep da ma shi ne karatun da kike ta roko na in bari ki karasa?"

(Thank you masoyana. Masu tunanin labari ya zo karshe su daina, akwai sauran aiki. Kar ku manta har yanzu akwai abin da ba mu warware ba)


Amrah A Mashi❤️

Continua llegint

You'll Also Like

234K 9.7K 25
"မောင် မဆိုးစမ်းနဲ့ကွယ်" "ကျုပ်ကိုမချုပ်ခြယ်နဲ့"
43K 3.6K 37
"Baba meyasa kazama boka bokanci fa haramun ne kuma k'arya ne shirka ne Allah baya yafewa mushirki..... "ke Izza ki kiyayeni idan kika nemi d'agamin...
13.9K 1K 47
Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko sede mu zubawa sarautar Allah idanu zuwa...
2.3K 231 15
Saboda yadda mahaifin mu ya din ga saka Mana suna Fatima, har se da nayi tunanin ko Muna da alaka da shi'a ne, saboda Naga yawancin sune mutanen da k...