INDON KAUYE

By asmaullahilhusna

2.5K 85 14

Wani numfashi yasaki mai ƙarfi agigice yajawota tafaɗo kanshi cikin karaji yace nashiga uku indo sa hannu kij... More

INDON KAUYE part 1
INDON KAUYE part 2
INDON KAUYE part 3
INDON KAUYE part 4
INDON KAUYE part 5
INDON KAUYE part 7
INDON KAUYE part 8
INDON KAUYE part 9
INDON KAUYE part 10
INDON KAUYE part 11
INDON KAUYE part 12
INDON KAUYE part 13
INDON KAUYE part 14
INDON KAUYE part 15
INDON KAUYE part 16
INDON KAUYE part 17
INDON KAUYE part 18
INDON KAUYE part 19

INDON KAUYE part 6

134 3 0
By asmaullahilhusna

🍃🍃🍃🍃🍃
    *_INDON ƘAUYE_*
           🍃🍃🍃🍃🍃

  (😂Funny and romantic story😂)


        *~ Na ~*

   🏵  *Asmieyn Sadeeq* 🏵
*HUSNA ABUBAKAR HUSSAINI* ✍

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

  ✨💧Tsokaci.... Wannan littafi na kudine Banyarda  wata takarantamin batareda hakkinaba.... Idan kuma hakan tafaru na yafe miki ke kikaci kadan💧✨

*PAID BOOK ₦200only*

Page 6️⃣

"Nidai asalin sunana AISHA sunan mahaifina ABUBAKAR mahaifiyata kuma MARYAM....shekaruna sha huɗu ,mahaifiyata da mahaifina sun rasu tun ina yar shekara huɗu a duniya , matan mahaifina biyu inna kande itace tafarko tanada yara guda biyu jummala da Abdullahi sannan  sai mahaifiyata  da ake kira da mairo itace ta biyu nikaɗai tahaifa kafin Allah ya amshi rayuwarsa,
Mahaifina ɗa ne ga AISHA da MUHAMMADU, Muhammadu wato kakana yakasance ɗan asalin garin Katsina, a ƙauyen suduji dake cikin Daura,haka kakata wato Aisha garinsu ɗaya da kakata sunada yara uku, babana wato Abubakar shine ɗansa na farko sannan sai gwaggo fatu sai autarsu Aisha ana cemata mami sabida sunanahaifiyarta akasaka mata domin agirin haihuwar tane kakarmu tarasu ,shine kaka yamaida sunanta sabida son dayake mata, to kaka dai bai sake aure ba har shima Allah ya amshi rayuwarsa ,kamar yadda na faɗa maka babana yarasu tun ina shekara sha huɗu, to Mami Kuma tayi aure Amma a birni saidai takanzo lokaci zuwa lokaci"
Tinda tafara magana ya ƙureta da idanu sosai yarinyar take birgesa....
Buɗe baki tayi daniyar magana saitaga ya ƙureta da idanu gashi a duniya indo tatsani kallo
"Wai ya da kallo...?"
Tafaɗa atsiwace
Ɗan yaƙe yamata tareda sosa ƙeyarsa
"Unmmm gani nayi kamar baki gajiya da magana"
Da kallon kama rainamin wayo tabishi
Kafin takaiga yin magana yayi saurin faɗin
"Kinga yahaƙuri tashi mutafi gida Kinga za a iya naiman mu",
Batareda tamasa musuba tamiƙe hartakama hanya saita tuna ae babu kaya ajikinta sai ɗaurin ƙirji.
Saddam da dama yaci burki yanaso yaga iya gudun ruwan haukar yarinyar ganin tajuyo kuma tanufi gurin kayan saiya kwashe da dariya
"Toh waida ke ahaka zaki tafi"
Batareda ta kulasaba tayi gaba abinta bayan ta zura kayan .
Koda suka isa gida basu samu kowa a tsakar gidanba sai Nu'aim wanda shima da alama fita zaiyi
Saddam na shigowa yafara aeka masa da wata uwar hada kai kace mace ne shi
Sinne kai kawai Saddam yayi yana ƙunshi dariya dan ko bai faɗa masana yarigada yasan laifinsa .
Da ƴan waƙe waƙenta ta ƙarisa shigowa hannunta riƙe da ƴar sanda ganinsu a tsaye yasa taci burki ,
Ko kallon inda take baiyiba yayi hanyar fita, saurin matsa masa tayi taƙame a bango ,hakan kuwa ba ƙaramin ɓatawa Nu'aim rai yayiba
"Wato yarinyar nan ma Ni take gudun haɗa jiki dani ko...?"
Yaɗa aransa ƙwafa kawai yayi yabawa rigarsa yayi waje
Indo kuwa naganin fitarsa tasauke ajiyar zuciya aranta tana mai tsine masa
Muryar inna tajiyo abayanta
"Ina kindawo ...? Toh maza kihaɗa murhu sannan kizo kisiyomin wake inɗora sanwar dazaki kaimin talla dandali zuwa anjima"
" Inna Wai ni zan fara talla...?"
"Na rantse indo kika tsaya min gaddama sainamiki ɗan banza duka sannan kuma dole kiyi talla dan ubanki tinda babu mai bani dan ci dake"
Jin za'ayi mata gorin da aka saba ne yasa taja ɗan ƙaramin bakinta ta tsuke cikin naiman zaman lfy tanufi inda ake haɗa hutar ta kama haɗawa
Saddam kuwa dake tsaye yana jin duk yadda sukayi kawai ya girgiza kansa yana mai ƙara gasgata zancen umman su , batareda yafurta komaiba ya kaɗa kai kawai yashige ɗakin da aka gyara domin saukarsu....
Tinda yashiga ɗakin babu abinda yake tunani sai rayuwar da ummansu tabasu labarin tayi ahannun inna kafin tayi aure, sosai yakejin tsanar inna kande sabida sam batada hali mai kyau tafiye son kanta dayawa ,amma dole yasan yanda zaiyi da indo bazai barta hakaba, gashi shikuma yanzu baida halin hanata wannan tallar da ake naiman fara ɗaura mata dama Nu'aim take shakka toh shi ga irin yanda Allah yayisa barinma yadda yaga yana nuna tsanar indon a fili yasan ko zaiyi bunga wallahi bazai taɓa sa baki a al'amarin yarinyarba ....
Nu'aim kuwa yana barin gidan kai tsaye cikin motarsa ya shiga bai tsaya ko ina ba sai asalin birnin jihar  garin Katsina domin Allah ya sani baijin zai iya zama batareda ya ɗan taɓa wani ɓoyayyen hali nasaba

