INDON KAUYE part 15

54 3 1
                                    

🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃

    *INDON KAUYE*

🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃

*Story written by*
*HUSNA ABUBAKAR HUSSAINI* ✍ 
           *(Asmiey)......*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*

*Page 15......*


Aɓangaren Nu'aim kuwa suna shiga ɗaki ta kanainayeshi tahanasa saƙat

Saida ta gama lugwigwiceshi kafin daƙyar yasamu ya ƙwace yana mamakin jaraba irinta khaleesat kamar wacce ya shekara bai kusancetaba

Faɗawa bayi yayi domin watsa ruwa

Zuciyar khaleesat fessss mijinta yadawo gareta aɗaya ɓangaren tana mamakin wacece suka taho da ita kodai ƴar aeki ce ae kuwa zatayi sauri tace tanaso dan daga gani yarinyar zata moru

Aɓangaren mutuniyar kuwa

Bayi Ramlah tashiga tahaɗa mata ruwan wanka masu ƙamshi acikin bahon wanka kafin tafito

"Kitashi kiyi wankan gashican na haɗa miki ruwan"

Da toh ta amsa kafin tanufi bayin

Saidai mai tana shiga bayin da sauri ta fito taja tayi turus

Dasauri Ramlah tajuyo domin ku'wa harga Allah ta bata tsoro

"Ha'an indo badai har kinyi wankan ba ..?"

Turo baki tayi kana tace

"Toh ae ba bayi kika kaini ba "

Murmushi Ramlah tayi kana tace

"A'a indo ae wannan shine bayi"

"Taɓ wannan ne bayi..? Hum'in "

Kama hannunta kawai Ramlah tayi ta maidata bayi tareda yimata bayanin yanda zatayi amfani da komai

"Kin gane dai ko..?" Ramlah ta tambayeta

Ɗaga mata kai kurum tayi tana kallon kwamin wankan dake cikeda kumfa sai ƙamshi ke tashi mai sanyaya zuciya

Fitowa tayi kana tajawo mata bayin

Sake bin bayin tayi da kallo tareda kallon inda akace wai tashiga tayi wanka

Taɓe baki tayi kana tace

"Taɓ Allah ya tsareni da shiga wannan rafin kawai Salan ya haɗiyeni

Dabarace tafaɗo mata kawai ta watsa ruwa taɗaura zani tanufi hanyar fita

cikintane taji ya kurɗa da sauri takoma da kallo tabi ɗakin da akace mata wai bayine saidai sam bata ga gurin kashiba

Tsaki tayi kana tajawo wata leda data gani ake gefe da alama abu aka cire aciki aka manta ba'a fitar dashi ba

Gefe taja ta tsugunna abinta

*Nu'aim*...

Kwance yake tana manne a ƙirjinsa sai hirarsu suke cikeda nishaɗi yana bata labarin yanda zamansa ya kaya a ƙauye saidai sam bai bata labarin indo ba

Khaleesat ce tace

"Wai nikam love wacece wannan yarinyar da kuka taho da ita..?"

Numfashi ya sauke kana yace

"Sunanta indo anan zatacigaba da zama damu yarinyar yayan mami ne daya rasu"

"Unmm a ɓangaren mami zata zauna ko..?"

Ɗaga mata kai kurum yayi kana yatashi

Jallabiyarsa yajawo yazura

.itama tashi tayi tasaka kaya kana suka nufi cikin gida domin cin abincin maminsa



*Saddam*.....

Sauri sauri ya kammala shirinsa kana ya sauko ƙasa domin wani bala'in yunwa ke addabarsa.

A bakin ƙofarsa yaci karo da sadiya tana ƙoƙarin shiga ,dakatawa tayi ganin yama fito

Murmushi ta sakar masa shima ya maida mata kana suka jero suka sauko ƙasa a daidai lokacin suka haɗu dasu Nu'aim suma sun ƙaraso

Ƙarasawa sukayi gaba ɗaya suka zauna kan dinning

Hira suka shigayi tsakanin sadiya da khaleesat Saddam na ɗan jefa musu baki

Nu'aim kuwa wayarsa yake lallatsawa

Gyaran murya mami tayi kana duk suka ɗago suna kallonta

"Mami ina abincin am hungry wallahi" Saddam yafaɗa yana yamutsa fuska tareda rikee ciki alamun dagaskiyarsa yake magana

Murmushi mami tayi kana tace ae naga the table is not complete so kabari yacika tukunna

Yamutsa fuska sadiya tayi dan sarai tafahimci Ramlah da wannan yar ƙauyen mami ke magana

Taɓa baki khaleesat kurum tayi hakanan taji yarinyar batayi mataba

Aɓangaren Ramlah da indo kuwa

Sosai indo tayi mai isarta kana ta ƙulle abinta

Dube dube tayi kana ta hango window

Da sauri tanufi windon ta buɗe kashin taɗauko tareda cillasa da iya ƙarfinta

Wannan kashi kuwa bai sauka a ko'ina ba sai jikin windon bedroom ɗin Nu'aim

Wanke ɗuwawunta tayi kana tafito

Zaune ta iske Ramlah da har ta gaji da jiranta

"Haba indo ae ko canja fata zakiyi sai haka ace wanka fisabilillahi kusan awa " cewar Ramlah

Da kallon kimma rainani indo tabita kana tace

"Waya faɗa miki wanka kawai nayi toh har kashi saida nayi......

An sorry Insha Allahu gobe zakujini....

INDON KAUYEWhere stories live. Discover now