17

500 39 0
                                    

🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗

*RAYUWAN NAJWA*

🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗️

*WRITTEN*

*BY*

*AYSHA ISA (Mummy's friend)*

*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*

*LITTAFAN MARUBUCIYA*

_*1. Na Tsani Maza*_

_*2. Meke Faruwa (labarin Amira)*_

_*3. Ruhin 'Dana*_

_*4. Illar Rik'o ( 'yar rik'o)*_

_*5. Shi nake so ( labarin Fusailah)*_

_*6. Bani da laifi ( bayin kaina bane)*_

*DEDICATED TO:*

_*Zaman Amana Asso.*_

*ALL MOST TRUE LIFE*

_*Your heart decide who you want in your life....*_

_*Godiya gareku masoyana bisa k'aunar da kuka nuna min, thanks dearies I really appreciate.*_

_*Tawan @ Bk gani na taho gareki, thanks for caring dear I really appreciate.*_

*Page 17*

Knocking Aisha ta hau bayan ra isa gun amma shiru ba'a bud'e k'ofar ba, murd'a handle din k'ofar tayi a hankali taga ya ya bud'e, ajiyar zuciya tayi sannan ta kutsa kai cikin d'akin, turus taja ta tsaya ganin yanayin da suke ciki.

Jin taku mutum da Usman yayi ne ya sanyashi rabuwa da Najwa, gefe ya koma ya tsaya ba tate da kallon inda Aishan ke tsaya ba don wani irin haushinta ya ta turmuke zuciyarsa, d'an guntun tsaki yaja had'e da fuzar da iska mai zafi yana mai takaicin faruwan hakan.

Ita kuma Najwa tana saketa ta, ta sauke nauyayen ajiyen zuciya, sai dai kunya ya hanata tab'uka komai wurin ta tsaya kamar statue.

Murmushi yake Aisha idanuwanta taf da kwalla tsabar takaici " kuyi hak'uri fa " tace kannan ta juya tba..." Aisha tace cikin sheshank'an kuka.

"Wallahi aunty ba abinda kike tunani bane, amma kinyi hak'uri don Allah."

"Don ki daina bani hak'uri Najwa, sai kace wacce ta aikata wani laifi keda mijinki..." Aisha tace cikin murmushi wanda bai wuce lab'e ba.

"Eh nasani mijina ne amma ai hakan bai kamata ba, kuma Allah baice haka ba, sai dai yarda da amincewarki. Wallahi aunty babu abinda ya faru illar wannan da kika gani..."

"Hmm! Najwa kenan babu komai , in ba don zuciya da bata da k'ashi ba bai ci ace wannan ya daman ba don Usman ba bako na bane amma da yake zuciya ba k'ashi gareta, kuma kishi yazama dole shiyasa. Koma meye Najwa ni na yafe" cewan Aisha.

"Nagode aunty, nagode da kika fahimceni, Allah ya karemu daga sharrin shaid'an, ya d'orar da zaman lafiya tsakaninmu."

"Ameen Ya Rabbi " cewan Aisha sannan ta koma ga kwanciya.

Saida safe Najwa tayi mata sannan ta mik'e ta fice daga d'akin ta nufa d'akinta. Rufo k'ofar Aisha tayi bayan fitan Najwa ta gyarawa Sadiq da Nasir kwanciya tayi sannan itama ta kwanta daga gefensu. Lula tayi duniya tunani tana jin yanda zamansu zai kasance idan hakan ya cigaba da faruwa don zuciyanta bazai iya d'auka ba.

Itama Najwa tana isa d'akin ta rufo k'ofarta, kan gado ta fad'a tana mai takaicin wannan abun da yafaru, hawaye na zuba kan kuncinta. Addu'a take a ranta kan Allah ya yaye mata wannan tsanar da take ma Usman d'in.

B'angaren Usman kuma haka ya kwana shi kadai don Aisha k'in komawa tayi. Tsaki kam yaja shi yafi a kirga gashi babu halin biyota d'akinta don yara, itama Najwan babu halin zuwa d'akinta don ba kwanarta bane. Haka dai ya rik'a juyi don yakai mak'ura har daga bisani barci yayi awon gaba dashi.

RAYUWAN NAJWAWhere stories live. Discover now