********

Sosai wutar taba indo wahala kafin takama ,saida tafaki idon inna tahuta kafin ta iskota aɗaki
Ranta baiso hakanan babu ƴanda ta iya tace
"Inna na gama "
Batareda innar takalli inda takeba tajeho mata kuɗin
"Gashi kije ƴar kasuwa kisiyomin shinkafa mudu biyu da wake rabin loka, saura idan kinje karki dawo sai gobe"
Zunɓura baki tayi ranta baisoba hakanan ta ɗauki kuɗin takama hanyar zuwa aeken inna babu yanda ta iya.....
Koda tafuta saida tabiyawa ƙawarta hinde akan tarakata...
Babu musu dake dama zaanice ta tadda mujemu haka suka kama hanya ana tafe ana tsokanar da aka saba tana ƴanko wata kwana sukaci karo da yaron maƙwabciyarsu nan indo taci burki jikinta har tsuma yake...
Ganin haka sai hinde taja baya gudun kar ahaɗa da ita domin kuwa idan bata manta ba ranar suna cikin tafiya da indo idi ya ringa tsokanar indo, taso kamasa ranar amma yagudu ...maganar indo ce tadawo da ita daga duniyar tunanin daya lulaƙa
Da sanɗa indo taƙarasa inda idi ke tsaye ya juya baya carap ta cafki kwalarsa
"Wana kama? Nace wanda kama?"
Tafaɗa tana jijjiga jiki
Idi da gaba ɗaya banda rawa babu abinda jikinsa keyi yashiga faɗin
"Indo na roƙeki da girman Allah kiyahaƙuri bani sakewa"
Ae ko sauraran ƙarshen inda zancen sa ya dosa indo batayiba ji kake ɗim ta tuna idi da ƙasa agurin indo tama idi ligiligi daƙyar hinde ta janye indo akan ruwan cikin idi ganin zatayi kisa
Ae nan indo tace dawa Allah ya haɗata ba hinde ba , bala'i tashiga surfa mata akan dan mai zata raba faɗan dama shi yasan baida ƙarfi mai nashi na naiman tsokana....daƙyar hinde tasamu ta shawo kan mutuniyar harta haƙura suka cigaba da tafiya don zuwa aeken inna....
Da kyar idi yaɗauki fatanyar ƙafarshi yayi gida yana gunjin kuka , yana isa yataradda mahaifiyarshi gindin murhu
Tana yin tozali da fuskar ɗanta da indo rayuwa kacakaca duk ta kumbura cikin tashin hankali maman tashiga faɗin ..
"Na higa uku Ni  haire ,yanzu idi ina kaje haka har amalanke tayi sama dakai ...?"
Cikin Muryar kuka yafaɗawa mamanshi ae indo ce tamasa duka
"Kutumar ubancan , wato iskancin indo yau takanka ya hauro kenan ..? Toh wallahi bazan yardaba ,yau ɗinnan basai gobeba zan ɗau mataki akan wannan azababbar yarinyar ,ace tafi ƙarfin kowa a ƙauyennan saidai tayi abinda taga dama toh wallahi Ni bazan ɗaukaba tashi muje gidan nasu yau za'ayita ta ƙare sainaga waya tsayawa indo a ƙauyennan da take taka kowa kuma ba'a iya ɗaukar mataki ,tashi mujeeeee"
Taƙarashe zancen nata cikin ɓacin rai dayake matar itama dama ƴar bala'i ce sai huci take kamar tahaɗiyi kunama
Nan ta hankaɗa ƙeyar idi sai gidan inna dake maƙwabtan junane bata wani bata lokaci ba ta isa gidan
Tun daga ƙofar gida tashiga zage zage ....arikice inna tafito jin kamar za'a rusa mata gida sabida bala'i zani ahannun har tana shirin faɗuwa ....
Da mamaki take bin haire maƙwabciyarsu da kallo ganin taci ɗanmara hannu a ƙugu kallo ɗaya zaka mata kafahimci jira kawai take ataɓata ta sace....
"Ina shegiyar yarinyar nan take ...?"
Da kallo kawai inna kebinta dan kobata faɗaba tariga da tasan wa take nufi , amma kuma ae idan bata mantava ae ta aeki indo tun ɗazu kuna har yanzu bata dawoba toh dawa take tinda wacce take zargin da ita ake ae batanan
Muryar haire ce tadawo da ita daga ɗan tunanin data shiga.
"Wabillahillazi bazan yardaba ko afutomin da indo in mata abinda yayiwa ɗana ko anbiyani kuɗin magani da kuma na jinya koh kuma na ɗagawa kowa dake ƙauyennan hankali"
Ganin abinnata na gaba kuma tasata aduhu yasa tace
"Wai nikuwa haire banfa fahimci inda zancenki yadosaba ko kyamin bayani dalla dalla "
