SHAFI NA ASHIRIN DA HUƊU

1.1K 140 34
                                    

***Tamkar saukar aradu ko kuma wadda aka bugawa gudima haka taji kalamansa, hawaye na bin fuskarta jikinta na rawa ta sake rungumeshi ta baya, daidai lokacin fauza ta fito saboda ta farka sakamakon mafarkin da tayi na ban tsoro kuma abin mamaki sai bata ga zaks ba har cikin cikin toilet ɗinshi ta duba amma baya ciki shine ta fito kuma fitowarta keda wuya idanuwanta suka gane mata dije rungume da mijinta ta baya tana wasu kalamai masu ɗaure,

"Haba jarumina..... Aljannar duniya ta, duk tsawon lokacin da zuciya ta da gangar jikina suka shafe suna jimirin jiranka amma yanzu da wannan sakayyar zaka tarɓesu..... Kaine fa rayuwa ta, Kaine farin cikina kuma kaine jina da duk wani ganina.... Ban taɓa son wani namiji ba wallahi sai kai, ban taɓa son kasancewa da wani ɗa namiji koma bayanka ba.... Dan Allah karka juya min baya ka dawo gareni muje muci gaba da daddaɗar rayuwar da muka fara yi abaya.... Ka ɗanɗana min zuma a bakina sai da nagama zuwa har wuya sannan zaka janye? Wallahi kaine farin cikina..... "

Duk waɗannan maganganun tana yinsu ne cikin kuka da hawaye kuma har lokacin tana rungume dashi, fauza dake tsaye tana kallonsu ji suka yi ta fasa wata mahaukaciyar ƙara sannan kuma ta faɗi awurin cikin sauri da azama ya fincike dije daga jikinsa ya nufi saman da gudu, ita kuwa dije zamewa tayi awurin ta zauna tana kuka wiwi, duk jin ta take yi kamar acikin mafarki lallai wannan shine ga ƙoshi ga kuma kwanan yunwa, wai zaks ne ya saketa, tashi tayi duk da jirin dake ɗaukar ta haka ta lallaɓa ta shiga cikin ɗaki gaba ɗaya ta tattaro kayanta bata bar ko tsinke ba sai ko wayarta da ta faɗi anan falon ƙasa lokacin da taga zaks,

Tana hawaye ta ɗaga kai ta kalli upstairs ɗin su zaks sannan ta wuce ta fita, mai gadin yana kan benci yana ta sharar bacci ta buɗe gate ɗin gidan ta fice, tunda ta fito kuma bata haɗu da ko kare ba akan hanya har sai da ta kusa zuwa babban titi sannan ta fara hango abin hawa tsilla tsilla suna ɗan wucewa, kuka take ta yi ta hanyar zubar da hawaye banda jiri dake ɗaukarta kamar zai kada ita,

Tana kunno kai wata mota da aka sharota a guje tazo tayi watsi da ita shikenan daga nan bata ƙara sanin abinda ke faruwa ba sai buɗe idonta tayi ta ganta a gadon asibiti ana yi mata ƙarin jini sannan duk jikinta raunuka ne da daddaujewa ko ina sai raɗaɗi sai zafi da ciwo, hawaye na bin kumatunta ta buɗe idanuwanta ta kalli jinin da ake ƙara mata, babu kowa acikin ɗakin sai ita kaɗai dake kwance gaba ɗaya jikinta yayi tsami, wasu sabbin hawaye ne suka cigaba da ziyartar kumatunta. Cikin kuka take yin wasu maganganu wadda ita kanta bata san tana yin su ba,

"yanzu bani da wani sauran gata sai na ubangiji na, ɗan birni ya yaudare ne, bazan taɓa iya mantawa da kai ba, wai laifin me nayi maka? Menene laifina? Ashe jiran da na zauna ina yi tsawon shekaru biyar laifine? Ashe nemanka da na fito sakin aure na nafito nema da kaina? Wayyo Allah, wannan wacce irin ƙaddara ce take biye dani....... Na shiga uku.... Dan Allah ka tashe ni daga wannan barcin kace mafarki nake dan nasan ba zaka taɓa juya min baya har kayi min haka ba.... "

Ya jima tsaye a kanta yana sauraren duk maganganun da take yi waɗanda suka fi kama da sumbatu dan shi duk tunaninshi ta ɗan samu buguwa ne shiyasa yayi azamar fita yaje ya kira Dr wacce ita ce ke kula da ita,

" akwai abinda yake damunta kamar na tsoro ko firgici, shine ya taru ya haɗar mata da zafin ciwon da take ciki shiyasa kaji tana waɗannan surutan amma insha Allah ba wata matsala bace babba, ina drugs ɗin da nace ka siyo?"

"na je ATM machine ne sai yanzu na dawo, bari naje na siyo...."

"yawwa ka hanzarta saboda akwai wata allura aciki da zarar ka kawo za ayi mata"

"ok bari naje na siyo"

Fita yayi ya shiga pharmacy ya bada ƴar madaidaiciyar takardar da aka bashi mai ɗauke da sunayen magungunan da ake buƙata nan aka haɗa masa ya biya kuɗin ya fito ya sake komawa ɗakin da take, shi dai ya rasa meyasa yake tsananin jin tausayinta dan tun daren jiya ya kasa runtsawa saboda halin da take ciki, zama yayi gefenta yana cigaba da kallonta daga bisani ya miƙe ya fita yaje ya sanar da likita cewa ansamo maganin da tace yaje ya siyo. Duk wani motsinta akan idonshi ne sannan baya iya nisa da ita gadinta yake yi kamar wanda yake tsoron kar a sace masa ita, zuwa yamma ta farka daga baccin da ta wuni tana yi, hangoshi tayi yana salla wadda da alama sallar la'asar yake yi, hawaye tafara fitarwa babu ko ƙaƙƙautawa har yayi sallama ya zo inda take cikin sauri, dogo ne siriri fari kuma a haife ma bazai girme mata ba,

SAƘON ZUCIYAHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin