SHAFI NA GOMA SHA SHIDA

901 98 7
                                    

***Har zata koma cikin gida wata zuciyar tace mata tabishi tunda da alamu fushi yayi kuma fushin nan itace sila, fasa shiga cikin gidan tayi ta nufi gidan mai gari saboda da duk yadda akayi can ya tafi, ita dai addu'a take yi akan kar Allah ya haɗata da wani ko wasu su ganta, duk da mijinta ne amma bata son aganta tana zarya a ɗakinsa,

Ganin ƙofar ɗakin abuɗe shine ya tabbatar mata da cewa yana ciki, a hankali tayi sallama daga nan ƙofar ɗakin batare da ta shiga ba, saida yaja wasu mintuna sannan taji ya amsa daga haka bai ƙara ce mata komai ba, tsayuwa ta cigaba dayi a wurin zuwa ɗan wani lokaci jin bazai bata izinin shiga ba yasa ta nemar izini ta hanyar cewa,

"In shigo...?"

Shiru yayi mata taji bai bata amsa ba, gaskiya zakar yana da zuciya da zafin rai dan ta daɗe da fuskantar haka, idan ransa ya ɓaci tamkar zai yi me, duk da bai bata izini ba amma tayi garaje ta hanyar shiga cikin ɗakin, zaune ta ganshi kan katifa yagama shirya kayansa a jaka irin ta goyawa da alama tafiya zai yi, zama tayi kusa dashi suna fuskantar juna duk da baiko kalle ta ba lokacin da ta shigo cikin ɗakin,

"Dan Allah kayi haƙuri bazan sake ba....." ta faɗa a hankali kanta a ƙasa,

Jin baice komai ba yasata ɗago kanta ta kalleshi,

"Kayi haƙuri dan Allah kaji....."

"Naji...." ya faɗa batare da ya kalleta ba dan a maimakon hakanma wayarshi taga yaciro zai fara latse-latsen nashi na sabo, bata taɓa sanin tana da irin wannan ƙwarin gwiwar ba sai yau, jakar kayanshi dake tsakiyarsu ta janye ta matsar gefe sannan ta matsa gareshi sosai tare da riƙe wayar tashi, sakar mata yayi dan haka ta ɗora ta saman jakarshi, a hankali ta shige jikinshi tare da kai yatsanta ɗaya saitin zuciyarshi,

"Haba aljannar duniya ta ashe dama zaki iya fushi dani har haka? Akoda yaushe ina kuri ina tinƙaho cewar inada wurin laɓewa wurin da ake magance min kuka na ashe ba haka bane? Dake kaɗai fa na dogara baya ga ubangijina, dan Allah kar kiyi fushi dani yake zuciyar da babu irin ta....... "

Murmushi taji yayi tare da saka dukkan hannayensa guda biyu ya rungumeta bakinsa saman goshinta yana sunbata cikin yanayin so da rarrashi,

" Kar kiyi min kuka..... Amma daga yau ban yarda a saki abunda bai dace ba sannan kiyi, yakamata kema ki san ƴancinki da duk wani hakki naki, lokaci yayi da zaki samu ƴancin kanki tunda yanzu ke matata ce, ban yarda ayi miki duk wani abu wanda zai iya tozartaki ko ya zubar miki da mutunci kuma ki yarda ba, ban yarda ba, ko aikeni yanzu bake za a rinƙa aika ba..... Idan har kika yarda kika cigaba da zama asararriya zamu raba hanya dake..... Nafi son ki zama jaruma mai ƙarfin zuciya"

"Ai tunda babbar ƙawar tawa zuciyar jaruma ce to bana jin nima akwai sauran ragwanta acikin tawa zuciyar..... Insha Allah zanyi duk yanda kace sannan zan zamo fiye da yadda kake son in zama"

Murmushi yayi amma baiyi magana ba sai dai ta ji yayi kissing ɗin goshinta alamun yaji daɗin maganarta, daga kan zuciyarsa a hankali ta ɗauke hannunta tayi sama dashi zuwa kan gemunsa, dama yasan maganar gizo bata wuce ta ƙoƙi, yasan tun farko abinda take ta hari kenan, hannu bibbiyu tasa tana wasa da gemunsa shiyasa sai zamewa yayi ya kwanta yayi pillow da cinyarta yana jinta tana ci gaba da wasa dashi,

"wai ina zaka je naga ka haɗa jaka?"

