Page 24- Bankwana

165 29 0
                                    

Page 24

Da na koma gidan ban shiga daki ba sai na nufi dakin Azumi, na same ta zaune ta rafka tagumi ita kadai da alama ba ta cikin kwanciyar hankali. Na ji dadi babu kowa a dakin, ina shiga ta daga kanta ta dube ni, ta firgita da gani na amma sai na sakan mata murmushi.

"Kar ki tsorata fa, tunda kin kiyaye kin bi doka to za ki zauna lafiya. Zuwa na yi in tambaye ki har yanzu ba su neme ki ba?"

Ta sauke nannauyar ajiyar zuciyar da har sai da na gane, ta amsa da
"Sun neme ni, na ji karar kiran su amma ban je ba, wallahi ban fita ba."
"A yaushe kenan?"
Na tambaye ta a hankali ta yadda babu wanda ke waje da zai iya jin mu.
"Jiya da tsakar dare, da suka ji shiru sun sake yin karar, har dai suka gaji na daina jin su."
"Good for you. Ina fatan za ki ci gaba da kiyayewa kamar yadda kika fara a yanzu."
Daga haka na mike na bar dakin ina jin zuciyata sakayau.

Ko da na koma ban aikata komai ba sai latsar waya, ina ji a raina this is the right time, na gama aikina, a yanzu ne ya kamata komai ya zo karshe, komai din da ke nufin har da shigar ma'aikatanmu daji domin far wa wadannan mugayen mutanen.

Sai kuma na dinga tunanin, to idan fa wadannan mutanen ba su ba ne ainahin wadanda suka kama mu? Idan ya kasance ba su ba ne suka kashe Ummu sai yaya kenan?
Kit! Na hadiyi kakkauran yawu; irin mai wahalar hadewa. 'Be positive Khairi.' Na tsinto wata murya can daga nesan zuciyata. Tabbas tsakanin dazukan nan ne aka sace mu, kuma an ce duk kidnappers guda ne suke aikata aika-aikar bangaren. So, ina kyautata zaton su din ne, su ne dai fulanin nan da ke addabar mutanen wannan yankin, har ma da na wani bangaren. Su ne wadanda ke zuwa har kofar gidan mutum su yi sama da shi, kamar dai yadda suka yi mana. Su ne kuma masu tare motocin mutane da rana tsaka su shige daji da su. Babu tantama su ne aka ce suna shiga cikin garuruwan Meshe da su Sassanya da rana su sha mai a baburansu babu ko shakkun za a iya kama su. Su ne jahilan nan, 'yan shaye-shaye, sannan masu keta wa mata haddinsu idan ba su samu kudin fansarsu ba...
Ban kara tunanin komai ba daga nan face zuciyata da ta dauke ni daf, ta kai ni can wani lokaci da ya wuce, lokacin da aka keta haddina ina ji ina gani...

TUNA BAYA

A daidai lokacin da muka cika wata hudu a hannun 'yan garkuwa da mutane, kai tsaye suka nuna sun gajiya da mu, sun gaji da rikonmu kuma alhali babu wani fata, tunda har a lokacin babu kudin fansa babu dalilinsu. Duk sadda suka yi waya da iyayenmu sai su ce har a lokacin ana hada kan kudaden ne. Tun muna jin wani labari daga gare su har muka daina, Ogan Kidnappers din ya daina neman mu idan zai yi waya da su, har dai wata ranar Asabar da ya sanya aka kira mu zuwa mazaunarsa.
Ko da muka je, lambar Baba ya kira a gabanmu, kafin ya dauka ya umurce mu da mu fasa kuka da karfi, idan ba haka ba zai yi mana dukan da za mu yi kukan na gaskiya.
A daidai wannan lokacin tuni hawayen namu ma sun yi nisa da zukatanmu, mun hakura, mun jingine duk wata damuwa tare da mika wa Allah dukkan komai.
Ihun da muka fasa din ma na karya ne, domin daga ni har Ummu babu mai ko dison hawaye sai dai karar kukan kawai.

Ko da Baba ya dauka, Oga Rabe, kamar yadda na ji suna kiran sa da shi, ya ce
"Gobe ne rana ta karshe, mun yi hakurin, mun daga muku kafa, sannan mun yi muku ragin kudi duka a banza! Me ya sa kuke neman kai ni karshe? To bari ka ji in fada maka; wallahi tallahi idan kuka wuce gobe ba ku kawo kudin fansarsu ba, duk abin da ya faru ku kuka ja! Zan ba su Zaki izinin su aiwatar da duk abin da ransu ya ba su game da su."

Cikin in'ina da tsoro Baba ya ce
"Ku yi hakuri...don Allah ku yi hakuri ku kara mana lokaci. Mun samu da kyar mun hada dubu dari takwas, na wurin Ummu kenan. Ita kuma Khairi, tsaye Mahaifiyarta take domin ganin ta hada amma wallahi abun ya gagara, babu, mahaifinta ya jima da rasuwa, a dangi an rasa mai taimaka mata. Ka taimaka ku kara mana lokaci."
"Taimako? Ka taba ganin inda mugu ya yi taimako? Ko ba mugaye kuke kiranmu ba? To ku fada ku kara, mu din mugaye ne, ba mu da imani, ku yi kokari ku wuce gobe ba ku kawo kudin nan ba ku ga zallar rashin imanin namu."
Daga haka ya yanke wayar, da alama ba za su daga mana kafa ba daga goben nan, saboda yadda na tsinci seriousness a cikin muryarsa.

DARE DUBUWhere stories live. Discover now