INDON KAUYE part 7

101 2 0
                                    

🍃🍃🍃🍃🍃
    *_INDON ƘAUYE_*
           🍃🍃🍃🍃🍃

  (😂Funny and romantic story😂)


        *~ Na ~*

   🏵  *Asmieyn Sadeeq* 🏵
*HUSNA ABUBAKAR HUSSAINI* ✍

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

  ✨💧Tsokaci.... Wannan littafi na kudine Banyarda  wata takarantamin batareda hakkinaba.... Idan kuma hakan tafaru na yafe miki ke kikaci kadan💧✨

*PAID BOOK ₦200only*

Page 7️⃣

Ɗaukar tallar tayi da wanda aka zuba mata duk tahaɗa aɗari tabar gidan .....

Koda inna tafito daga kewayen batabi takan abincin taba ɗaki kawai tawuce domin miƙe gajiya
Aɓangaren indo kuwa koda tafita kai tsaye tasha tanufa inda anan yan ƙauyensu kezama domin tafiyar da kasuwancin su...

Ƙarƙashin wata bishiya gefen wasu ƴan mata biyu tasamu tazauna batareda takula kowa ba,
Ahankali tajawo farantin kayan sana'arta ta ɗauko wanda inna tabata matsayin nata nan tahauci hannu baka hannu ƙwarya
Ɗaya daga cikin ƴan matanne maisuna ladi ta yafito ta gefenta mai suna Abu tana nuna mata indo da baki
Kawai sai suka kwashe da dariya tareda tafawa
Tsayawa indo tayi cak da abinda takeyi ta ƙuresu da ido batareda ta furta komaiba, ganin dagaske da ita sukeyi yasa cikin bala'i ta nufesu gadan gadan batayi wata wataba tacacimi Abu da kokawa dan tafi ladi zaƙewa, kan kace kwabo tayi mata lilis ganin haka sai ladi tafara bawa indo haƙuri ,Abu kuwa taci na jaki ba baka sai kunne, Ana haka sai wani yaro yazo siyar gyaɗa indo naganin haka tayi caraf ta anshe kuɗin taja yaro inda kayan tallarta yake batareda takuma maganaba tazubawa yaron shinkafa tamiƙa masa .....yaro ya coge yaƙi amsa faɗi yake
"Niba hinkapa zan sayaba😥, gyaɗa nakeso"
Dan gwarar masa dashi agabansa tayi tana mai binsa da mugun kallo alamun karka ƙureni
Fashewa da kuka yaron yayi ,ganin zai tara mata jama'a yasa ta kwaɗa masa mari tareda sashi dole yaɗau shinkafar datasaka masa a leda ta koreshi...
Can saiga yaro yadawo tareda yayansa mai suna lawan
Tinda indo tahango haka ido ya raina fata dan babu ƙarya ƙato ne
Yana isowa dayake yaron ya nuna masa indo tindaga naisa kai tsaye kawai yanufeta
Da ido kawai indo ta kafesa don don ganin damai yazo dan harga Allah tafara tunanin sheƙa masa yajin shinkafarta
Tinda lawan ya kyalla yaga indo yaji zuciyarsa takamu,asukwane ya ƙarasa gareta
Ganin irin kallon dayake Binta dashi yasa itama jikinta yayi sanyi ahankali tamaida laidar yajin ta'ajiye..
Washe mata baki yayi yana sosa ƙeya, ganin haka sai indo ta tsuke fuska takoma mazauninta tazauna

*****************
Zaune take a kan makeken gadonta daya ƙawatu da lafiyayyen sanin gado mai kalar ruwan ganye... kallo ɗaya zaka mata kasan ba ƙarya Naira tazauna , kyakkyawar gaskece domin kuwa kallo ɗaya zaka mata ka hango kyawun nata ,farace tass babu ko sirki, dukda zaune take zaka fahimci babu ƙarya ƙirarta a ƙare take ataƙaicedai khaleesat tayi tako ina ba raini ...
Tsaki. Danaji ta jaane yadawo dani daga duniyar zayyano halittar khaleesat dana tafi
Hannunta riƙe yake da waya da alamu kira takeyi amma wanda take kiran bai amsaba ..
Yatsina face ɗinta tayi ganin an ɗaga wayar...
Kamar batason magana tabuɗe baki dakyar tace"aloooo"
Aɗaya bangaren ya amsa da "hey babe "
Jin muryarsa kaɗai ya sanyayawa khaleesat zuciyarta da takasance cikin ƙunci a ƴan kwanakinnan sakamakon kewar mijinnnata mafi soyuwa agareta datake kwana dashi take tashi...
Jin shiru ba amsa yasa cikin cool voice NASA kamar wanda baison yin magana yace "hello babe kina jina kuwa ...?"
Da "unmmm" kawai ta amsa sakamakon jin harshenta yayi mata nauyi da duk wata gaɓa tajikinta
Ahankali tajawo pillo ɗin gefenta ta rungume domin wani kalar kewar mijinta takuma ji ya lulluɓe ta
Fahimtar hakan dayayi kuwa saiya saki murmushi afili yafurta "hhhh haba Madam badai harkin hau network ba..?"
Cikin shagwaɓa tace "unmm Ni wallahi hearty banyardana , Allah yakamata kadawo haka ,kasan yadda nake buƙatarka akusa sani kuwa...?"

Murmushi kawai yayi aransa yana mai mamakin irin jarabar khaleesat dan duk maitarsa toh tinda yagamu da khaleesat yagane shiɗin wasane, wani lokacin har tsoro take basa , yanzu kwana biyu kacal da bata jisaba shine duk tabi ta ɗaya hankalinta, toh inaga anturasa course inda bazaiyu yaje da itaba...?

"Hello hearty kana jina kuwa..?"
Numfashi yasauke jin ashefa basu gama wayar ba
"Unmm ina jinki Matana abar ƙaunata"
Lumshe idanunta tayi tana maiji inama zata buɗe idanunta taga gwarzon mijinnnata a gefenta

Ahaka dai waɗannan masoya sukasha soyayyarsa nidai nan na barosu jin khaleesat nason sakin layi😜

******************
Indo kuwa nan lawan yamata juye yabata kuɗin shinkafarta harda ɗori akai cikin farin ciki tayiwa su abu da ayanzu sun zama ƙawaye sallama tanufi gida
Ahanyarta na shiga gida taci karo da Nu'aim da alamu masallaci zashi kallo ɗaya tayi masa taɗauke kanta zata shige gida
Harta saka kai kawai taji an fusgota tayi baya
Azabure tashiga rarraba idanu
Kafeta yayi da idanu yagama ƙare mata kallo kafin yashiga magana ahankali amma wai anan shi dole faɗa yakeyi
"Ke wacce kalar shashashace da baki iya gaida nagaba dake...?"
Da kallo kawai take binsa dan idan zaka kashe indo alokacin batsan mai yake cewa ba itadai taga ɗan ƙaramin bakinsa na motsi kuma saita shagala da kallonsa batareda ta ankara da wanda ke gabantaba
Marin ɗaya kwasa matane yadawo da'ita daidai kawai saita fashe dakuka tareda cukwikwiyesa duk ta tsorata gani take zai kuma sakar mata wani...
Cikin tashin hankali yashiga ƙoƙarin rabata da jikinsa amma ina saikuma naniƙesa da take kuma
Sosai yakejin yanayinsa na sauyawa daga maikuzari zuwa mai kasala, jin haka yasa cikin ɓacin rai yadaka mata tsawar data gigita indo babu shiri tacikasa
Arikice tayi cikin gida bata ko cikin nutsuwarta

INDON KAUYEWhere stories live. Discover now