Page 30- Visiting

162 23 0
                                    

Page 30

Ina jin Umma ta kira Kawu Danladi ta sanar da shi na samu mai neman aurena kuma yana son ganawa da su, ya ba shi lokaci sannan suka yi sallama ta yanke kiran.

"In ban da addini da al'ada da suka farlanta neman aure a wurin maza kuma makusantan mutum, sannan dangin uba, wallahi da babu dalilin da zai sanya ni komawa ta kan dangin mahaifin nan naku Khairi. Ni ban taba ganin mutane marassa kirkinsu ba, wadanda ba su damu da diyan dan'uwansu ba. Tun da mahaifinku ya bar duniyar nan ko turmin atamfa babu wanda ya taba dauka ya kawo min da nufin in dinka muku, ko kuma wani taimakon daban. Duk da irin kokarin da ya yi da su a lokacin da yake raye.
Har gara matan ma, tunda sukan wanko kafa su zo su duba lafiyarku. Haka lokacin da aka sace ku din nan, da kukana da komai na je neman taimako amma babu kwandalarsu da suka dauka suka ba ni. Shi Alhaji Sambo ma kai tsaye ya ce ba zai bayar da kudinsa ga 'yan fansa ba, haka na baro gidan nashi cike da kunar rai da kuncin zuciya. Shi ya sa ma ko da za a je neman auren Safra ban nufi kiran sa ba sai na kira Danladi tunda ya fi shi kirki duk da shi din ma dai sai a hankali. Amma ko ba komai an tarbe su da mutunci, duk da babu ruwa ko lemo amma shimfidar fuska ai ta fi ta tabarma.
Da alama iyayen Aliyun masu dattako ne in dai yadda yake haka su ma suke, to gara wurin Danladin za su fi samun tarbar mutunci a kan shi wancan mai kudin da ba su da amfani sai gare shi da iyalinsa. Ramin kura ne daga shi sai 'ya'yansa."

Na yi shiru ina sauraren ta har ta kai aya.
Jin na yi shiru ya sanya ta kallo na sai ni ma din na kalle ta, ta gyada kai hade da guntun tsaki.
"Mutum ya yi ta yi miki magana eh ko a'a ma ta gagara. Ni kam na rasa wace irin mutum ce ke."

Murmushi na yi na ce
"Allah Ya ja da ran Hajiya Ummana."
Na fada jikinta.
"Ni daga ni kar ki karya ni ki yi wa autata asara."
Bata fuska na yi ina gunguni,
"Auta ce kadai mutum ai ko."
"Eh mana, daga ke har Safran nan da watanni kadan za ku tafi ku bar ni. Ni da autar dai za mu ci gaba da rayuwa kafin mai jirgin sama ya zo neman aurenta."
Ta karasa tana dariya. Ni ma dariyar na yi ina tuna wasu lokutta can a baya, lokacin da muke zama mu yi nishadi har da Ummu, su hade min kai ita da Umma suna tsokana ni kuma Mama ke shigar min idan tana nan.

"Tashi ki kira min Aliyu in fada masa yadda muka yi da Danladi. Kira shi maza ki hada mu."
Ban musa mata ba na mike na dauko wayata daki na latsa kisan sa.
Ko gaishe shi ban yi ba na fada masa Umma ce ke son magana da shi sannan na kai mata wayar na komawa ta daki. Ban san yadda suka yi ba dai sai wayata da ta kira ni na karba.
Babu jimawa sai ga texts message dinsa ya shigo;
"You're soon to be Mrs Turaki."

Gajeren murmushi na yi ina maimaita karantawa, wato dai Umma ta tabbatar masa da za a ba shi ni shi ya sa ya yi min wannan maganar.

Gani na yi ya kamata in je gidan Anti Maryam, amana ba ta ce haka ba. Yadda matar nan ta yi min halacci ba tare da ko sisinmu ba, bai kamata in yar da ita ba. Don haka na koma waje na sanar da Umma ina son zuwa gidan Anti Maryam ta ce ba damuwa. Sai Safra ta raka ni tunda ita Sadiya tana makarantar islamiyya.

A can muka wuni sai daf da maghriba muka dawo. Ana yin maghribar kuwa Haidar ya kira ni ga shi nan zuwa. Da ma ban sauya kaya ba sai kawai na zauna jiran zuwan sa.
Ba a jima ba ya iso, na ce masa ya shigo ciki. Umma na parlor suka gaisa ta kara jaddada masa zancen Kawu Danladi ya amsa cikin nutsuwa sannan ta ba shi wuri tare da sanya Sadiya ta kira ni duk da ina jin su daga cikin daki.
Bayan na fito na gaishe shi amma bai amsa ba sai wani irin mayen kallo da yake bi na da shi da wadannan mayatattin idanuwan nashi da kullum suke tamkar mai jin bacci. Kunyar kallon na ji na sunkuyar da kai ina tambayar shi Mami.
Sai a sannan ne na samu amsa.
"Mami na asibiti an kwantar da ita, yanzu haka ma daga can nake, na fada mata wurinki zan zo ta ce in gaishe ki kwarai."

DARE DUBUWhere stories live. Discover now