SHAFI NA GOMA SHA BAKWAI

912 97 9
                                    

***Tana goge hawaye ta shiga cikin gidan, indoriya na tsaye tana shanya tagama wanki, ganinta ta shigo tana goge hawaye yasa indoriya dafe ƙirji saboda tasan duk yanda akayi ba lafiya ba,

"Dije lafiya kuwa?"

"lafiya lau indo, ɗan birni ne ya tafi kuma inaji a jikina kamar bazai dawo ba....."

Ajiyar zuciya indoriya ta sauke sannan ta kama hannunta suka nufi cikin ɗaki,

"Haba dije ya zaki rinƙa faɗar irin wannan mummunar maganar? Ya za kice wai bazai dawo ba, dan Allah karki sake irin wannan maganar....."

"shikenan indoriya...... Bazan sake ba, Allah ya dawo dashi lafiya"

"amin, hmmmm su dije ansha giyar soyayya, dan Allah ya kika ji zuciyar ki a lokacin da kika ji cewa shine mijinki?"

Wani murmushi dije tayi wanda bata shirya masa ba, cikin jin daɗi ta gyara zamanta ta dubi indoriya,

"hmmmm indo kenan, ai bakina bazai taɓa iya sanar dake ɗunbin farin cikin da na samu kaina ba lokacin da ya faɗa min wai shine mijina..... Indo ban san da wanne baki zan godewa ubangiji ba domin shine ya cika min burina ya bani abinda nake so, ni kaina ban san irin son da nake yimasa ba "

" ya cancanci dukkanin Soyayyar ki dije domin shima yana sonki kuma ya kasance mai ƙaunarki tun kafin ya mallake ki, nidai abinda zan faɗa miki kawai shine ki riƙe masa amanar kanki da kuma soyayyarshi, karki bari shaidan ya ɗarsa miki wani abu game dashi har ki saɓa masa ko ki bijirewa umarninsa.... "

" insha Allah indo wannan shine abinda bazan taɓa aikatawa ba, bazan taɓa juyawa jarumi na baya ba insha Allah, zanyi masa dukkan biyayya sannan zan cika kowanne irin umarninsa"

Dariya indoriya tayi sannan cikin tsokana tace, "har ya nuna miki tasa jarumtar ne da kike kiransa da jarumi?" bata kai ga bata amsa ba taji ƙarar wayar da ya bata wacce ke ajiye a gefenta, ɗauka tayi kamar yadda ya koya mata tun wancan lokacin da ya bata,

"amincin Allah ya tabbata ga aljannar duniya ta....."

"iya aljannar duniyar ki kaɗai kike yiwa fatan aminci? Nikuma fa?"

"to ai da mamallakin ita zuciyar nake bawai ita kaɗai ba, nasan idan har aminci ya cika ta sannan ya ratsa kowanne sashe dake cikin ta zai isa har ga abin ƙaunata kuma abin bege na....."

"wannan zuciyar tawa kamar ta fini gata awurinki kar kisa infara jin kishi da ita....."

"Dama jarumin yana da kishi ne?"

"Baki taɓa ganin irin nawa salon kishin ba ashe ko?"

"shiyasa nake son jin yanda nasa salon yake yau"

Dariya taji yayi sannan cikin muryarsa mai taushi taji yace,

"idan nawa kishin ya motsa tsaf zan iya cireta daga kirjina in yar matsawar na gane ta fini fada awurinki"

Hannu tasa ta rufe bakinta alamar tsananin mamaki,

"Haba jarumi..... Bana fatan haka kuma bazan so hakan ta faru ba, ni ai mamallakin zuciyar nafi tsananin so"

"to ita kuma baby girl ya irin nata kishin yake?"

"hmmm ni ai duk ranar da aljannar duniyata tayi min kishiya da zuciyar wata daban to zan haɗiyi tawa zuciyar....."

Dariya taji yayi sannan cikin kulawa da lallaɓawa taji yace,

"no, wannan aljannar duniyar taki ai taki ce ke ɗaya, kin manta kince kin kulleta kin tafi da mukullin...."

"wai ni ban tambaye ka ba, ya hanya?"

"Gani tsaye ina jiran mota kuma kamar ma ga wata can na zuwa, bari na duba idan na sauka zan kira ki, ki kular min da kanki...."

