Page 54- Shaidar Zur

147 26 1
                                    

Page 54

Cike da farinciki muka fito daga kotun, fuskata a kan mijina ta sauka, na kuwa gaggauta isa na shige cikin jikinsa ina sakin ajiyar zuciya.
"Congratulations Baby girl."
Ya furta cike da shaukin soyayya. Na dago fuskata na dube shi,
"Tun ma kafin a gama shari'ar?"
Na tambaya ina murmushi.
"Ai wannan zaman ya gama fayyace komai. Da izinin Allah next zama za a yanke musu hukuncinsu."

Kama hanya muka yi tare da nufar bakin mota, ko sallama da Barrista Fa'iz ban yi ba can na hange shi da su Safare suna magana.
Haidar ya tada motar muka tafi.
Hannuna a cikin nashi na ce,
"Ka san ita shari'a ana zaton wuta ne a makera amma sai a gan ta masaka."
"Duk da hakan dai muna kyautata zato."
"Haka ne. Amma sai mu ci gaba da addu'a, don Barrista Rafiq mugu ne, zai iya juya komai kafin nan da kwana biyar din nan."
Hannuna ya sumbata, ya ce,
"Be positive baby girl. Za mu yi nasara da izinin Allah."

Da wannan tattaunawar muka isa gida don na ce ba zan koma wurin aiki ba saboda zazzabin da ke jikina. Da farko asibiti ya ce mu je amma na ce ya bari ko zuwa yamma ne idan mun huta sai mu je. Daga nan ma mu fita da su Afreen ko ice cream ne su sha.

***
Bayan sallar la'asar, a lokacin har Kuluwa ta gama shirya Ummu da Afreen cikin kananan kaya riga da wando sai hula mai butterfly. Ni ma riga da wandon ne amma sai na dora original jilbaab a kai. Ko da na fito Haidar sai aikin doki yake yi wa yaran. Na yi tsaye ina kallon su da mamaki, idan wannan ta hau sai waccan ta ce ai ita ce a layi. Shi kuwa ya biye musu sai rabon rigimar tasu yake yi.
Gyaran murya na yi duk suka juyo suka kalle ni.
"Yawwa Mummy gara da kika fito. Kin ga Daddy nan sai yi wa Afreen yake yi ni kuma sau biyu kawai ya yi min ko?"
Ta karasa kamar za ta yi kuka. Kafin in ce komai ita ma Afreen din sai cewa ta yi,
"Mummy, tun dazu Daddy yake yi wa Yaya, ni sau goma da biyu kawai ya yi min."

Dariya muka sa ni da Haidar, na ma rasa abin da zan ce da wannan rigima tasu. Sai kawai na bude musu hannuwana biyu duka suka shige.
Na yi kissing goshin kowacce sannan na mike na ce,
"Duk ku rabu da Daddy. Idan mun sayi ice cream dinmu ba za mu ba shi ba."
Sai kawai Ummu ta kyalkyace da dariya, ta ce,
"Mummy ai shi ne zai saya mana ko. Idan muka hana shi next time ba zai sake saya mana ba."
Ai kuwa Haidar ya kama tafi yana min dariya.
"Yara ma kansu sun san gaskiya. Ai ba a hana ma-ba-da rago fata ko my happiness?"
Ta dan bata fuska, sai kuma ta ce,
"Rago za ka saya mana Daddy? Ye ye ye...Daddy zai saya mana rago..."
Ta kama tsalle tana kwala kiran Kuluwa wai ta zo ta ji Daddy zai saya musu rago.
"Wannan 'yar taka Daddy, 'yar farin ce ta gaske."
Na gyada kai ina dariya.

Daukar ta ya yi suka yi gaba suna dariya, ni kuma na kama hannun Afreen saboda ba zan iya daukarta ba jikina babu karfi don zazzabin da gaske so yake ya kwantar da ni.

Daga gida kai tsaye asibiti muka fara nufa. Gwajin jini da fitsari aka fara yi min, aka ce bayan minti talatin result din zai fito, don haka sai Haidar ya ce mu yi saving time kawai mu fara kai su Ice Hub shan ice cream din kafin mu gama da can result ya fito.

Da muka je kowacce ita ta zabi flavor din da take so sannan aka bi da topping, ni ma na zabi nawa, Haidar kuma da ma ice cream bai dame shi ba. Bayan ya je ya biya kudin muka wuce ya saya mana family size na pizza.
Daga nan a maimakon mu koma asibiti, sai na ga ya dauki wata hanyar daban, sai ga mu a wani katon wuri zagayayye, mai cike da dabbobi. Kallon shi na yi cike da mamaki, kafin in ce,
"Kar dai..."
Ya yi saurin karasa min,
"Ba kina yi wa 'yata dariya ba? Rago zan saya mana. Da ma naman gidan ya kusa karewa ai."
Ya kuwa kama hannunta suka fice suka bar ni sake da baki ina al'ajabi.

Sun dan jima kafin su dawo. Ya ce ya biya kudin, har gida za su kai mana ragon don da ma a nan yake sayen na sallah, ya san su sosai.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now