INDON KAUYE part 13

127 3 0
                                    

🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃

    *INDON KAUYE*

🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃

*Story written by*
*HUSNA ABUBAKAR HUSSAINI* ✍ 
           *(Asmiey)......*

PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*

*Page ...... 13*

BAYAN KWANA BIYU
Sosai walwalar indo yarage kallo ɗaya zaka mata kafahimci tana cikin damuwa sosai shima saddan yashiga damuwa
Tambayar duniya yayi mata amma taƙi faɗa masa dalilin sauyawarta a en kwanakin

Tauraron da inna kewa indo yakuma tsananta sabida ko fita tarage yi kullum tana gida sai aeki yamata ga talla

Ayau  Nu'aim da Saddam suka shirya domin zuwa ganin aekin dasuka saka ayi musu a gidan gonarsu

Indo na zaune a ruɓaɓɓen ɗakinta ta haɗa kai da gwiwa sai tunani takeyi yanzu idan cikin yayi girma yazatayi
Saddam ya daɗe tsaye a kanta batama saniba saida ya ɗan zungureta kafin ta zabura ta miƙe

"Kishirya muje ki rakani wani waje a mota"
Kai mai hali baya fasa halinsa ae tuni indo ta zabura ta miƙe ƙoƙarin cire rigar jikinta takeyi cikeda farin ciki zata yawo ganin haka yasa saddam saurin ficewa aɗakin yana mai farin cikin ganinta tana dariya

Bata wani ɓata lokaciba tafito sanyeda wata ƙoɗaɗɗiyar doguwar rigar atamfa tareda ɗan kwalinta
Cikeda murnarta tafito ƙofargida
Saidai farin cikinnatane ya maƙale mata a maƙoshi sakamakon ganin harda nu'aim zava tafi

"Ƙaaraso mana " inji Saddam ya ƙarashe tareda sake mata murmushi
Dan yafitosa tayi alamun ya matso
Babu musu ya matso dafff da ita
Akunnen ta raɗa masa
"Wai da wannan mugun zamu tafi..?"
Murmushi yayi kana yace
"Eh mana ae shine jagoran tafiya idan kikace nadashi za'a jeba yace afasama sai mukoma gida"
Zaro ido tayi kana tace
"Aaaaa haba tayyaa ae kawai muje dashi ƙila Yamamah anfani"
Dariya suka saki tareda tafawa
Ɗaure fuska Nu'am yayi tamau sabida tsaf yaji abinda sukace tareda buɗe mazaunin drivern yayi yashige haɗida banko musu ƙofar yana bin Saddam da mugun kallo
"Idan bazaka tafi bane saika koma gida" ya ƙarisa zancen da kawar da kai gefe
Saurin ƙumshe dariyarsu sukayi kana duk suka nufi bayann mota bai tanka musu ba saida suka shiga suka zauna indo sai washe baki take yau tahau mota suka tsinkayi muryarsa
"Ubanwa kuka maida driver ɗinku....? Ke dawo gaba kafin in takaki"

Dasauri tabuɗe tadawo gaba Saddam sai kumbure kumbure yake tafaman yi

Figar motar yayi bai tsaya ko'ina ba sai a wani tangamemen gidan gona
Zagaye zagaye suketa famanyi aciki suna duba yanayin yanda aka tsara musu gurin
Babu ƙarya gurin ya ƙawatu sosai domin ya haɗa abubuwa kashi kashi
Akwai ɓangaren kiwon kaji ,akwai na kifi, akwai na fruits  da dai sauransu
Sosai indo tazuba ƙauyanci tun Nu'aim na fiskewa har shima saida ya saki jiki yadara
Agajiye suka koma gida ahanya indo tahau bacci
Saida suka isa tafarka banda dariya da tsolanarta babu abinda Saddam yakeyi

*Bayan kwana biyu*
Shirye shiryen komawarsu birni ta kankama domin sun kammala abinda ya kawosu
Sosai indo tashiga damuwa domin babu ƙarya ta saba da Saddam sosai shima yasamu
Ana gobe zasu tafi Saddam yasamu Nu'aim da maganar sutafi da indo
Fafur yanuna masa baison zancen jiki a sanyaye Saddam yabar ɗakin a waje ya samu indo tazabga uban tagumi tana tunanin halin dazata shiga idan sun tafi ga muguntar inna danma tana ganinsu shiyasa take raga mata wasu abubuwan
Dafa kafaɗarta yayi
Ahankali taɗago suka haɗa ido ,kafin yayi magana tace
"Amma kayimin alƙawarin tafiya dani birni ko...?"
Kawar dakai gefe yayi ganin haka ta tashi da gudu tayi ɗaki

Yajima agurin kafin shima ya shiga ciki

Adaran suka haɗa kayansu domin tafiyar gobene
Jiki a sanyaye shima ya isa ga tashi jakar shirya kayansa yashigayi fuskarsa babu walwala ko kaɗan
Nu'aim na ankare da sauyawar ƙaninnasa amma ya basar
Saida suka gama shirya kayan tass tukunna suka naimi gun kwanciya

