Page 39- Kukan Zuci

156 22 0
                                    

Page 39

Bayan isha'i kowa ya watse aka bar ni da su Safra kawai. Sai da suka gyara gidan tas, suka kara turaren wutar Dukhan by Ayn, mai matukar kamshi, daya daga cikin wadanda Anti Maryam ta saya min tun daga garin Abuja, tare da khumra da body milk mai zama a jiki (+234 808 892 9221). Sai ga su sun zo wai za su tafi. Ban san sadda na sakar wa Safra harara ba ina karawa da jan dogon tsaki.
"Ba ku ma da hankali tunda har kuke tunanin tafiya ku bar ni ni kadai a katon gidan nan."
"To Yaya Khairi ai dai kin san ba zama za mu yi mu kwana ba ko? Kuma dare ke yi, dole mu tafi tun kafin mu rasa abun hawa."

Allah Sarki Ummu. Da tana raye na tabbata ba za ta yi tunanin tafiya ta bar ni ba ko don halin kadaicin da zan shiga. Na hau share hawayen da guminsu kawai na ji ban san sadda suka fara saukowa ba.
Ganin ina kuka kuma sai ya rikita su. Sadiya ta hau share min hawayen tana ba ni hakuri.
"Idan muka zauna Yaya babu wanda zai mayar da mu, kuma kin ga unguwar nan akwai nisa da cikin gari, samun abun hawa ba abu ne mai sauki ba."

Na gamsu da hujjarta. Don haka sai na jinjina musu kai tare da mikewa na taka musu har bakin gate. A lokacin ne na kare wa gidan kallo. Kato ne sosai da wurin faka motocin da zai iya kwasar akalla mota bakwai. Sai shuke-shuken da suka kara kawata gidan.

Ko da na koma ciki ma sai da na tsaya duba ko'ina na gidan. Komai cas, kuma daidai da ra'ayina. Sai na ji wata irin soyayyar Haidar tana kara kwaranya a cikin zuciyata. Tabbas ya yi kokari fiye ma da yadda na yi tunani.

Wanka na shiga daga nan na yi alwalla. Da na fito wata doguwar riga na saka jikinta mai taushi da zanen flowers daga gaba. Hannunta gajere ne ko guiwa bai kai ba. Na dauki hular shantili na dora a kaina da ya sha wani irin gyara yana fitar da walkiyar mayuka. Sannan na zira dogon hijabi na gabatar da sallar isha'i da ke bisa kaina.
Da na gama ma ban tashi daga bisa carpet din ba sai na ci gaba da tunanin rayuwa; hakika komai yakan zo wa bawa ne ba a yadda ya taba zato ba. Tun daga ranar da na budi ido na tabbatar da an haike min, na cire mafarkin cikar duk wasu burika nawa, daga ciki kuwa har da samun ingantaccen miji. A gani na duk wata macen da aka yi wa fyade ba za ta taba samun ingantacciyar rayuwa ba, miji nagari kuwa sai dai ta gani a wurin wasu. Ashe duk ba haka ba ne, ashe akwai nagarin da ke dabaibaye rayuwarmu, su kalailaye zukatanmu.
A yau ga ni a gidan Aliyu Haidar, irin mazan da kowacce mace ke mafarkin samu, wanda yake kaunata da dukkanin zuciyarsa.
Na saki sassanyan murmushi ina kara godiya ga Allah da Ya gwada min wannan rana.

Kamar an ce in dago kaina sai na ga mutum tsaye a kaina yana sakin murmushi. Na sunkunyar da kaina kasa, cike da mamakin yaushe ya zo? Don har ga Allah ko karar bude kofa ban ji ba, kuma alamu sun nuna ya dan jima a tsaye. Kokarin mikewa na ke ya dakatar da ni.
"Jira ni in yi alwalla sai mu yi nafila."

Ban musa masa ba, na koma na zauna ina sakin ajiyar zuciya. Bai wani jima ba ya fito yana gyara hannun rigarsa da ya nannade saboda alwalla.
Jan mu sallar ya yi, bayan mun gama ya yi mana addu'a sosai ina amsawa da amin, kafin ya matso inda nake, ya dafa goshina hade da yi min addu'ar da ake yi idan an mallaki sabon abu.

"Taso mu je ki ci abinci. Don na tabbata kina jin yunwa."
Tabbas kuwa ina jin ta din. Na mike jiki ba kuzari na bi bayansa. Har mun isa bakin kofa ya juyo ya ce
"Ba za ki cire hijabin nan ki huta ba?"
"Ai ba ta takura min ba."
Na ba shi amsa a hankali. Murmushi kawai ya yi sannan ya dage kafada muka fita.

A tsakiyar parlor manyan ledoji ne, shi da kansa ya je ya dauko plate da cups biyu. Gasasshiyar kaza ce gashin Hausa, wadanda duk ke garin Katsina sun san mansho suya, to kazarsu ce, asalin ta Hausa mai dadi. Ina ci ina lumshe ido.
Ya zuba mana fresh orange juice a cup.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now