Nan haire ta kwashe ƙarya da gaskiya rafaɗawa inna harda faɗin indo ta anshewa idi kuɗi
Salati inna ta doka sannan tabuga tagumi
"Nidai nashiga uku na lalace ,wannan wace iriyar rayuwace ace ɗan da ka haifa bai jawo maka maganaba sai ɗan kishiya toh wallahi bazai saɓuba , haire Ni bazance miki komaiba amma bari tadawo kya fanshe koma maikikeso ajikin matsiyaciyar yarinyar Ni babu abinda yashafeni "
Ae kuwa babu kunya haire tanaimi kujerar tsuguno tazauna wai anan jiran indo take
Saddam dayagama jin abinda ke wakana girgiza kai kurum yayi yafito daga ɗakin hannunsa riƙe da fadar ƴan ɗari Biyar biyar
Kai tsaye inda haire ke zaune yanufa ko magana bai mataba ya miƙa mata kuɗin hanunsa wanda na tabbata shi kansa baisan adadin abinda yaɗaukoba
Jiki na rawa tamiƙa hannu zata amsa sai yayi saurin janye hannunsa
Da fuskar tausayi tashiga kallonsa
Saida yagama ƙare mata kallo wanda kallo ɗaya yayi mata yafahimci haire irin matan nanne masu shegen son abin duniya
Gyaran murya yayi sannan yashiga faɗin
"Ehmmm naji duk abubuwan dakika faɗa tun shigowarki amma wai yanzu indo ita tayima wannan rusheshen ƙaton ƙauhen ɗan Ali duka kuma har kika iya wanko ƙafa ko kunya babu wani ke kinzo rama masa...? Yanzu da indon na gida nufinki kamata zakiyi kiduka ...? Hmmm wallahi dako kinyi kuskure na ƙarshe a rayuwarki "
Yana gama faɗin haka ya cilla mata kudin tareda faɗin
" Ga wannan babu yawa , kyayi jinya kikuma sayi magani amma kuma ko kallon banza ban lamuci ke da ɗanki wani yakuma yiwa indo ba balle harta kaiki ga ƙoƙarin yin abinda kika furta, inda kunne yaji Tom jiki ya tsira"
Ae jiki na rawa haire ta suri kuɗin dan ko fahimtar inda zancen Saddam yadosa batayi itadai yanza babban burinta ta ganta aɗakinta
Da "toh Insha Allahu ɗan samari babuma mai sake tada maganar " tabishi da kwata kwata batama cikin nutsuwarta...
Bai jira cewartaba yajuya domin barin wajen ...karaf suka haɗa idanu da inna da gaba ɗaya tafice a hayyacinta ganin maƙudan kuɗaɗen da akaba haire ,cikin rawar baki tashiga faɗin
"Yanzu ɗan sabida almubazzaranci shine zaka ɗibi wannan tulin dukiya kaba wannan mahaukaciyar matar sabida wannan shegiyar yarinyar...?"
Da kallon mamaki kawai Saddam yashiga Binta ganin shirmen da take faɗa  ,bai iya furta mata komaiba yabarsu nan yayi shigewarsa ɗaki....
Haire kuwa tuni tafice agidan baki har kunne...
Sosai wannan abu ya baƙantawa inna rai kuma sosai taɗau alwashin fanshesa ajikin indo.....
Sai daf da magrib sannan indo tadawo daga aekrn da aka mata lokacin tuni inna tacika tayi fam,
Ko sallama babu indo tafaɗo gidan lokacin ruwan da inna taɗaura na sanwar shinkafa da waken ma har ta ƙone, 
Tana shiga ganin yanayin fuskar inna nan jikinta yayi sanyi amma dake mutuniyar waska ce kawai saita basar taƙarasa shiga
Gaban inna taje tamiƙa mata aekar
"Inna gashi"
Da wani mugun kallo inna tabita batareda ta iya furta komaiba sabida takaici daƙyar ta iya furta
"Sai yanzu kikaga damar dawowa...?"
Da kallon mamaki indo tabita jin zancen da innar keyi
Ganin kallon da innar taga indon namatane yasa ta daka mata tsawa
"Ba dake nake ba ...? Nace sai yanzu kikaga damar dawowa...?"
"Inna bake kikace idan naga dama karna dawo yanzu"
Cikin takaicin halin indo inna takaiwa bakin indo bugu
Ihu tabuga jin wani bahagon yafi ya lulluɓe ta
Bata gama dawowa hayyacinta ba inna ta haye ruwan cikinta taringa bugu kamar tasamu sa'anta ana cikin haka Nu'aim yadawo
Sallamar dafarone tamaƙale a ƙasar makoshinsa ganin irin jahilin bugun da inna kewa indo
Batareda yafurta komaiba ko yanuna alamun yadamu yasakai yashige ɗakinsu...

