INDON KAUYE part 9

103 2 0
                                    

🍃🍃🍃🍃🍃
    *_INDON ƘAUYE_*
           🍃🍃🍃🍃🍃

  (😂Funny and romantic story😂)


        *~ Na ~*

   🏵  *Asmieyn Sadeeq* 🏵
*HUSNA ABUBAKAR HUSSAINI* ✍

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

  ✨💧Tsokaci.... Wannan littafi na kudine Banyarda  wata takarantamin batareda hakkinaba.... Idan kuma hakan tafaru na yafe miki ke kikaci kadan💧✨

*PAID BOOK ₦200only*

Page9️⃣

*TUSHEN LABARI*

Alhaji Kabir mashi shine cikakken sunan mahaifinsu Nu'aim, babban ɗan kasuwane wanda duniya tasan da zamansa ,yanada jijiyoyin kasuwanci aƙasace aƙalla biyar na ƙetare dama iyaka ,matansa biyu tafarkon itace Hajiya Aisha wato ƙanwaar mahaifin indo kenan
Hajiya A'isha ta kasance mace mai sanyin hali amma bata ɗaukar raini  ,tanada ƴaƴa uku ,Nu'aim shine nafarko wanda keda shekaru 27 aduniya,  sai Saddam shikeda shekaru 25 a duniya sai autarsu mai suna Ramlat tanada shekaru 18 a duniya

Sunan matarsa ta biyu kuma Hajiya Zaliha ,Hajiya Zaliha dai takasance mace maison abin duniya ,sam batada godiyar Allah,ga baƙin kishi da makirci wanda aduniya banda Hajiya A'isha babu wanda ta tsana sai Nu'aim ,Hajiya Zaliha takasance ƙanwa ga mahaifiyar khaleesat matar Nu'aim
Tanada yara biyu ne kacal aduniya, babban shine kamal shekarunsa 26 a duniya sai ƙanwarsa basira wacce takeda shekaru 18 a duniya

*Zamuzo muji wani kalan zama akeyi acikin gidan Alhaji kabir mashi anan gaba kaɗan*

*WAYE NU'AIM WACECE KUMA KHALEESAT*

Nu'aim dai yakasance mutum wanda baicika son shiga abinda ba'a kasa dashiba ,banaace masa miskili ba amma kuwa bada kowa yake mu'amala ba ,sannan mutumne mai ra'ayin kansa ,mutane kan yabi halayensa wasu kuma sukan kushe ataƙaice dai Nu'aim sai ahankali🙄matarsa ɗaya mai suna khaleesat, shekararsu biyar da aure amma sam ko ɓatan wata bata taɓayiba wanda hakan ba ƙaramin ɗaga musu hankali yakeyiba baki ɗaya ,barinma khaleesat tafisa damuwa  sabida wani ƙudiri nata itada uwarta wanda zamu sani anan gaba kaɗan
Khaleesat dai sun haɗu da Nu'aim ne tadalilin ƙanwar mahaifiyarta dake auren mahaifinsa takan kawo musu ziyara akai akai dan babu ƙarya abin ajini yake duk inda akwai danshin Naira toh Insha Allahu saikaga khaleesat agurin ,wanda akan dukiya babu abinda bazata iya aekatawa arayuwarnan ba
Tunda take zuwa gidan Allah baitaɓa haɗa su da Nu'aim ba sabida shiba mazauni bane kasancewarsa soja ,kwatsam akaci Sa'a Nu'aim yazo pass saiga khaleesat takawo ziyara kamar yadda tasaba
Kallon farko datayiwa Nu'aim taji aranta tayi miji
Sosai akasha artabu bana wasaba dan khaleesat tayi ƙoƙarin bayyana masa soyayyarta garesa amma tashin farko Nu'aim yayi mata tatas ataƙaicedai Saida mahaifiyata da ƙanwar mahaifiyarta wato Hajiya Zaliha sukayi ƴan shigeshigensu suka rufe idon kowa akayi auren ta dole batareda ran Nu'aim yaso ba
Hajiya A'isha sam bataso wannan haɗinba dagarko kamar daddy zai Goya mata baya amma aƙarshe saɓanin tunaninta saiya juya mata baya aka nuna mata fin ƙarfi saida akayi auren
Koda akayi auren Nu'aim gurin aekinsa yakoma hakan yasa yatafi da matarsa
Amma kace mai ...?
Tunda suka lula yadaina zuwa gida yadaina kiran gida
Baƙaramin tada hankali mami tayiba wanda hakan yasa daddy dakansa yashirya yarafi kasar Cairo domin duba lafiyar ɗan nasa
Da mamaki daddy yake kallon Nu'aim ganin lafiyar sa ƙalau ba yadda sukayi tsammanin ganiba
Nan daddy cikin ɓacin rai yasashi suka tattara suka dawo gida Nigeriya
Alokacin banda baƙin ciki babu abinda ke nuƙurƙusar khaleesat dan aduniya batason taga kowa yaraɓeta itada mijinta tafison daga ita sai ƴaƴanta idan sun zo duniya
Ahaka dai koda suka isa gida already gidansa dake gra layout suka sauka
Nan sabon iskancin khaleesat ya sauya salo domin kuwa idan akaje gidan sai tasa marigayi yake cewa kowaye yazo masu gidan basa nan idan kamatsa saika shiga sai mai gadi ya kira awaya ya faɗa mata babu kunya khaleesat zata fito tacemaka maigidan bayanan kuma ƙarya ne Nu'aim na ciki
Cikin rashin sa'a Ramlah tazo gidan labari ya maimaita kansa mai gadi yayi mata abinda aka saba sakashi data matsa sai ga khaleesat tafito ganin ƙanwar Nu'aim baisa tabarta tashigoba daga ƙofa tace mata "yayan naki ae bayanan " bata gama rufe bakiba saiga Nu'aim yakutso Kai mai gadi yabuɗe masa gare zai fita
Hakan kuwa sai akan idanun Ramlah
Nu'aim kuwa baima lura da wacce ke gurinba yayi wucewarsa hakan kuwa da yafaru sai yayiwa khaleesat daɗi
Haka Ramlah takoma gida cikin bacin rai
Koda mami taji abinda yafaru sai bata ɗau mataki ba tabarine saita tabbatar

*To be continued......*

INDON KAUYEWhere stories live. Discover now