Page 17- Headmaster

174 28 0
                                    

Page 17

Na maimaita kalaman da na jiyo daga bakinta, don tun daga wannan ban kuma sake mayar da hankali in ji abin da suke fadi ba. Na dai samu bayanin da nake so, wato ko ma wace ce wannan matar, a nan gidan take, sannan tana da alaka da 'yan garkuwa da mutanen da ke kauyen, uwa-uba ma ita ke ba su bayani, irin wadanda ake kira da informers.

Da ma jikina ya ba ni tabbas akwai mai yi wa maigari zagon kasa, don daga yanayin kalamansa na jiya na fahimci akwai wata a kasa, akwai munafukin da ke jikinsa sosai wanda kuma shi ne yake isar da sakon gare su.

Jin alamun za ta tafi ya sanya ni gaggauta tafiya, ina rufe kofar dakin tana shigowa gidan, kiris ya hana ma da ta gan ni. Na gode wa Allah da ba ta gan ni din ba.
Na koma makwancina ina ta aikin sauke ajiyar zuciya. Ya zama dole gobe da sassafe in yi magana da daya daga cikin ma'aikatanmu, so samu ma Oga Ahmad. Na san idan na samu network duk sakunan da na tura masa ta whatsapp za su je masa. Don haka da safe abin da zan fara yi kenan, in je wurin dutsen nan tunda an ce kofar gidan maigarin ne ba ma da nisa ba.

Wannan dare dai haka na cinye shi babu bacci, kodayake da ma ba baccin na zo yi ba, aiki na zo yi wa kasata, don haka dole ne in jure, in cire komai in yi abin da ya dace.

Da sassafe sai ga koko da kosai wai inji maigari. Na karba da godiya don ba zan iya cewa a bar shi ba, kuma ba zan ci ba tunda haka dokar aikinmu ta tanadar mana. Ba a jima ba kuma sai ga Amarya ita ma da nata kwanon na dumamen tuwo. Sai ga sauran matan maigari biyun kowacce da nata langar kuma abinci ne a ciki. Na ji dadi kwarai saboda yadda suka karrama ni, da ma an ce mutumin kauye akwai karamci.

Jakata ta goyo na bude na ciro cake din leda da lemu, ban bari kowa ya gani ba saboda yaran ma duk ba su nan, Amarya kuma ta fita can wurin kishiyoyinta. Na ci cake dina da lemo na koshi sannan na tattara wadancan kwanukan sai da daya daga cikin yaran Amarya ta shigo na ba ta na ce ta fitar na koshi.

Towel dina na wanka na daura tare da zuba doguwar hijabi na dauki kayan wankana. Ina fitowa Amarya da azamarta ta je ta zuba min ruwan wanka don da ma ta riga ta dora. Har bandakin ta je ta dan wawwanke shi sama-sama sannan ta ce in shiga. Sosai na ji matar ta shiga raina, tana da matukar kirki da karamci, ya ita ya mijinta.
Sai dai har ita din ban yarda da ita ba, aikinmu babu yarda a cikinsa ko kadan.
Na yi mata godiya sannan na je na yi wankan.

Bayan na shirya na sanya kayana na NYSC, na dan yafa farin mayafi sannan na fito na yi musu sallama cewa zan tafi makarantar da aka tura ni.

"Kin san makarantar ne ko in sa Farida ta raka ki?"
Amarya ta tambaye ni tana goge hannunta bayan ta ciro shi daga bokitin da take wanki.
"A'a gaskiya ban sani ba sai an raka ni. Amma kafin nan zan tsaya a gaban dutsen can in yi waya da 'yan gidanmu sannan in wuce."
"To shi kenan. Kafin ki gama za ta jira ki kofar gida."
Na yi mata godiya sannan na fice.

Cikin sa'a kuwa ina isa na kunna DATA sai ga sakuna sun fara shigowa, na yi hamdala don ba karamin dadi na ji ba.
Na latsa kiran Oga Ahmad, bayan ya dauka na gaishe shi cikin girmamawa ya ce
"Ina cikin ganin sakunanki da ke shigowa kenan kika kira ni."
Na amsa da
"To bari in jira har ka duba Yallabai. Don kauyen ne babu service sai an je wurin wani dutse. Kuma yanzu haka na fito ne zan tafi makaranta."
"Haka ne, na sani ai. Ko kin manta duk sai da muka binciko komai kafin ki je?"
Murmushi kawai na yi, kit ya kashe kiran.
Daga nan na kira Umma muka gaisa, ta sake yi min fatan alkhairi sannan na kira Mama, ita ma addu'a ta yi min sosai muka yi sallama.
Sai na kara samun wani irin kwarin guiwa. To wanda ke tare da addu'ar iyaye me zai bata masa rai har ya tsorata?
Na saki murmushin jin dadi. Sai kuma na tuno da Anti Maryam, na latsa kiran ta ita ma.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now