Tun indo na iya ihu har ƙarfinta ya ƙare saida inna ta tabbatar bazata iya tashi ba sannan taƙyaleta...
Annan tabarta tayi gurin murhu
"Kinji na rantse kuma tallar da kikemin baƙinciki saikinyita kimin dare"
Indo bajinta Amma bata iya furta komaiba amma aranta taɗau alwashin wallahi saita ɗau fansa
Kamar gaske ta rarrafa tayi ɗakin dake amatsayin nata domin kuwa ɗakin inna dana jummala ɗaya itakuma indo sai aka ware mata wani ɗan ɗaki wanda idan ba an faɗa makaba zaka rantse ɗankin tumaki ne .... Allah Sarki anan baiwar Allahn ke rayuwa ko ajikinta dake mutuniyar abin duniya bawai yadamaita bane....
Tana shiga ɗakin akan wata lamushashiyar katifarta takwanta tana maida numfashi domin agaskiya ba ƙarya ta bugu....
Aɓangaren inna kuwa sosai tazage tana girkinta saida tahaɗa komai tarufe tukunyar da langa baiwani jimaba dake wutar takama sosai yasa baiwani ɓata lokaciba ya nuna , robobin data saya domin zuba abincin siyarwar su taɗauko ta zuzzubawa kowanne dake abincin mai da yajine dandanan tagama haɗa komai ragiwar daya rage tajuye akwanan Samira saitarage kaɗan tazubawa indo,kwalla mata kira tayi .indo naji tayi mata banza can dai kamar karta amsa jin tasake kiranne yasa cikin ƙunƙuni ta amsa kiran badan ranta yasoba
"Gani"
"Dama cemiki nayi bangankiba...?"
Kawar da kanta gefe tayi batareda ta tankawa zancen nataba
Can saitakuma cewa
"Gashinan maza kiɗauka na ɗari huɗu da Talatin ne ,kuma narantse Miki da Allah indo bazan lamunci asarar ba"
Saitakuma tura mata wanda tazuba mata akwano awulaƙance tace
"Ga wannan maza kicinye kibani kwanan kafin anjima kifaɗama duniya bana baki abinci"
Da kallo indo tabi abinda wai take cewa abinci dan wallahi abincin haifi loma uku zuwa huɗu ba ,cikin takaici tasuri kwanan badan ranta yasoba saidan babu yanda zatayi
Inna kuwa kwashe abincinta tayi ta adana acewarta bazata ciyar da ƙarti ba wato su Nu'aim kenan
Wohohooo inna tamanta su basu iya cin garaugarau ba😂

