INDON KAUYE part 6

125 3 0
                                    

🍃🍃🍃🍃🍃
    *_INDON ƘAUYE_*
           🍃🍃🍃🍃🍃

  (😂Funny and romantic story😂)


        *~ Na ~*

   🏵  *Asmieyn Sadeeq* 🏵
*HUSNA ABUBAKAR HUSSAINI* ✍

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

  ✨💧Tsokaci.... Wannan littafi na kudine Banyarda  wata takarantamin batareda hakkinaba.... Idan kuma hakan tafaru na yafe miki ke kikaci kadan💧✨

*PAID BOOK ₦200only*

Page 6️⃣

"Nidai asalin sunana AISHA sunan mahaifina ABUBAKAR mahaifiyata kuma MARYAM....shekaruna sha huɗu ,mahaifiyata da mahaifina sun rasu tun ina yar shekara huɗu a duniya , matan mahaifina biyu inna kande itace tafarko tanada yara guda biyu jummala da Abdullahi sannan  sai mahaifiyata  da ake kira da mairo itace ta biyu nikaɗai tahaifa kafin Allah ya amshi rayuwarsa,
Mahaifina ɗa ne ga AISHA da MUHAMMADU, Muhammadu wato kakana yakasance ɗan asalin garin Katsina, a ƙauyen suduji dake cikin Daura,haka kakata wato Aisha garinsu ɗaya da kakata sunada yara uku, babana wato Abubakar shine ɗansa na farko sannan sai gwaggo fatu sai autarsu Aisha ana cemata mami sabida sunanahaifiyarta akasaka mata domin agirin haihuwar tane kakarmu tarasu ,shine kaka yamaida sunanta sabida son dayake mata, to kaka dai bai sake aure ba har shima Allah ya amshi rayuwarsa ,kamar yadda na faɗa maka babana yarasu tun ina shekara sha huɗu, to Mami Kuma tayi aure Amma a birni saidai takanzo lokaci zuwa lokaci"
Tinda tafara magana ya ƙureta da idanu sosai yarinyar take birgesa....
Buɗe baki tayi daniyar magana saitaga ya ƙureta da idanu gashi a duniya indo tatsani kallo
"Wai ya da kallo...?"
Tafaɗa atsiwace
Ɗan yaƙe yamata tareda sosa ƙeyarsa
"Unmmm gani nayi kamar baki gajiya da magana"
Da kallon kama rainamin wayo tabishi
Kafin takaiga yin magana yayi saurin faɗin
"Kinga yahaƙuri tashi mutafi gida Kinga za a iya naiman mu",
Batareda tamasa musuba tamiƙe hartakama hanya saita tuna ae babu kaya ajikinta sai ɗaurin ƙirji.
Saddam da dama yaci burki yanaso yaga iya gudun ruwan haukar yarinyar ganin tajuyo kuma tanufi gurin kayan saiya kwashe da dariya
"Toh waida ke ahaka zaki tafi"
Batareda ta kulasaba tayi gaba abinta bayan ta zura kayan .
Koda suka isa gida basu samu kowa a tsakar gidanba sai Nu'aim wanda shima da alama fita zaiyi
Saddam na shigowa yafara aeka masa da wata uwar hada kai kace mace ne shi
Sinne kai kawai Saddam yayi yana ƙunshi dariya dan ko bai faɗa masana yarigada yasan laifinsa .
Da ƴan waƙe waƙenta ta ƙarisa shigowa hannunta riƙe da ƴar sanda ganinsu a tsaye yasa taci burki ,
Ko kallon inda take baiyiba yayi hanyar fita, saurin matsa masa tayi taƙame a bango ,hakan kuwa ba ƙaramin ɓatawa Nu'aim rai yayiba
"Wato yarinyar nan ma Ni take gudun haɗa jiki dani ko...?"
Yaɗa aransa ƙwafa kawai yayi yabawa rigarsa yayi waje
Indo kuwa naganin fitarsa tasauke ajiyar zuciya aranta tana mai tsine masa
Muryar inna tajiyo abayanta
"Ina kindawo ...? Toh maza kihaɗa murhu sannan kizo kisiyomin wake inɗora sanwar dazaki kaimin talla dandali zuwa anjima"
" Inna Wai ni zan fara talla...?"
"Na rantse indo kika tsaya min gaddama sainamiki ɗan banza duka sannan kuma dole kiyi talla dan ubanki tinda babu mai bani dan ci dake"
Jin za'ayi mata gorin da aka saba ne yasa taja ɗan ƙaramin bakinta ta tsuke cikin naiman zaman lfy tanufi inda ake haɗa hutar ta kama haɗawa
Saddam kuwa dake tsaye yana jin duk yadda sukayi kawai ya girgiza kansa yana mai ƙara gasgata zancen umman su , batareda yafurta komaiba ya kaɗa kai kawai yashige ɗakin da aka gyara domin saukarsu....
Tinda yashiga ɗakin babu abinda yake tunani sai rayuwar da ummansu tabasu labarin tayi ahannun inna kafin tayi aure, sosai yakejin tsanar inna kande sabida sam batada hali mai kyau tafiye son kanta dayawa ,amma dole yasan yanda zaiyi da indo bazai barta hakaba, gashi shikuma yanzu baida halin hanata wannan tallar da ake naiman fara ɗaura mata dama Nu'aim take shakka toh shi ga irin yanda Allah yayisa barinma yadda yaga yana nuna tsanar indon a fili yasan ko zaiyi bunga wallahi bazai taɓa sa baki a al'amarin yarinyarba ....
Nu'aim kuwa yana barin gidan kai tsaye cikin motarsa ya shiga bai tsaya ko ina ba sai asalin birnin jihar  garin Katsina domin Allah ya sani baijin zai iya zama batareda ya ɗan taɓa wani ɓoyayyen hali nasaba

INDON KAUYEWhere stories live. Discover now