SHAFI NA GOMA SHA ƊAYA

849 91 5
                                    

Yanda jikin buwalle ke rawa saboda tsantsar munafurci dake cinta tana alla alla taje gida takai rahoton da idanuwanta suka gane mata haka itama dije jikinta ke rawa yana kaɗawa kamar mazari. Lokacin da ta shiga gidan tuni har buwalle ta gama fesawa jama'ar gidan abunda ya faru na ganin wai da tayiwa dije da ɗan birni tsirara haihuwar uwarsu manne da juna,

Wasu hawaye masu ma'anoni da dama sune suka fara sintiri akan kumatun dije suna wanke mata fuska wato abinma dai harda ƙari da sharrin buwalle, yanzu shikenan ta san bata da wata mafita sai wacce Allahu subhanahu wata'ala ya kawo mata, zamewa tayi daga tsayen da take ta zauna zaman dirshan, yanzu gaba ɗaya ji take ta nemi rashin lafiyar da take yi ta rasa saboda tashin hankali, kowa ita yake kallo shiyasa tayi ƙasa da kanta tana ci gaba da hawaye tare da addu'ar neman mafita,

"munafuka....... Ai dole ki sunkuyar da kai, kina kai kanki ɗakin maza tirr dake dije, wallahi kin gama yin asara...... Me za ayi da haihuwa irin taki..."

"Ai mai maɗi bafa yau tafara zuwa ba dama can ta saba zuwa su haɗu suyi iskancinsu, sau nawa ina kama su a bayan gari suna yi....." Buwalle ta faɗa cikin sharri,

"Ke buwalle kiji tsoron Allah wall......"

"Ke...... Rufe mana baki shashashar banza shashashar wofi, abinda buwalle ta faɗa gaskiya ne domin ko abinda ke jikinki kaɗai ya isa ya sanar damu gaskiyar al'amari, kalli jikinki, meya haɗa ki da rigarsa matsawar ba iskanci kuka yi ba?" Kasa ɗaga ido ta kalli baba tayi jin abinda yagama faɗa ya sake tayar mata da hankali nan ta fara rantse rantse akan ita basu taɓa yin iskanci da zaks ba amma babu wanda ya saurareta, sunkuyar da kai tayi cikin takaici tana kallon jacket ɗinshi dake jikinta wadda take ta faman tashin ƙamshi kamar anyi ɓarin turare a jiki, ƙamshin dake sakata acikin wata duniya ta daban domin irinsa sak taji yana fita daga jikinsa a daren jiya.

  Shi kam zaks ko ajikinsa wai an tsikari kakkausa bayan fitar su dije sake lumshe idanuwanshi yayi sannan ya buɗe yana kallon gefensa inda ada dije take kwance, wayar da ya bata ya gani ta tafi ta bar masa, ɗan tsaki yayi acikin ransa yana ƙorafin wayar ma bata yi masa wani amfani ba tunda har yaje ya dawo bai ji muryar ta ba, tashi yayi yana kallon yanda gari yayi haske shaahh gashi ko salla bai yi ba wanda rabonshi da yin sallar asubah ba akan lokacinta  ba har ya manta saboda wannan horon daddy ne da kansa yake zuwa ya tashe su su fita masallaci komai sanyi haka kuma komai ruwa, tashi yayi yaje yayi alwala yana mai jin kunyar fuskantar ubangiji a wannan lokacin da sunan wai sallar asubah tunda yasan lokaci ya ƙure masa. Bayan ya idar da salla wuri yasamu ya zauna acikin ɗakin nasa ya harɗe hannayensa yana tunanin halin da ya jefa dije yau, ko shakka ba yayi yasan yanzu tana can tana fuskantar tuhuma da ƙalubale mai tarin yawa haɗi da horo mai tsanani domin ayanda yasan buwalle yasan harda sharri zata ƙara akan abinda ta gani, lumshe idanuwanshi yayi sannan ya ɗan kishingiɗa acikin ransa yana jin cewa duk runtsi ba zai taɓa barin dije ta fuskanci duk wani ƙalubale da rayuwa zata kawo mata ita kaɗai ba sai dai su tunkari kowacce matsala tare. Bacci ne yayi nasarar ɗaukeshi a wurin wanda bashi ya farka ba sai misalin ƙarfe 10 na safe, wanka ya fita yaje yayi sannan ya dawo ya shirya cikin ƙananan kaya na jeans da t shirt,kwanukan abin karyawar da aka kawo masa lokacin yana wanka ya kalla, sam baya jin zai iya koda shan ruwa a cikin wannan halin da dije ke can bai san me take ciki ba, wayarshi ya ɗauka ya fita bayan ya rufe ɗakin, gidansu dije ya nufa kai tsaye yana ta saƙawa da kwancewa acikin ransa,

