Page 35- Award Morning

149 24 0
                                    

Page 35

Jin na yi shiru ya sanya shi ci gaba da fadin
"Ki yi kokari ki yi wa Umma bayanin yadda za ta fahimta, kin ji Buttercup?"

Ta ina ma zan iya tinkarar Umma da wannan maganar? Ai kunya ma ba za ta taba bari na iya ba.
"Baby boy ko za ka kira Safra ka fada mata? Wallahi ni dai kunya nake ji."

Ya yi murmushi.
"Sarkin kunya. Da in kira Safra da wannan in samu Umman da kaina mana."
"Haka dai ya kamata."
Na ba shi amsa a hankali.
"Shi kenan. Zuwa jibi zan zo sai in mata bayani. Gobe dai hidimarki ba za ta ba ni dama ba."
Cikin annuri na ce
"A can wurin taron za a kwana ne?"
Cikin rashin fahimta ya ce,
"What?"
"Na ji ka ce hidimata ba za ta bayar da dama ba. Kuma na san duka program din one or two hours ne."

Ya yi dariya sosai. Ya ce
"Kin gan ki. Ba wannan nake nufi ba. Hidimar gyare-gyare da 'yan tsare-tsaren gidanki nake nufi. Ni ba ma zan je wurin bayar da award din ba fa."

Na kuwa bata fuska, cike da shagwaba da bacin rai na ce
"Okay. Shi kenan kar ka zo din."

Na yanke wayar ina jin takaicinsa. Shi ya kirkiri ba ni award din tun farko, sannan kuma sai ya ce ba zai samu halarta ba a matsayinsa na mafi kusanci da ni a yanzu?
Ina kallon wayar na ringing har ta tsinke na ki dauka. Sai da ya yi kira biyar a na shida na dauka. Na ki magana shi ma kuma bai ce komai ba, sai da muka cinye fiye da minti guda a hakan kafin ya ce
"Da ina kusa da ke da na yi maganin wannan rigimar taki honey pot."
Na yi masa shiru ya ci gaba da magana.
"Ba za ki kula ni ba? Allah za ki iya gani na anjima in dai ba ki yi min magana ba."

Na kuwa yi gaggawar fadin
"To dan Allah kawai sai ka ce wai ba za ka zo wurin ba ni award ba. Idan har ba za ka je ba ni ma ba za ni ba. Sai mu ga wanda za a ba."
"Calm down Cupcake. Wasa fa kawai nake miki. Ai ko babu komai a tsakaninmu kokarin da kika yi dole zai sanya ni zuwa wurin ba ki award. Ballantana kuma Khairin ta Haidar ce."
Na saki sassanyan murmushi.
"Na ji wannan dadin bakin. Tsabar ana son tsara ni kuma yau cupcake na koma?"
"Ai ke fa komai ce, idan na ce komai, ina nufin komai nawa. You are my World. So zan iya kiran ki da duk abin da yake cikin duniyata."

Na lumshe idanuwa ina jin dadin kalaman nashi, soyayyarsa na dad'a ninkuwa a cikin zuciyata.

"You know what? I love you so much, I love you with all I have got."
Na sake lumshe idanuwana ina imagining yadda nashi lumsassun suke a yanzu.
"And I have a big suprise for you amma ba yau zan fada miki ba, may be sai abin da nake planning din ya gama tabbata."
"Thank you."
Kawai na iya furtawa ina jin yadda zuciyata ke wani irin narkewa da dad'ad'an kalaman nashi da ke ratsawa tun daga cikin kunnuwana suna isa duk wata gaba da ke cikin jikina.

***
Washegari karfe takwas na shirya cikin khakina na dora kimono kalar grey, sannan na yafa karamin mayafi na yi wa Umma sallama tare da jaddada musu sai sun iso zan jira su.

Ko da na fita yana zaune a mota yana jira na. Ban yi tsammanin ganin sa ba a yanzu, kai tsaye na doshi motar na bude na shiga da sallama.
"Good morning."
Na furta ina kallon sa.
"Morning wife. Ya kika tashi?"
"Alhamdulillah."
"Ya Umma da su Sister Halimatu?"
"Duk suna lafiya."
"Ma shaa Allah. Muna isa zan bayar da motar a zo a dauke su in shaa Allah."
Na jinjina kai kawai. Daga nan muka dauki hanyar zuwa wurin aiki.

Babban conference hall da yake cikin wurin aikin namu ya sha ado cikin galar green white green sannan da katon tambarin DSS daga sama.
Tun daga nesa Aysha ke sakar min murmushi har na karaso ta zo ta shiga jikina.
"Kawata taron nan duk naki ne."
Ta fada ko gaisawa ba ta bari mun yi ba.
"Namu ne mu duka Aysha. Nasarar dayanmu ai tamu ce duk ahalin DSS na jihar Katsina. Ko ba haka ba?"
"Haka ne mana."
"Yawwa dai. To ballantana kuma ke da kike tawa."

DARE DUBUWhere stories live. Discover now