Jin cikinta ya kurɗa yasa tayi haramar ɗaukar buta domin kewayawa

Saɗap saɗap naga indo tafito daga maɓoyarta da kallo nabita domin ganin mizatayi ,ganin tanufi inda inna ta ɓoye abincintane yasa nayi saurin Binta
Da kallo kawai indo Kebin abincin ganin uban abincin daya rage amma aka bata ɗan kaɗan murmushin mugunta tasaki cikin sauri taɗibi abincin yadda baza'a fahimci antaɓa ba sai naga gaciro wani abu agefen ganinta buɗewa tayi saida takwashe da dariya jin zata tonawa kanta asiri yasa tayi saurin toshe bakin cikin ƙanƙanin lokaci tayi abinda zatayi tabar gurin jin ƙarar ruwa da alamu innar takusa fitowa.....

Ɗaukar tallar tayi da wanda aka zuba mata duk tahaɗa aɗari tabar gidan .....

Continue Reading

You'll Also Like

681K 26.5K 74
Lilly found an egg on a hiking trip. Nothing abnormal on that, right? Except the egg was four times bigger than supposedly the biggest egg in the wor...
619K 32.9K 50
𝐒𝐜𝐞𝐧𝐭 𝐎𝐟 𝐋𝐨𝐯𝐞〢𝐁𝐲 𝐥𝐨𝐯𝐞 𝐭𝐡𝐞 𝐬𝐞𝐫𝐢𝐞𝐬 〈𝐛𝐨𝐨𝐤 1〉 𝑶𝒑𝒑𝒐𝒔𝒊𝒕𝒆𝒔 𝒂𝒓𝒆 𝒇𝒂𝒕𝒆𝒅 𝒕𝒐 𝒂𝒕𝒕𝒓𝒂𝒄𝒕 ☆|| 𝑺𝒕𝒆𝒍𝒍𝒂 𝑴�...
434K 41.5K 32
She is shy He is outspoken She is clumsy He is graceful She is innocent He is cunning She is broken He is perfect or is he? . . . . . . . . JI...
1.9M 141K 63
"ရှင်သန်ခြင်းနဲ့သေဆုံးခြင်းကြား အလွှာပါးပါးလေးကိုဖြတ်ကျော်ခါနီးမှာမှ ငါမောင့်ကိုစွန့်လွှတ်တတ်ဖို့ သင်ယူနိုင်ခဲ့တယ်၊ လူတွေက သံသရာမှာ ရေစက်ရယ်၊ဝဋ်ကြွေး...