SHAFI NA UKU

1.1K 125 0
                                    

***Cikin shasshekar kuka ta daga kanta ta kalleshi sakamakon kamshin turaren jikinsa da ya mamaye wurin gaba daya haka kuma abangare daya zata iya cewa tunda take bata taba jin kamshin turare mai dadin wannan ba,

Wayarshi ya ciro daga aljihunsa saboda baya ganinta sosai wannan dalilinne yasashi kunna hasken jikin wayarsa yayi amfani dashi wurin haska ta, fuskarta caba caba da hawaye,ganin ya zuba mata ido yana kallonta sai abun yaso bata tsoro dan har tafara kokarin matsawa baya musamman da ta fahimci kamar bata sanshi ba acikin kauyen dan ko mai kama dashi bata taba ganiba,

"Baby girl......Meya faru dake kike yin kuka?"

Jin muryarshi da ta daki dodon kunnuwanta ai sai ta sake tsorata ta sake shiga rudu,

"Tsorona kike ji?" Ya sake tambayar ta shi kansa batare da yasan dalilinsa na nacewa har sai yashiga cikin al'amuranta ba,kai ta daga masa duk tayi tsuru tsuru alamun tsoro ya bayyana karara akan fuskarta,

"To ki daina jin tsorona kinji,nima yanzu dan garinku ne,dan uwanku,zan zauna tare daku har tsawon wani lokaci......."

Jin abinda yafito daga bakinsa yasa taji tsoron dake mamaye cikin zuciyarta ya dan kau duk da bai tafi gaba daya ba,k'ur yayi mata da ido ko kiftawa baya yi wanda bai san dalilin haka ba,acikin zuciyarsa yake kiyasta shekarunta wadanda aganinsa baza su gaza 19 ba zuwa 20,

Bai san abinda ta tuno ba sai gani yayi ta sake fashewa da wani sabon kukan,

"Ke....." Kukan me kike yi?" Jin tsawar da ya daka mata yasata toshe bakinta da hannunta ta daina kukan babu shiri domin zaks baya wasa idan yayi maka tsawa har saika gigice musamman ma yara,

"Buwalle ce bayan mun taso daga talle ta kamani da kokawa tasa na zubar da kudina kuma iya mai mad'i dukana zata yi sannan ta hanani abinci........."

Tunda tafara yi masa bayanin yake kallon dan madaidaicin bakinta har ta dasa aya,

"Wacece buwalle?" Ya bukata har lokacin yana tsugunne gabanta,

"Agidanmu take,sa'ata ce"

"Mamanku daya?"

"A'a ni babata da baba na sun mutu"

Dan jijjiga kai yayi alamar tausayawa yana jin wani abu yana sosa zuciyarsa,

"Nawane kudin?"

"Zobiya ne da fan goma"

Dan murmushi yayi yamike tsaye ya ciro wallet dinshi,garin ciro mata kudin NYSC ID card dinshi yafado bai lura ba,mika mata yayi,

"Gashi,amma ki daina zama a irin wurin nan kina kuka ke daya kinji,babu kyau,maza ki tashi ki tafi gida"

Kai ta daga masa sannan tace "To, nagode madallah Allah yasaka da alkhairi"

Har yajuya zai tafi yasake juyowa,

"Am meye sunanki?"

"Sunana Dije"

Murmushi yayi baice komaiba yatafi acikin zuciyarsa yana fadin ashe mai babban suna ce.

Ita kuwa dije tana kokarin daukar farantin ta bayan tafiyar zaks tayi kicibus da ID card dinsa akasa dauka tayi ta cusa cikin zaninta sannan ta dauki kayanta ta nufi gida aranta tana ta tambayar kanta to shi wannan bakon mai kirki a gidan wa ya sauka? Kodai gidan mai gari?, Ita dai Allah take ta yiwa godiya da ya bata mafita da yau Allah kadai yasan bakar wahalar da zata sha a wurin mai mad'i. Kamar yadda ta tsammata kafin taje gida tuni buwalle taje ta tsara karya da gaskiya, shiyasa lokacin da ta shiga gidan ta iske mai madi tana ta ruwan masifa tana jiran dawowarta,tana zuwa ba tambayar ba'asi ba komai tahau jibgarta,idan da sabo ta saba da irin wannan bakar muguntar da ake nuna mata kuma duk gidan babu mai kwatarta dan kamar kowa haushinta yake ji,yanzuma ga d'an marmari nan zaune yana sharbar tuwonsa na dawa miyar lalo amma babu abinda ya shalleshi da abinda yake faruwa,shine babban d'a agidan wato dai shine dan mai mad'i nafari.

Tana shirin kwanciya kan yar yagalgallalliyar tabarmarta taji abu azaninta koda ta taba sai taji ID card din zaks murmushi tayi tana mai yaba kirkin sa da kyawunsa sannan kuma gashi dan gayu dan birni,ko me yazo yi garin nasu oho,insha Allah gobe zata je ta nemi ta kai masa katinsa,ta raya hakan acikin ranta.

Rasa abinda yayi masa dadi yayi lokacin da yashiga dakin da aka bashi,sam baida sukuni gashi shi bai saba da kwanciya da wuri ba sai yakai 2 nadare baiyi bacci ba amma nan gashi ko 10 bata yiba kowa yashiga gida,"kai me za ayi da rayuwa irin wannan" yafada acikin ransa bayan yaja dan gajeren tsaki,

Fu'ad yakira duk da saida yasha wahala kafin ya sameshi domin rashin kyawun network,haka yayi baccin wannan rana cike da rashin jin dadi,washe gari sai da misalin karfe 9 sannan yatashi, abincin karyawa aka kawo masa koko da kosai ya dan daure yaci sannan yafita yana sanye da kayansa na bautar kasa amma babu hula,

Makarantar da aka turoshi wadda take kwallo daya dal acikin kauyen ita yaje yayi report sannan yafito,can gaba da makarantar kadan ya zauna kan wani gungumen icce dake kasan wata bishiyar kashu, Twitter yahau bayan ya dauki hotonshi zaune awurin yayi posting.

Tunda garin Allah yawaye yau dije take aiki itace debo ruwa itace zuwa yagar zogale banda sauran ayyukan gida gashi ko abincin karyawa bata samu ba domin kafin tadawo daga rijiya dan marmari yaje ya cinye dumamen nata,fita tayi daga gidan ita kanta bata san inda zata je ba domin wata irin wahalalliyar yunwa take ji mai rikitawa mutum lissafi,bata son taje wajen indoriya aminiyarta domin bata son dora mata wahala duk da cewa tare suka taso tun suna yara itama marainiya ce kamarta kuma ta azabtu wurin matar uba shiyasa suka hada kansu har Allah yabawa indoriya miji tayi aure ta auri idi magini,sau da yawan lokuta awurinta take cin abinci duk da ita dinma hannu bai cudi baya ba kawai rufin asirine,

Tana tafe tana share hawayen da yacika mata ido dan har bata ganin gabanta taji tayi tuntube da abinda bata san ko menene ba...................

SAƘON ZUCIYAOù les histoires vivent. Découvrez maintenant