Part 16-20

1.4K 106 0
                                    

Zaune ta same shi cikin mota k'afafun shi a waje, yana ganin ta fito ya rufe kofar bakin shi har kunne, gaisawa sukayi agurguje ummi tace "am Jamal na fito ne dan na faďa maka ko wacece ni, muna cikin halaka Jamal " cike da mamaki yace "halaka kuma wace irin halaka ummi?" Kanta k'asa tace "Jamal nifa ba yanda ka ďauka bace, a yanzu haka inada aure akaina kuma na fito ne dan na fada maka haka, dan allah muyi hakuri da juna kaje ka nemi wacce ta fini, watakila itace mafi alkhairi a gareka" cikin wani irin yanayi yace" Aa Ummi dan allah karki min haka, wallahi ina sonki, kuma na faďa maki komi a game dani kinsan koni waye kinsan labaran soyayyata har guda huďu, Dan allah Ummi ki amince ki aure ni ko zaki chanza wannan labaran nawa marasa daďin ji, idan kuma baki so na ne basai kin b'ullomin da wannan hanyar ba"
"Aa Jamal ba haka bane, wallahi an ďaura min aure yanzu haka gobe zan tare in allah ya kaimu, haba Ummi kar ki raina min wayo mana, ki fito ki faďa min gaskiya kawai "cikin kosawa tace" kaga Jamal na faďa ma gaskiya ina da aure dan allah kar ka sake kirana kuma ka manta dani a rayuwar ka, ka gafarceni bansan haka zata faru ba, zata wuce ya rik'e hijabinta yayi dai-dai da karasowar Alhaji manu wanda ya tsinkaye su tun daga nesa amma amma yana tunanin kosu waye, yana ganin haka ya kunna tocilar shi dake hannun shi, da sauri Ummi ta juya sai ko yaga fuskarta, Ummi ma na ganin Alhaji manu ta tsorata sosai kubce hijabinta tayi ta ari na kare da gudu ta shiga gida, yayi dai-dai da fitowar La mamma da abba tare da Salman suna tambayar k'annanta dake wasa a tsakar gidan.

Yana ganin ta ruga da gudu ya ciro wayar shi ya kira AUWAL babban ďa ne ga baba yahaya, yana ďauka yace "kai kana ina?" Cikeda ladabi yace "yanzu na shigo gida zan gaida su Mamma" to mu haďu da kai gidan baban ka Hamidu" bai ko amsa ba ya kashe wayar, tunda ummi ta shiga ďaki ta kasa zaune ta kasa tsaye dan tasan yau kam sai allah babu abinda zai hana a daketa a gidan nan, addu'a take koda za'a daketa to kowama ya daketa amma banda yaya Auwal.

Kai tsaye falo ya shiga yana "kare ma su La mamma kallo babu wanda ya iya tambayar shi lafiya saida auwal ya shigo sannan ya kalli La mamma yace "Hawatan kin bani kunya banyi tsammanin haka daga gareki ba, na ďauka amanar dana baki zaki kula da ita ashe ba haka bane" cikin rashin fahimta jiki na rawa La mamma tace "mi kuma ya faru wallahi bansan komi ba alhaji" maida kallon shi yayi ga salman yace kira min ita" wucewa yayi yana tunanin komi tayi hatsabibiyar oho.

Yanda ya ganta tana ta safa da marwa yasa yace "wace tsiyar kikayi?" Hararan shi tayi ta cigaba da kai da kawo warta, "to wuce muje alhaji na kiranki kuma allah yasa ya bani bulalar da kaina na zane ki" yan cikinta ne suka kaďa da sauri tace "bulala kuma?" Gira ya ďaga yace "ai ke da kinga auwal kinsan da bulalar shi yazo saboda ire iren ku" inna lillahi wa inna ilaihi raji'un na shiga ukku, yaya salman ka taimaka min wallahi babu abinda nayi,kace karya dakeni "ke wuce muje ni nasan mi kika aikata, ina mijinki bansan fitarki ba saidai naga kin dawo" wuce wa yayi ya barta nan kamar zatayi fitsari daga tsaye, jin muryar alhaji ne "yana fadin kaga kace mata in bazata fito ba ni saina shigo na fito da ita" a hankali ta buďe kofar dakin tana raba idanu ganin Auwal ya kara kaďa mata yan hanjinta, kusa da La mamma ta durk'usa kamar zata shige jikinta, cikin bacin rai alhaji yace "ummi ni zaki zubarwa da mutunci, ni zaki tozarta a unguwar nan ki fita wajen wzni ďan iska har yana rik'e miki hannu" to bara kiji wallahi baki isa ba ko ubanki bai isa in shinfiďa doka ba "ya ketare ta bare ke yar daya haifa" carbin dake hannunn shi ya cilla ma Auwal yace "zane min ita ta yanda bazata sake tunanin sab'a ma umarni na ba nan gaba" tsabar rashin imani da tausayi yasa Auwal jayo hijabin Ummie ya fara tsula mata carbin kamar allah ya aikoshi, ihu take taba ba alhaji hakuri amma ina ga abba zaune amma babu yanda zaiyi koda Ummie taji dukan na ratsa har cikin ruhinta sai ta fara kiran sunan "wayyo La mamma kice yayi hakuri wallahi bazan sake ba, Abba ka bashi hakuri wallahi babu abinda nayi, wayyo yaya Salman dan allah kace yayi hakuri" har saida hijabinta ya fita ta zama daga ita sai doguwar riga, ganin yanda take tana kokarin shigewa jikin auwal tana so ta rik'e carbin yasa Salman jin ba daďi, mikewa yayi ya rik'e carbin ya kamo Ummie da hannu ďaya ya kalli alhaji yace " Dan allah ayi hakuri bazata sake ba insha'allahu" mik'ewa Alhaji yayi tsaye yace " kwarai bazata sake ba kamar yanda bazata sake koda awa ďaya a gidannan ba" kallonta yayi ya daka mata tsawa "wuce mu tafi" raba ido tayi don batasan inda zata wuce ba duk ta ruďe "zaki wuce ko sai na sa ya ďauko min ke?" Da sauri ta dauki hijabinta jiki na rawa duk zugi takeji a jikinta saida takai bakin kofar ďakin sannan ta juya ta kalli su Abba cikin kuka tace "Abba ka yafe min dan allah, La mamma kiyi hak'uri" da sauri ta bar wajen suna fita kofar gida Alhaji yace ma Salman "dauko motarka na kaita gidanta" mamaki ne yasa Salman yin tsaye amma daya mashi tsawa saiya wuce babu shiri ya ďauko motar, basu tsaya ko ina ba sai sabon gidan Salman da duka jiya ne aka kammala gyaran shi, yana iza k'eyar ta yace Salman ya maida shi gida suna tafiya Ummie ta faďi k'asa ta fashe da kuka tare da k'ara kamar ta kashe kanta take ji.

Love you all❤

Auren Haďi (COMPLETE)Where stories live. Discover now