96-100

955 62 0
                                    

(AUREN HADI)
:

:

Ummi ce ta fito daga daki da gudu ta taka d'aya daga cikin kujerar dinning ta dire kan dinning d'in tana dariya daga ita sai daurin kirji da key din motarta a hannu, Salman ne ya fito cikin k'ananan kaya yana mika mata hannu yana fadin "haba jaririyata ki bani mana yanzu zan dawo fa."

Cikin dariya tace "um um , gaskiya ba zan baka ba, nasan yanzu da kan tafi saina koma inna kiranka, ni kuma gashi nayi wanka kaya kawai zan saka ba sai muje na kaiku ba."

Dafe kugu yayi yace "kin yarda zaki kaini da kanki?"

Cike da tabbatar masa tace "Allah kuwa da gaske nake."

"To kije kiyi sauri kisa kayan dan Allah karki jima."

"To" ta fad'a tare da daga masa hannuwa tace "to sauko dani na kasa."

Kallonta yayi yace "da nine na doraki?"

Turo baki tayi tace "dan Allah ka saukeni, ko so kake wajen saukowa da kaina na bude kafafuna iska ta shiga? "ta karashe maganar tana fashewa da dariya.

Ido ya zaro tare da zura hannayenshi ya sauko da ita yana fad'in "kai, ai ba zanso haka ba, bana so kuwa iskan ya shiga."

Haka ya zauna yana jiranta, bata jima ba ta fito cikin doguwar rigar atamfa sai hijab da nikab data saka, fita sukayi ta kulle ko ina kafin ya shiga motar tata suka wuce izuwa in da yake zama, ya yarda da tuk'inta shi yasa ya dinga mata hira suna dariya wani lokacin har tsakulkuli yake mata, haka har suka kai in da yake zama kaf abokananshi idansu ne ya dawo kansu, yayin da mafi yawansu suka k'ara ji har zuciyarsu sun birgesu tare da fatan ina ma sune, su kuma 'yan badanul aswad kuma suka ji ransu ya baci tare da takaici.

Gaishe dasu tayi cikin girmamawa kowa ya amsa da fara'arsa,Khamis ne ya taso suka gaisa da Salman sannan yace ma Ummi "yau kuma ke kika kawoshi da kanki?"

"Eh, yaya Khamis yau rigima suke ji wai dole da mota ta xan kawo shi,

"To ina zaki yanzu?"

Sai da ta tayar da moton tace "gida zanje, amma saina biya naga Jawahir da kuma amaryarka."

"To Allah ya kiyaye hanya, ki gaishemin da Jawata nima."

Dariya tayi tace "to amaryar fa?"

"Kiyi abinda na saki kawai."ya fad'a yana jan Salman izuwa wajen zamansu.

Hannu Salman ya d'aga mata yace "ki kular min da kanki, sannan ki kula da hanya sosai kinji ko."

Itama hannu ta d'aga masa tace "ku kular min da kanka, saina dawo."

Saida ta bace wa ganinshi sannan ya zauna suka fara gaisawa da abokan nasu, anan kuma hira ta barke irin tasu ta maza.

Bata jima gidansu Jawahir ta wuce gida zuciyarta d'auke da tunanin yanda taga matar Khamis kamar ba amarya ba, dan kayan dake jikinta ma daban daban ne, haka har takai gida, gidan su Salman ta fara zuwa ta samu tarba wajen Mama dan da kyar ta samu ta fito ta leka gidan Alhaji da kuma nasu gidan, ko kad'an Mama bata nuna mata damuwa ko wani abu dangane da rashin haihuwarta, wannan kuma na kara kwantar mata da hankali tana kuma jin dadi sosai.

Sai bayan sallah isha ta kama hanya, saida ta biya ta dauki Salman sannan suka wuce gida cikin farin ciki da nishadi abinsu,
:

*BAYAN SHEKARA BIYU*
:

Ummi ce zaune a tsakiyar gado tana ta ruzgar kuka iya k'arfinta, Salman ne gefenta ya kura mata ido yana kallo dan ya gaji da rarrashinta, ganin kukan bana karewa bane yasa sake gyara zama yace "Ummi na baki hakuri yafi cikin carbi amma kink'i hakura, ban san ya kike so dani ba."

Auren Haďi (COMPLETE)Where stories live. Discover now