SHAFI NA ASHIRIN DA SHIDA

915 103 17
                                    

***
Tun bayan zuwanta asibitin da kwana biyu ta ɗan fara sakin jiki dashi domin yana da wasu ɗabi'u da halaye masu saurin shiga rai da dasa ƙaunarsa acikin zuciyar duk wanda Allah ya haɗa su zama tare, na farko yana da tsananin kirki ƙololuwa, yana da yawan tsokana sannan kuma shi mutum ne da yayi riƙo da addininsa dan sam baya wasa da ibadarsa musamman ma salla shiyasa cikin kwanaki biyu zuwa uku tafara sabawa dashi sannan kuma ta ɗan saki jiki dashi, shine yake ta faman ɗawainiya da ita kamar wani ɗan uwanta na jini. Kamar koda yaushe yau ma fita yayi ya siyo mata abinci tuwon shinkafa da miyar agushi, tana zaune agefen gadonta tayi nisa a karatun da take yi a wayarshi inda take karanta wani littafi na hausa wanda marubuciya ummi A'isha ta rubuta mai suna kamar da wasa, ita kaɗai take dariyar dramar fahad da mai gado, ajiye ledar take away ɗin dake hannunshi yayi sannan cikin murmushi yace da ita,

"princess da alama kina jin daɗin wannan labarin da kike karantawa...... Amma kin yi sallar azahar ɗin ko?"

"Ka jika, sau nawa zanyi sallar? Agabanka fa nayi kafin ka fita"

"Ohh anyi haka, mantawa nayi, sorry, to yanzu ga abinci....."

Ɗan yatsine fuska tayi sannan ta ajiye wayar shi dake hannunta agefenshi,

"nifa a ƙoshe nake jina ma"

"ki ci ki ƙara jin ƙarfin jikinki dan zuwa anjima kaɗan za a sallamemu....."

Ras! Taji gabanta yayi wata mummunar faɗuwa domin idan aka sallameta bata san inda zata dosa ba kuma saboda ita dai ba zata koma ƙauyensu ba har sai tare da mijinta wannan alƙawari ne da ta yiwa kanta, dama asali zaks tafito nema kuma ta ganshi sannan ga yanda abu ya kasance dan haka babu buƙatar ta sake komawa ƙauyensu,

"wai dan Allah tunanin me kike yi? Ba anhanaki tunani ba?"

Ɗan firgigit tayi sannan ta kalleshi, "waye ya hanani tunanin?"

"ni mana....."

Dariya tayi tare da jan take away ɗin tafara ƙoƙarin buɗewa, ɗaya ta ɗauka sannan shima ta miƙa masa,

"Ka ganka kana abu kamar wani wanda ya kwana biyu a duniya....."

Murmushi yayi bayan ya buɗe take away ɗin yafara ci,

"wannan yarinyar na fuskanci tun ranar da nayi suɓul da bakan sanar dake shekaru na ki ka fara ganin damata....."

Dariya tayi bayan ta ta kai laumar tuwo bakinta, "wai yarinya, to wallahi ka daina cemin yarinya dan ba girmata kayi ba, idan aka bi diddigi ma nice na baka wasu ƴan watanni"

"haba haba, babu wannan maganar wallahi, ki kalle ki kamar wata jaririya sannan ki haɗa kanki da ni? Allah na girmeki ko babu yawa...."

"da wata ɗayan zaka rinƙa nuna wannan girman, wata ɗaya ne fa...."

"Naji dai, koma kwana ɗaya ne dai ai nafiki, kuma dole ace da mijin iya baba"

"babu maganar dole anan, sai an gadama dai"

"baki taɓa soyayya da age mate ɗinki ba ko? Shiyasa baki san daɗin ta ba, amma yanzu tunda gani zaki ga yanda ake soyayya da mate ɗinka, ita tafi kowacce daɗi"

"ni wallahi dariya kake bani idan naji ka faɗi haka"

"Ai banma baki dariya ba sai ranar da kika ganni da babbar riga bayan an ɗaura mana aure da ke...."

Dariya ta fara yi harda su ƙwarewa, shi kam abincin nasa ya rufe ya tashi ya fita yabarta tana ƙarasa cin nata abincin, bayan kamar mintuna 15 ya dawo tare da likita, sake duba ta yayi sannan yace zasu iya tafiya, fita ya ƙara yi sannan ya dawo riƙe da takardar sallama, kayanta ya haɗa mata da ba masu yawa ba sosai sannan sai kayan ciye ciyenta da yake siyo mata, tare suka fito yana rike da kayan ita kuma tana riƙe da wayarshi da takardar sallamar da aka basu tana duba uban kuɗin da ya biya dan kuɗin gado ma kanshi iya shi kaɗai dubu talatin banda na nagani da sauran tsarabe tsarabe irin na asibiti, gaban motar ya buɗe mata ta shiga,

SAƘON ZUCIYAWhere stories live. Discover now