Bai jira amsarta ba taji ya kashe wayar, daidai lokacin indoriya ta shigo ɗauke da ɗumamen tuwo, cike da mamaki dije ta kalleta,

" wai dama bakya nan? Yaushe kuwa kika fita? "

Dariya indo tayi sannan ta zauna akusa da ita,

" kina can duniyar soyayya, ai gani nayi gara inbaku wuri kar in zauna inji sirrin masoya masoyan ma mata da miji"

"hmm indo Wai dama haka miji yake da shiga rai? Wai dama haka Soyayyar miji take da ɗunbin tasiri a zuciya?"

"dije kenan, Meyasa zaki ga duk matar da mijinta ya mutu ake tausaya mata saboda mutuwar miji daban take, miji yana da wani muhalli keɓantacce mai girman gaske a zuciyar mace shiyasa shaƙuwarsa da ƙaunarsa daban take....."

"wallahi duk sai yanzu nake gane wannan karatun indo..."

Wuni guda tayi cur a gidan indo dan bata koma gida ba sai magriba, ƙiri ƙiri tana gani iya ta baiwa kowa na gidan tuwon dare amma ita kuma ta hanata sai fita tayi dandali ta siyo awara da rogo.

Zaks kuwa wurin azahar ya isa gida shida fu'ad wanda yaje ya ɗaukoshi daga inda mota ta ajiye shi, a gurguje yayi wanka sannan suka shiga part ɗin mommy , gaskiya babu abinda yakai gida daɗi domin jinsa yake yi kamar a wata sabuwar duniyar ta daban. Tunda suka shiga sashen mommy suke tare har yamma sai lokacin yasamu damar kiran wayar hannun dije amma bata tafiya, ɗan tsaki yaja aransa yana cewa "wannan shine ɗaya daga cikin illar rashin iya karatu da rubutu, da ace ta iya ai da yanzu zan iya sending mata text massage Amma yanzu ko na tura ma nasan nayi abanza mtswwwww"

"kai kuma kaida waye?" yaji muryar fu'ad yana tambayar sa,

"wallahi network ne ke bani headache inata kiran wani layi baya tafiya...."

"zuwa anjima sai ka sake trying, yanzu kazo muje dining..."

Tashi yayi yabi bayan fu'ad yana ƙoƙarin mayar da wayar tashi cikin aljihu, bai sake kiranta ba sai lokacin da yazo kwanciya bayan sunyi sallama da fu'ad kowa yashiga ɗakinsa, fitowarshi kenan daga wanka daga shi sai ɗan towel a wuyan shi bayan wanda ke ɗaure a ƙugunshi,jin tafara ringing amma ba a ɗauka ba yasa shi zama gefen gadon shi yana cewa,

"Ohh my God ko dai baby har tayi bacci ne...."

"Na ɗauka ai aljannar duniya ta tamanta dani da ta jita acikin yan uwanta"

Dariya yayi ya sake kishingida a gefen gadon,

"ta yaya wannan maganar zata samu ko gurbin zama bayan aljannar duniyar taki cike take da ƙaunar son jinki kusa da ita baya ga kewarki dake faman azabtar da ita...."

"duk kewar da take ciki bata kaini ba, ina kewarta fiye da yanda bakina zai furta, inaji kamar babu wani abu da yayi saura acikin duniya ta tunda har aljannar duniyata bata kusa dani...."

"karki damu ai kwana biyu kacal zanyi in dawo gareki...."

Har 12 suka kai suna wannan wayar abinda bata taɓa sanin zata iyaba wai waya da wani namiji har ƙarfe goma sha biyu dare lallai abin da ban mamaki, shi kam baya taɓa barin wata ƴar ƙofa da yasan fu'ad zai iya fahimtarsa komai ƙanƙantarta, washe gari kuwa tsadaddiyar laptop ɗinshi ya ɗauka da niyyar zuwa ya siyar domin biyan bashin kuɗin dije, dubu ɗari biyu aka siya sannan wanda ya siya ɗin ya tura masa kuɗin cikin account ɗinsa, daga can direct gida ya wuce, lokacin da yashiga part din mommy yashiga direct saboda yunwa yake ji, fu'ad ya gani tare da mommy tsaye cikin babban falonta da alama wata muhimmiyar magana suke tattaunawa, ganinsa sai gaba ɗaya kallonsu ya koma kansa cike da tuhuma gabansa ne ya yanke ya faɗi ras dan da alama kamar sirrin da yake ta ƙoƙarin binnewa tare da ɓoyewa zai bayyana koma ya riga da ya bayyana......

SAƘON ZUCIYAWhere stories live. Discover now