Tunda ya shigo kwanar gidansu dije ya ke jiyo amon muryar sarkin noma da babansu dije tana tashi,

"Kar kayi mana haka sarkin noma, yarinyar nan tun ranar da ka ganta kace kana so na baka bai kamata yanzu kazo kace wai ka fasa ba a dawo maka da komai naka da ka bayar ba......"

"Malam jatau...... Na rantse maka da girman Allah bazan auri ƴarka ba na fasa, yarinyar da ta bada kanta tun a dandali...... Nan fa akace a ɗakin samari take kwana, wato saida samari suka gama buɗe mata ido sannan ni kuma za a lanjaro a lanjara min jaraba to wallahi bazata taɓa saɓuwa ba wai bindiga a ruwa..... A shiga a fito min da kaya na da kuma dukkan kuɗaɗena rankatakaf domin kuwa sisin kwabo bazan bari ba wallahi........ "

" Tun ɗazu sai cewa kake yi wai yarinya tana kwana a ɗakin samari, wanne munafukin ne ya faɗa maka wannan maganar?"

" Ahafff danma dai maganar daga gidanka ta fito malam jatau, koma dai menene nidai Allah yayi bani da rabon wahala bai yanka min kazar wahala ba bare inyi zaman figarta..... A shiga a fito min da kayana da kuɗi na idan kuma ba haka to na rantse hukuma ce zata rabamu, zan je wurin hukuma ta ƙwatar min hakkina ta dolen dole... "

Daidai lokacin zaks ya ƙarasa, tsayawa yayi yana kallon ikon Allah tare da kashe kunne dan jin meyake faruwa, maganganun da yaji suna fita daga bakinsu sarkin noma yaji abin yayi masifar ɗaure masa kai, take ya fara tambayar kansa,

" Aure? Baby girl za ayiwa aure? To ya akayi ni ban saniba? Meyasa bata sanar daniba?"

"Shikenan..... Ubangiji Allah ya kaimu ranar auren, na haƙura zan aureta ahakan, kasan ai ina sonta ya zanyi? Ai abinda zuciya keso dole abata shi sai a zauna lafiya....." sarkin noma ya faɗa yana wata irin dariya wacce shi kaɗai yasan ma'anarta, hannu yabawa malam jatau suka yi musabaha sannan ya tafi acikin ransa yana faɗin," malam jatau kenan da alama kamanta waye nomau sarkin noma, wallahi zan baka mamaki dan kuwa sai na tozartaka acikin ƙauyen nan, Allah dai ya kaimu ranar ɗaurin aure"

Zaks maida hankalinsa yayi ga malam jatau bayan tafiyar sarkin noma, ganin yana ƙoƙarin shiga gida yasa shi saurin zuwa ya dakatar dashi, a ɗage malam jatau ya kalleshi sannan cikin kakkausar murya yace,

"Shin ka sake biyota nan ɗinma ka ƙarasa lalatata?? Lalatacce nace nan ɗinma da wata lalatar ka zo? To wallahi ka buɗe kunnenka da kyau kaji, ƴata aure zanyi mata da kake hure mata kunne kake ƙoƙarin sakata a mummunan layi, kaga wancan wanda ya tafi to shi zan aura mata...... "

Ɗaga ido zaks yayi ya kalleshi sannan cikin ɓata fuska da shan kunu yace, " baba shi zaka aurawa ko zaka aurawa ɗansa? Wancan ai tsoho ne taya zai auri ƙaramar yarinya kamar ta? "

" Haka na gadama kuma haka nayi niyya, sannan kayi hanzarin bar min ƙofar gida tun kafin mu saka ƙafar wando ɗaya dakai...."

Baki zaks ya saki acikin zuciyar sa yana jin wani irin raɗaɗi da ɓacin rai, ji yake tamkar ya shaƙo malam jatau yayita jibga ko zai huce......

SAƘON ZUCIYAHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin