SHAFI NA BAKWAI

953 114 7
                                    

*** Washe gari haka ta tashi sukuku gaba daya bata da cikakkiyar walwala dan komai tana yinshi ne cikin sanyin jiki da rashin kuzari,ga tarin damuwa cunkushe cikin kokon ranta,yanzu idan wannan bawan Allahn yatafi bai dawoba ya zatayi? Wannan tambayar ita taketa nanatawa acikin zuciyarta ahaka tagama duk wasu aikace aikace da suke nata,

Tana runfar dabbobi tana sharewa gamida zuba musu abincin da zasu ci taga mai madi ta dauki mayafinta ta fita,barin abinda take yi tayi ta nufi tukunyar da akayi dumamen safe domin wata irin matsananciyar yunwa take ji kasancewar daren jiya bata ci komai ba,zama tayi ta cinye guntun tuwon da yarage acikin tukunyar wanda baifi guda daya da dan gutsire ba,tun kafin ta tashi daga wurin taji wani bugu agadon bayanta sannan cikin bala'i taji muryar dan marmari yana zuba mata masifar cinye masa dumame da tayi,

"Ubanwa yabaki tuwona da har kika zauna kika cinye min? Wallahi yanda banci tuwon nan ba kema sai kin amayar dashi....." Wata wawura ya kaiwa makoshinta hakan yayi daidai da shigowar mai madi,cikin azama taje ta kwace ta a hannun dan marmari wanda ke ikirarin sai ya lakada mata na jaki,ganin ya dauko wani katon ice yasata ranta a na kare shikuma ya take mata baya,

Gudu take kamar zata tashi sama dan marmari na biye da ita da icce,tana shan kwana tayi kicibus da zakar wanda ke sanye cikin uniform dinsa na NYSC yana rataye da yar madaidaiciyar jakarshi abaya kunnenshi makale da earpiece yana daddanna wayarshi,bangajeshi tayi batare da ta saniba har hakan yayi sanadiyyar faduwar wayar dake hannun shi, abayanshi ta boye jikinta na rawa kamar mazari,

"Baby..... Menene?" Ya bukata batare da ya dauki wayarshi dake kasa ba,

"Dan marmari ne zai dake ni...." Tun kafin ta rufe bakinta taji saukar icce akan kafadarta ta hagu,

"Ubanwa yasaki ki cinye min dumame na?"

Durkushewa tayi awurin tafara kuka hakanne yasake kular da zaks har zuciya ta debeshi ya shake dan marmari yafara kikkifa masa mari,cikin bacin rai da tashin hankali yake fadin,

"Waye yafada maka ana yiwa mace irin wannan dukan? Saboda baka da hankali kuma kai dakiki ne? Daga yau idan ka sake koda harararta ne wallahi sai na targada ka"

Shi dai dan marmari aguje ya bar wurin bayan zaks ya lallasashi. Tsugunnawa yayi agabanta inda take durkushe tana faman gursheken kuka,

"Kiyi hakuri baby girl...... Daina kukan haka kinji....."

Dan sassauta kukan nata tayi tana mai goge hawayen ta,

"Kinga yau nima gidanmu zanje intafi sai bayan weekend sannan zan dawo...... Ko zamu tare?"

Girgiza masa kai tayi tana share fuskarta,

"Kina tsoron kar na gudu dake ko?"

Murmushi ta dan yi sakamakon jin abinda yafada, hannunta ta saka cikin zaninta ta ciro masa identity card dinshi duk da bata son rabuwa dashi amma gara tabashi abinsa dan gudun samun matsala,

"Ga hotonka da ka yar rannan...."

Karba yayi yana dubawa cike da mamaki,

"Kayi hakuri ban san me amfani bane shiyasa na rike,bana son rabuwa dashi ne"

Murmushi yayi batare da yayi magana ba yaciro wallet dinshi daga aljihunsa ya bude,wani dan karamin hotonshi passport mai sanye da kayan NYSC yaciro ya mika mata,

"Idan hotona kike so gashi"

Karba tayi cike da farin ciki,shi kansa yagane tayi murna da hoton dan sai kallon hoton take tayi tana fara'a kamar ba itace tagama kuka ba yanzu,

"Nima kibani naki hoton"

"Bani da hoto" ta fada cikin damuwa, wayarshi ya ciro ya setata ya dauketa ahoton batare da yayi magana ba,

Mikewa tsaye yayi yana gyara zaman jakarshi akafadarshi,

"Baby girl bari nawuce,sai nadawo kinji,duk wanda yasaki kuka idan nadawo ki sanar dani"

Mikewa itama tayi tabishi tana yimasa addu'ar sauka lafiya,kamar bazasu rabu ba dan har wurin da zai samu mota ta rakashi.

