40

892 39 11
                                    

🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗

*RAYUWAN NAJWA*

🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗️

*WRITTEN*

*BY*

*AYSHA ISA (Mummy's friend)*

*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*

_____________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*LITTAFAN MARUBUCIYA*

_*1. Na Tsani Maza*_

_*2. Meke Faruwa (labarin Amira)*_

_*3. Ruhin 'Dana*_

_*4. Illar Rik'o ( 'yar rik'o)*_

_*5. Shi nake so ( labarin Fusailah)*_

_*6. Bani da laifi ( bayin kaina bane)*_

*DEDICATED TO:*

_*Zaman Amana Asso.*_

*ALL MOST TRUE LIFE*

*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM*

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

*Page 40*

Najwa ce ta fito ɗaki sanye da hijabin har ƙasa, ƙarasowa tayi falon inda Habibah ke zaune bakin ta ɗauke da sallama. Amsawa Habibah tayi fuskantar ɗauke da murmushi, a zuciyarta kuma faɗi take " Masha Allah, dole Doctorna ya ruɗe, don gaskiya wannan kyan ba a baya ba..."

Gaidasawa suka yi daga nan kuma duk suka yi shiru, jin shirun ta yi yawa Najwa ta ce " ƴar uwa ni kuwa ban gane ki ba."

Murmushi Habibah ta yi haɗa da miƙewa, kusa Najwa ta koma ta zauna sannan ta ce " nasan dama bazaki gane ni ba, sunana Habibah matar Dr. Sufyan."

Ras Najwah taji gabanta ya faɗi, duƙar da kai tayi ƙasa tana wasa da zoben dake ɗan yatsun ta, " Ya Allah see me through, ko dame kuma ta zo?" Najwa ta ce a zuciyarta tana mai rintsa ido, riƙe hannunta da Habibah ta yi ne yasa ta buɗe idanuwanta, amma har yanzu ta ƙasa ɗago kai ta kalleta domin ita gani take bata kyauta mata ba duk da dai bata amshi tayin nasa ko ba.

"Nasan zaki yi tunanin abinda ya kawo ni ko?" Habibah ta ce, shiru ta yi tana jiran amsar Najwa, jin Najwan ta yi shiru bata ce komai ba yasa Habibah ta ci gaba da magana ta ce " komai bane illa alfarmar dana zo nema a wurin ki, Najwa ina rokon ki don Allah ki yarda ki auri mijina, Najwah tunda mijina ya fara nemanki ya rage wasu abubuwa da yake min a matsayin mata, tun yana ƙoƙarin ɓoye min har dai nazo na gane dalilin canji nasa, hakan yasa na tada ɓalle, kullum cikin faɗa muke dashi, wanda ta sanadiyyar haka yasa bai fiye zama gida ba,  indan ba zaki manta ba a lokacin da kuka yi zama asibiti yakan daɗe tare daku yana hira. Sai kwatsam aka yi masa transfer, a lokaci ba ƙaramin farin ciki nayi ba. Kwana biyu ya yi a can bayan ya yi reporting ya dawo nan don ya sanar dake manufarsa a kanki, yazo ya tarda an riga an sallame ku, babu yadda bai yi ba ya samu gana dake amma abin ya ci turo, har abin yaso taɓa shi, haka dai yazo ya haƙuri ganin ba yadda zai sameki.  Sai kwatsam few months back naji ya ce kin dawo wanda yayi sanadiyar komawar mu gidan jiya. Najwa ina rokon ki, ki duba girman Allah ki amshi ƙoƙan barata, ki amince mijina ya aureki, ta hakan kawai ne zai dawo min da farin cikin gidana kamar da, please Najwa" Habibah ta ƙarasa magana cikin magiya.

Ajiyar zuciya Najwa ta yi ta ce " Ok, amma ki bani lokaci zan yi tunani a kai."

"Nagode, Allah yasa naji alkhairi" Habibah ta ce cikin sanyi murya. Daidai wannan lokacin Nusaiba ta buɗe ƙofan falon bakin ta ɗauke da sallama, rufo ƙofar ta yi ta ƙaraso ciki, yayin da  ita kuma Ummita ana buɗe ƙofar ta ruga a guje, kan cinyar Najwa ta hau tana nuna mata chocolate dake hannunta " Mummy kinga Uncle Mahmoud ya siyan min choco."

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 02, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

RAYUWAN NAJWAWhere stories live. Discover now