PART 1-5

3.5K 173 2
                                    

PART 1-5
💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗
𝙱𝚒𝚜𝚖𝚒𝚕𝚕𝚊𝚑𝚒 𝚛𝚊𝚑𝚖𝚊𝚗𝚒𝚛 𝚛𝚊𝚑𝚒𝚖
💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗💗

𝙳𝚊 𝚜𝚞𝚗𝚊𝚗 𝚊𝚕𝚕𝚊𝚑 𝚖𝚊𝚒 𝚛𝚊𝚑𝚊𝚖𝚊 𝚖𝚊𝚒 𝚓𝚒𝚗 𝚔𝚊𝚒

𝚈𝚊 𝚊𝚕𝚕𝚊𝚑 𝚢𝚊 𝚢𝚊𝚏𝚎 𝚖𝚒𝚗 𝚔𝚞𝚛𝚊𝚔𝚞𝚛𝚊𝚒𝚗𝚊 𝚒𝚍𝚊𝚗 𝚗𝚊 𝚛𝚞𝚋𝚞𝚝𝚊 𝚍𝚊𝚒𝚍𝚊𝚒 𝚊𝚕𝚕𝚊𝚑 𝚢𝚊 𝚋𝚊𝚖𝚞 𝚕𝚊𝚍𝚊 𝚒𝚍𝚊𝚗 𝚔𝚞𝚖𝚊 𝚊𝚔𝚊𝚜𝚒𝚗 𝚑𝚊𝚔𝚊 𝚊𝚕𝚕𝚊𝚑 𝚢𝚊 𝚢𝚊𝚏𝚎 𝚖𝚊𝚗𝚊 𝚋𝚊𝚔𝚒 𝚍𝚊𝚢𝚊

Duk girman gidan bai hana cika da mutane ba saboda hidiman biki da akeyi, kowa farin ciki yakeyi ba bakin ciki a nata hayaniya, shagalin biki kenan da za'a daura nan da minti ashirin, amare ne guda hudu da angwayen su.

Ban an kara ba naji an bige ni in juyowa naga wata kosansan budurwa nagani sai gudu take tana waiwayen bayanta kafin na kula naga wani 'kakk'arfan saurayi da gudu yana biyarta da belt a hannu, bin bayan su nayi har cikin katon falon inda taci karo da wata kyakyawar tsohuwa ta b'oye bayan ta tana fadín,

"Dan allah hajiya ki taimakeni kice karya dakeni" tsaye yayi yana huci, cikin zafin rai ya kaimata duka da belt din hannun shi yanda ya sauka a bayanta ne yasa tasaki wani ihu, tsohuwar ce da ranta ya ba'ci tace "kai SALMAN ashe bakada hankali wai miyasa kuke hakane kamar wasu kananan yara?" Juyawa tayi ga yarinyar ta jawo ta tace" mi kika mashi nasan dai bai biyo ki haka nan tunda shi ba mahaukaci bane shi?" Cikin kuka tafara mata bayani" wallahi hajiya muguntar sace ta tashi, daga naji karb'ar charger wurin yaya MUBARAK shine fa kawai yake kallona daga nace ya kama bakin shine ya biyoni" tana rufe baki ya kama kunnen ta cikin masifa yace "kinji ta ko hajiya dan ta raina ni ni zatace wai nakama bakina, ina abin kallo ajikin ta yake, wallahi saina karyaki in kika k'ara shiga harkata shed'aniya kawai" fizge kunen ta" tayi cikin zafin nama ta mike tsaye zatayi magana kuma saita ruga a guje sabida ďaga belt din da yayi zai buga mata, juyawa yayi shima yabar wajen.

Saida tabi kowannen su da kallon sannan tace" na samu hanyar da zanyi maganin ku tak'adaran yara kawai, kuna yan uwa amma kun zama b'era da mage, insha'allah komi yazo k'arshe daga yau, idan kuka zama ďaya zaku daina duk, wannan shirmen" wucewa tayi ďakin kakan yaran inda bata gushe ba har saida burinta ya cika

09:00 aka ďaura auren amare huďu gamida wanda aka k'ara suka zama su biyar.

   Ko suwaye cikon na biyar din nan🤔
  Ku biyoni domin cigaban labarin

Please and please vote and comment because your vote will encourage me

Love you all😘❤

𝙼𝚊𝚎𝚎𝚖𝚊𝚛𝚑♡︎

Auren Haďi (COMPLETE)Where stories live. Discover now