Tun bayan tafiyar shi kuma saita nemi farin ciki da sukuni acikin zuciyarta tarasa haka ta daure ta sakawa zuciyarta dangana da kuma hakuri.

Zak's tun acikin ahanya suke waya da fu'ad yana sake jaddada masa wai ayi masa tanadin abinci dan da yunwa yadawo,me fu'ad zaiyi idan ba dariya ba,

Misalin karfe 1 saura na rana mai keke napep ya saukeshi a kofar gidansu yashiga,adaki yasamu fu'ad yafito daga wanka yana shiryawa,

"Kai.... Zaks kaga kuwa yanda kayi wani mashahurin baki? Gashi ka rame chaiii......."

"To taya bazan yi baki inrame ba alhalin bana samun abinci ina koshi....."

Daga haka ya wurgar da jakarshi yafita,kai tsaye part din momy yawuce,yana shiga kuma saman tabe yaje yafara bude bude,guntun abincin da akayi karin kumallo yagani abisa dukkan alama na rana bai sauka ba. Zama yayi yafara bawa cikinsa hakkinsa dama kuma baiko karya ba yau yataho,ahaka mommy tafito ta sameshi,

"Zakar...... Akan abinci aka sauka?"

"Ai kibari kawai mommy,da wata tsohuwar yunwata nadawo ne...."

"Ikon Allah,to ko baka samun abinci acan kana koshi?" Tafada cike da kulawa tana zama cikin daya daga cikin kujerun dake zagaye awurin reras,

"Mommy taya zanci abinci a wannan kauyen inkoshi? Kinga garin kuwa"

"To ka kara hakuri insha Allah wannan karon idan zaka koma zansa ayi maka yan dabaru, snacks da su dambun nama sai ka rinka ragewa...."

Shigowar fu'ad ce ta katse musu maganar da suke yi,shirin masallaci yayi bayan yaci ya koshi nan suka fita tare da fu'ad,a lokuta da dama yana jin dije tana fado masa cikin tunaninsa,da daddare kuwa hotonta ya tisa agaba yana ta kallo cike da tarin tausayinta. Washe gari wuni yayi adaki yana bacci sai yamma sannan yashirya yafita wani boutique yashiga domin yana son siyawa dije inner wears duk da bai san ta yanda zai bata ba amma yasan mutukar yasiya mata to ya taimaka mata, dozing din pants yadauka mata sannan yasoma duba bra duk da baida tabbacin size dinta amma dai yayi garajen zabar wasu wadanda yake ganin watakila za adace,

Boye boyen kayan yayita yi gudun kada fu'ad yagani daga karshe ma sai yabarsu cikin motarsa,gaba daya weekend bacci yake sha dama kuma yayi sa'a Daddy baya nan. Tun ana igobe zai koma kauye mommy tasa aka yimasa snacks da dambun nama kamar yadda ta alkawarta,washe gari takama ranar Monday kuma ranar ne zai koma,gaba daya yana cike da farin ciki tare da dokin ganin Dije, Allah sarki yasan itama yanzu haka tana can tanata zumudin ganin dawowarsa,

Tun bayan da suka shiga mota suka fara tafiya yaji zuciyarsa na bugawa sakamakon hirar da yaji wasu mutum biyu nayi wadanda ke zaune bayan kujerarshi,

"Kai jama'a wannan duniya ina zaki damu? Saleh kaji annobar da aketa fama da ita awasu wurare muma tashigo mana ko? Wai wannan yarinyar Dije aka samu yashe gefen hanya wasu samari sun yimata fyade......"

"Kai dai bari Mudi, wallahi naji,ai wannan abu ya munana kuma ya kazanta,ance jami'an tsaro sun zo sun shiga maganar ai....."

"Babu abinda zasu iya ai,da dai ba yayan masu garinne sukayi ba shine sai ace za adauki mataki"

Zaks bai iya jin karshen wannan tattaunawar tasu ba yadafe kansa da dukkan hannuwanshi guda biyu wanda ke barazanar tarwatsewa gaba daya yanemi nutsuwarsa yarasa ji yake kamar zuciyarsa zata buga.

SAƘON ZUCIYAWhere stories live. Discover now