SHAFI NA HUƊU

1.1K 126 5
                                    


***Cikin kiɗima ta ɗaga kanta ta kalleshi jin tayi tuntuɓe da abinda bata san ko menene ba,shi ɗinma ita yake kallo duk fuskarta ta jiƙe da hawaye,

"Baby girl....... Me aka yimiki kike kuka? Ko yauma kunyi fada da itane?"

Girgiza masa kai tayi sannan tace "a'a"

"To meke saki kuka?"

"Babu komai......"  Tabashi amsa har lokacin hawaye bai bar fita daga cikin idanuwanta ba,

"Meyasa bakya zuwa makaranta?"

Shiru ta yi na wasu ƴan sakanni sannan tabashi amsa da,

"Ina son zuwa, iya mai maɗi ce bata son makarantar boko saboda wai lalata yara take su kangare sufi ƙarfin manya......"

Murmushi yayi ya ɗan shafi sumar kanshi,

"Wato mu da muka yi lalatattune kenan kuma kangararru?"

Girgiza masa kai tayi sannan ta ɗan durƙusa ta zauna,

Bai kai ga sake yin magana ba yahangi wasu ƴanmata guda uku ɗauke da kayan talle,ɗaya tana saida dafaffiyar gwaza ɗayar kuma dafaffen rogo sai ta karshensu tana saida soyayyiyar gyaɗa mai gishiri,kiransu yayi suka ƙaraso suka sauke kayan agabanshi sai kallon dije suke kamar yaune suka fara ganinta,

Rogon ne yabashi sha'awa saboda yanda yake fari tas sannan da gani zaiyi laushi gashi sai tururi yake yi duk yanda akayi yanzu aka saukeshi daga wuta,

Naira dari yaciro daga cikin wallet ɗinshi yasiyi rogon hamsin gyaɗar hamsin ga mamakinsa sai yagansu tuli guda dan tsaf mutum uku zasu ci su ƙoshi,

Ganin yaran sunƙi tashi sai kallon dije suke yasashi daure fuska sannan yace,

"Me kuke jira? Ku tashi ku tafi tallenku mumu..........."

Tashi suka yi kowacce ta ɗauki kayanta suka wuce ta tsakiyar tana taɓo ta farkon tana faɗin,

"Huwaila dama na faɗa miki dije ce,ko meya kaita tsayawa da wannan....."

"Kubarta bata san ƴan birni ba,pan birni fa yan iska ne"

Maida hankalinsa yayi gareta yana kallonta,

"Zo muci rogo....."

Duk da tana jin yunwa mai tsanani girgiza masa kai tayi alamar wai ta koshi,

"To ɗauki kici ki bar min tunda baza kici tare dani ba...."

Girgiza masa kai ta sake yi, ɗaure fuska yayi sannan yace "ɗauki kici nace"

Babu shiri ta ɗauka,abunka da mai jin yunwa tuni ta fara ci hannu baka hannu kwarya dama amutukar yunwace take,gaba ɗaya ma tamanta da yana wurin dan idonta yarufe saboda yunwa,

Shi kam tagumi yayi yana kallonta ko ƙiftawa bayayi,yasha ganin mata kyawawa kala kala amma bai taɓa ganin mai kyawunta ba, bai taɓa cin karo da wata mace ma'abociyar kyau da cikar halitta ba kamar ita, komai na halittar ƴa mace da ka iya ƙara ƙawata surarta ya bayyana agareta amma dayake wani abu sai ƙauye wai ganɗama ganɗaman ƴanmata haka suke yawo babu mayafi ko hijabi,idanma sun fito da mayafin sai su ɗaureshi a ƙugunsu suci ɗamara kamar waɗanda zasu yi dambe,

Saida tagama ci nutsuwarta ta dawo gareta sannan ta tuna a inda take kuma agaban wanda take,cike da kunya ta ɗaga kanta ta kalleshi nan suka haɗa ido akaro nafarko domin shi ɗinma ita yake kallo tun ɗazu,rufe fuskarta tayi cikeda kunya,

"Kin ƙoshi?" Taji ya tambayeta har lokacin ita yake kallo,

Kai ta daga masa acikin ranta tana yiwa Allah godiya domin duk lokacin da take cikin tsanani yakan aiko mata da sauƙi ta hanyar kawo mata ɗan birni da har yau bata san sunansa ba,

SAƘON ZUCIYAWhere stories live. Discover now