INDON KAUYE part 8

95 3 0
                                    

🍃🍃🍃🍃🍃
    *_INDON ƘAUYE_*
           🍃🍃🍃🍃🍃

  (😂Funny and romantic story😂)


        *~ Na ~*

   🏵  *Asmieyn Sadeeq* 🏵
*HUSNA ABUBAKAR HUSSAINI* ✍

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

  ✨💧Tsokaci.... Wannan littafi na kudine Banyarda  wata takarantamin batareda hakkinaba.... Idan kuma hakan tafaru na yafe miki ke kikaci kadan💧✨

*PAID BOOK ₦200only*

Page 8️⃣

Cikin tashin hankali yashiga ƙoƙarin rabata da jikinsa amma ina saikuma naniƙesa da take kuma
Sosai yakejin yanayinsa na sauyawa daga maikuzari zuwa mai kasala, jin haka yasa cikin ɓacin rai yadaka mata tsawar data gigita indo babu shiri tacikasa
Arikice tayi cikin gida bata ko cikin nutsuwarta
Koda ta'isa ciki tsaye ta taradda inna riƙeda ƙugu da wani kalan mugun kallo take binta
"Dan ubanki Ina kuɗin tallah na...?"
Ciro kuɗin tayi a gefen ɗankwalinta batareda ta kalletaba tabata
Fisgar kuɗin tayi tafara ƙirgawa ganin kuɗin yacika harma da ɗorin Naira hamsin kawai saita hau salati da sallallami
"Yanzu indo dama maganar da nakeji agari dama dagaskene ....? Toh inba da gaskeba dan uwarki nasaka miki shinkafar ɗari huɗu da Talatin ki dawo min da ɗari biyar ,toh gidan ubanwa Kika samosu...? Nace gidan ubanwa Kika samosu..?"
Da kallon mamaki indo kawai take binta dan ko bata fito fili tafaɗaba mataba ta fahimci ina zancenta yadosa
Cikin hawaye indo tace "inna wani ne fa yayimin juye shine yabani kuɗin gaba ɗaya"
"Innalillahi wa'inna ilaihi raaji'un wato dai yatabbata dama bin mazan kikeyi idan kin fita gantalinki idan ba haka shiɗin ƙarunane dazai kama yimaki juyen hinkafa harta ɗari biyar batareda kin masa wani abuba ..?"
Ƙasa magana indo tayi kawai saita hau kuka
"Ba kuka zakiminba ubanki zanci dama ae gado ba wasaba idan bakiyi bama ae sainaji dalili shegiya mayyar maza idan kinso ko ciki kikaga damaryi kizo ki haife Ni baidameniba ko babu komai nasamu ɗan aeke tallah kuwa babu fashi yanzu ma na koko zaki juya gashinan na dama ,dama ke nake jira maza kiɗauka ki koma saura ki koma kwarton naki yakuma yi miki juye"
Babu ƴanda ta iya haka tanufi inda robar kokon take ta'aza akai tayi waje domin komawa
Tana fita fuskarta shaɓe shaɓe da hawaye taci karo da Saddam yana ƙoƙarin shiga cikin gidan cikin tashin yyashiga faɗin "Ummina yadai maiya faru kike kuka..?"
Ƙasa magana tayi sai kuka ,ganin takasa magana yasa kawai yahau lallashinta,
Tin yanayi da baki har yakai yarungumota yana lallashinta tareda mata alƙawarin tafiya da ita birni
Jin zancen birni ae kawai sai indo tasaka tsalle taɗale wuyansa tana ihun murna
Adaidai lokacin Nu'aim yakaryo kwana
turus yaja ya tsaya yana mai binsu da mugun kallo
Saddam ne yafara ankarewa nan yashiga kici kicin sauketa amma ina murna tarufewa indo ido batamasan yanayiba
Kaɗa kai kawai Nu'aim yayi kana yayi shigewarsa ciki zuciyarsa banda tafasa babu abinda takeyi

***************************
Agarin Abuja kuwa
Khaleesat na hango a falonta tareda wata budurwa wadda kallo ɗaya zaka mata kafahimci ƙanwace agun khaleesat domin sosai suke kama saidai ita batada haske she is dark in comflexsion Amma dai tanada kyau ba laifi
"Yaya dan Allah kishigemin gaba naroƙeki nasan yaya Nu'aim nasonki dole zaibi zaɓinki kodan farantamiki , amma wallahi Allah yasani bazan iya haƙuri da Saddam Ba "
"Hmm Amma ke wallahi sadiya kina bani mamaki ,wai ina ajin naki...? Ina kissar taki..? Ina fasahar taki ...? Da namiji kwaya ɗaya tal yake naima ya gagareki, mai akayi akayi namiji balle wani Saddam da lokaci ɗaya idan nayi yanzu zai shiga hannu , wai ke harkin manta letures ɗin mommy ne ..? Hhhhh ko kin manta yadda mukayi lokacin Nu'aim , toh wallahi kema tanan zakiyi ki damƙo ɗan banza amma yanzu bama wannanba kinsan sun tafi Katsina yau kwana uku kenan Amma hearty yacemin Insha Allah Nanda Friday zasu dawo, kinga kima dawo nan ɗin da zama koda sun dawo sai plan ɗin namu yatafi yadda Yakamata , ammakiyi hankali da hajiyarsu matarnan yar jaraba ce na rantse kekuma gaki da zuciya toh wallahi indai kinason kiyi achieving goals ɗinki akan Saddam dole ki koyi kawaici da haƙurin dole "

Sauke numfashi sadiya tayi jin zancen yayar Tata
"Amma anty kina ganin zamana anan bazai jawo wata matsalarba fanni wallahi mata tamin sainaci uwarta"

"Dalla matsa banza toh ahaka kikeson mallakar Saddam ɗin tab toh wallahi ina faɗa miki uwarsu atsaye take akan ƴaƴanta ke kin manta wai abinda yafaru abayane ...? Ina ba a Cairo mukeba Dan kawai ya shekara baizoba shine aƙasa yadawo da yadawonma muka sauka a gidanmu ganin zan mata ɗanyan kai ba nan kusa da'ita tasa muka dawoba wanda dole sabida son danakewa hearty yasa na canza taku dan gani nayi ana naiman yin waje sani"

Dariya sadiya takwashe dashi tuna gwagwarmayar da yayar Tata tasha kafin zuwan wannan lokacin

Khaleesat tabuɗe baki zatayi magana sukaji ƙarar buɗe ƙofa ,bakowa bace face jidda yarinyar yayan daddy....
Da mugun kallo tashiga binsu ɗaya bayan ɗaya kafin tasaki shewa
"Wato ke sadiya bakiji warning ɗin danayi miki akan Saddam bako ...? Toh gaki ga gidan nida ke shege ka fasa muzuba mugani nida ke muga wazaici riba"

Tana kaiwa nan tabuga musu ƙofa tabar falon

Tirƙashi  ana wata ga wata wainikam ina labarinnan ya dosa ne...? Munata tafiya babu waiwaye.....

ASALIN LABARI

INDON KAUYEWhere stories live. Discover now