Part 26-30

1.2K 59 0
                                    

(AUREN HADI)
::

:
Misalin 11:30 ya farka, wanka ya fara yi ya fito ya kalli agogo, tsaki yayi yana fadin me yarinyar nan take nufi da ni ne da har yanzu bata kawo min Tea na ba?"wani tsakin ya k'ara saki ya fito ya nufo k'ofarta, zai bud'e wata zuciyar ta gargadeshi karya sake ganinta a yanda ya ganta dazun, ya dan jima a tsaye kafin ya zira kai cikin d'akin, ga dukkan alama tayi nisa a cikin baccin ta har yanzu babu riga a jikinta tayi rub da ciki, sai lokacin ya kalli shatikan carbin da ke bayanta duk ya farfashe, ga kananan kitsonta da ya kwanta a bayanta kamar ya taba wata zuciyar ta gargade shi, k'afarta ya kama ya fizgo a tsorace ta mike zaune tana murza ido tare da kallonshi kafin tace" wai dan Allah miye haka, haka ake tada mutum daga bacci kamar a gidan mahaukata, kai idan aka maka haka za kaji dad'i?" ke rufe min baki ina abinda na saki?" kallon shi tayi ido bude tace" wane abu kuma?" Tea din fah, ko ni kike so naje na dafa?" kau da kai tayi tace" nifa ba zan'iya ba, ace Tea ba za'a shashi da safe ko da rana ba sai dare yayi kuma sai na kai har cikin d'aki haba gaskiya da sake" ganin ya fara waige waige yana neman abun bugu yasa ta tashi da gudu ta bar d'akin ta shiga cuisine ta fara hadawa.

Tana kammalawa ta kawo mashi har dakinshi, kallo d'aya ya mata yaga bacci pal a idonta dan haka sai yaja tsaki yace" ba kida aiki sai bacci kamar kasa" lumshe ido ta sake mika mashi faranti tace" ni ka karb'a dan Allah  tafiya xanyi, wata harara ya watsa mata yace" ki aza a kaina mana tunda ba babu wurin ajewa" gefen gadon ta d'ora harta juya zata fita yace" waye zai zuba kenan?" dawowa tayi  ta zuba mashi kallonshi tayi cikin muryar bacci tace" sugar nawa zan saka a ciki?" daya" ya bata amsa idonshi na kallon hannayenta da suka sha jan lalle da bak'i abin sha'awa,tana gamawa ta mika mashi wani kallo yayi mata yace" ki aje ko dole sai na karba" ajewa tayi ta juya cikin magagin bacci  ta fita, har saida ta fice, sannan ya kalli faranti yanda ta kawatashi ma kad'ai da abin birgewa ne ga kamshin da ke tashi mai dadi, d'auka yayi ya kurb'a har saida ya lumshe ido dan shi kansa yasan Bai bata shan  tea mai dad'in wannan ba kuma gashi duk abinda ake sakawa a waccen nan ma an saka "to miye banbanci?" ya tanbayi kanshii

Yau ma da zazzab'i ta tashi tana yin sallah asuba ta nufi cuisine dan ta tuna abinda ya fad'a mata akan girkin, gashi kuma ta d'ora mai wuya abincin da Abbanta yafi sone ya karya dashi ta d'ora tuwon shinkafa da miyar agushi, duk da ta d'ora da wuri saida tayi late akan lokacin da ya bata sakamakon zazzab'in daya addabeta ga kuka da tasha abunta ta k'oshi.

Tana fitowa zata aje kwanukan ta ganshi zaune ya hakimce rai a b'ace saida ta gama jera duka kayan ta zuba mashi zata wuce d'aki yace" zonan" dawowa tayi ta tsaya sannan yace" k'arfe nawa yanzu?" da k'yar ta gane lokacin dan jiri kawai take gani, a hankali tace" 08:22" bien" ya fad'a yana kallonta yace" nawa mu kayi da ke na dinga samun abinci a nan" kamar za tayi kuka tace" dan Allah kayi hakuri banji dad'i ne shiyasa, kuma kaga tuwo ne nayi" cikin tsawa yace" to sai me, ina ruwana da abinda kika dafa, kina nufin haka zan dinga zaunawa jiranki kullum kenan?" dafe kanta tayi saboda sarawar da yake mata gashi shi kanshi Salman k'in guda uku uku take ganinshi dan haka tace" kayi hakuri dan Allah ka taimaka ka siyo min madara wallahi mutuwa zanyi" wani kallo ya mata yana magana akan wani abu ita kuma tana magana akan wani abu daban, kafin ya ankara ya jita a k'asa ta fadi hannunta kuma har yanzu a kanta ya ke, cikin bacin rai yace" ke dan Allah tashi miye haka kamar wacce tasha k'waya" ya jima yana mata magana amma kamar bada ita yake ba, dan haka ya kama ta, ta mike tsaye ya zaunar da ita akan kujera, da kyar take bud'a baki tana fad'in" madara yaya Salman dan Allah ka Siyo min in sha" hararanta yayi yace" ke tafi can sai naci na koshi in yaso na siyo maki jarababba kawai kin d'ora ma kanki shan madara kamar wacce saniya ta haifa" kanta a duke tace" kaima  miyasa ba zaka siyo min ba in yaso sai kaci tuwon, kenan duk jarabar gare mu, kuma wallahi saina fad'ama la mamma nace ka ce mata saniya tunda ai kasan ita ta haifeni in ba kana san cin zarafinta ba miye na had'a yar da ta haifa da saniya" maida hankalinshi yayi ga cin abincin shi har saida ya koshi sannan ya fita ya barta a wannan halin.
:
Tunda ya fita bai sake tuna wata Ummi ba harkokin gabanshi kawai yake hankali kwance har saida lokacin dawowar shi yayi da rana, kai tsaye yazo gidan yana shigowa baiga alamun girki ba dan haka ya d'auko belt a d'akinshi ya nufi d'akin Ummi da ke kwance tun safe ga ciwon kai ga zazzab'i ga amai da take na duk wani abinda ta ci....

Auren Haďi (COMPLETE)Where stories live. Discover now