Idanuwansa a lumshe ya bata amsa da,

"Zan je in nemo sadakinki in kawo miki abin ki ko kin yafe min?"

Kunya ce ta lulluɓeta shiyasa bata san lokacin da ta haɗa tasa fuskar da tata ba,

"Atoh idan kin yafe min shikenan sai inyi zama na infasa tafiya...."

"Na yafe maka...."

Ta faɗa tana sake ɓoye fuskarta, dariya yayi ya ɗan kalleta,

"To yanzu dai kin gama wasan in tafi ko da saura?"

"wai ina zaka tafi?"

"zanje gida amma kwana biyu zanyi kawai in dawo ko zamu tafi tare?"

Ta san tsokanarta kawai yake yi amma taya zai tafi da ita gida yanzu,

"kinyi shiru ko baza ki bini ba?"

"Ai bazaka tafi dani ba"

"waye ya faɗa miki?"

Ƙirjinsa ta taɓa da hannunta,

"ƙarya ta faɗa miki to"

"Ai bata yimin ƙarya, zuciyar ka bata taɓa yimin ƙarya ba"

"shikenan, tunda kin shaideta ta gode...."

Tashi zaune yayi ya buɗe wallet ɗin shi ya ƙirgo kuɗi ya miƙa mata "amshi kuɗin abincinki.... Zuwa lokacin da zan dawo, idan fita ta kama ki taki ta kan kanki nayarda kuma na amince miki kije duk inda kike so amma idan aikene ko talle or whatever da yashafi gidanku ban baki izini ba.... Kuma idan kika fita za a faɗa min"

Hannu biyu ta saka ta karɓa tana jin kamar ƙarshen haɗuwarsu kenan, ji take aranta kamar fa idan ya tafi bazai dawo ba, wannan tunanin shine yasata kuka harda hawaye shaɓe shaɓe tagumi ya rafka yana kallonta domin bai san dalilin kukan nata ba, zuwa can ya haɗata da jikinsa ya rungume yana lallashinta,

"ni dai dan Allah karka tafi.... Kaji"

"kwana biyu fa kawai zanyi in dawo baby girl.... Daina kuka, zamu rinƙa gaisawa awaya kafin na dawo"

Ita dai ba dan tana so ba ta haƙura ta yarda akan hakan, saida ta sake jagwalgwala masa gemu sannan tabari, ƙaramin cumb ya ɗauko ya bata,

"to gyara min intafi dama kece kika hargitsa shi..."

Cikin kunya ta karɓa tafara tattaje masa shi shikuma da wannan damar yayi amfani ya sake shigewa jikinta har ta ware damuwar dake tare da ita ta gushe, sai da ya tabbatar bata da sauran damuwa sannan suka fito tana ɗauke da jakarshi, sai yau ta yarda so yana makantarwa dan babu wanda take gani sai iya shi sau dayawa shine zata ji suna gaisawa da mutane ko yana yiwa wasu sallama wanda ita sam bata lura ma dasu sai idan taji magana, ƙofar gidan indoriya ya rakata dan acewarta gara taje can ta rage lokaci, jakar ta miƙa masa ya karɓa tare da riƙe hannunta, kissing hannun nata yayi sannan ya saki, wayarshi ƙaramar yabata sannan yayi mata sallama ya juya ya tafi, yanda yake tafiya yana waiwayenta haka take tsaye ƙyam tana kallonsa ƙwalla fal idonta har yayi mata nisa ta daina hangoshi..........

SAƘON ZUCIYAWhere stories live. Discover now