Awannan daren sosai zuƙata biyu suka kasance cikin damuwa domin kuwa kusan Saddam bai samu ya rintsa ba sai wuraren 2 na dare
Indo kuwa ae baccinma gagararta yayi kiran assalatun farko inna tazo ta tasota tafito waje takama aekace aekacen ta batareda tayi la'akari da sanyin da akeba haka bata damuba domin acewarta bataso taga wucewarsu gwara tayi aekinta tayi maza ta shige ɗaki

Nu'aim najin sanda inna ta taso indo hakan baƙaramin taɓa masa rai yayiba jin ita innar ta koma tayi kwanciyarta
Wayarsa ya lalubo ya duba time ƙarfe 4 da minti 45 tsaki yayi kafin yazura jallabiyarsa
Fitowa waje yayi ya isketa sai rawar sanyi take zubawa yayinda take wankewanke
Kawar da kansa gefe yayi kafin yace
"Ke wuce ciki "
Ɗago kai tayi ahankali tazuba masa manya manyan idanuwanta tace
"Yaya aeki inna tace kamata"
Tsawa yadaka mata "nace ki wuce ciki"
Jiki na rawa ta zuba aguje tayi ɗaki
Alwala shima yayi kafin yayi shigewarsa ɗaki

*Washegari*

Misalin ƙarfe 9 duk sun shirya cikin shiga irinta alfarma
Indo na ɗauki sai kuka take zubawa,yayinda jummala keta tsokanarta
",Hhhh shegiya aljana zamuga yanzu waye zai ringa tayaki ɗaibo ruwa da saro icce hhhhhhh waike zaki birni hhhhh basaikije in ganiba idan kika tafi ubanwa kikeso yarinƙa miki tallata"
Ire-iren kalaman da jummala taketa caɓawa indo kenan
Duk rashin haƙuri irinna indo ayau bata iya tace mata komaiba
Sai kuka kamar wacce akace idan suka tafi mutuwa zatayi
Dakin inna suka shiga domin yi mata sallama
Ayatsine taɗago tace
" to A'i tagaida asshaaa"
Nu'aim ne yace
"Toh inna mudai zamu wuce sabida mun kammala abinda ya kawomu so dan Allah ina naiman alfarmar tafiya da indo"

Da sauri Saddam ya ɗaugo kai yana kallon yayan nasa cikeda farinciki yake tunanin yaushe ya canja ra'ayinnasa

Muryar inna suka tsinkayi cikeda bala'i haɗeda tijara take faɗin
"Babbar bura ubannan kayyasa wacce indon inama laifi da jummala kace toh dana ɗan yarda amma kace indo...? Toh idan katafi da ita ubanka ne zaikemin ƴan aekace aekacen gidan...? Tallar fa wazai mata ..? Toh tun muna shaida juna ka kama hanyar ka kayi tafiyarka dan babu inda zaku da ita"

Bai ce mata komaiba ya fice a ɗakin
Kwance yasameta tayi rufff da ciki sai sauke ajiyar zuciya takeyi
"Ke tashi kifito muwuce"
Da wani irin bahagon super tatinƙura ta tashi
"Yaya dagaske...?"
"A'a dawasa ,Ni dallah kifito idan ba hakaba narantse wucewata zanyi"
"To toh bari na haɗa kayana"
Tsaki yayi ganin buhun da tajanyo wai kaya
"Kibarshiridan muka je can zan siyamaki wasu"
Washe baki tayi cikeda farin ciki
Tayi waje da gudu
Awaje suka iske Saddam
Suma gun motar suka isa cakkkk taja ta tsaya
Saddam dake murnar zava tafi da ita yashiga tambayarta dalilin tsayawarta
"Laaa bari na yiwa aminiyata sallama ince mata zan tafi birni " ta ƙarishe zancen tareda kwasawa a guje
Tarota Nu'aim yayi yace
"Waini ke wacce iriyar sakaryar yarinyace to na rantse kika tafi saimun wuce domin bazaku jirakiba"
Jiki asanyaye tazagaya tashige bayan mota

Dagudu jummala taje tagayawa inna gashicanfa zasu tafi da indo birni
Ae zani a hannu tafito aguje tana bala'i
Hangota da Nu'aim yayi ne yasa yatada mota tareda baɗeta da ƙura
Fuska jagejage da ƙura inna taja tsunmar kafarta ta koma cikin gida tana mai tsinewa su Nu'aim takeyi

******Sosai suke zuba gudu a mota domin daga garin katsina zuwa Kaduna tafiyar awa 3 ce
Sosai indo tayi danasanin biyosu sabida ganin nisan tafiyar
Can tace
"Yaya sadda wai haryanzu bamu kai bane dan Allah Ni kumaidani gida nafasa ɗuwawuna zafi yake min"

Murmushi yasakar mata kana yace
"Munkusa zuwa mai sunan mamina"
"Toh bari na rufe ido idan ankawonsai kace in  buɗe"

Da toh ya amsa mata
Tacikin madubin motar Nu'aim ke satar kallonta

INDON KAUYEWhere stories live. Discover now