18

525 37 0
                                    

🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗

*RAYUWAN NAJWA*

🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗️

*WRITTEN*

*BY*

*AYSHA ISA (Mummy's friend)*

*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*

*LITTAFAN MARUBUCIYA*

_*1. Na Tsani Maza*_

_*2. Meke Faruwa (labarin Amira)*_

_*3. Ruhin 'Dana*_

_*4. Illar Rik'o ( 'yar rik'o)*_

_*5. Shi nake so ( labarin Fusailah)*_

_*6. Bani da laifi ( bayin kaina bane)*_

*DEDICATED TO:*

_*Zaman Amana Asso.*_

*ALL MOST TRUE LIFE*

_*Happiness belongs to those who always think good of others & pray for  all. May our souls be purified,  may we always think good of others, so as to remain forever happy. (Ameen)*_

_*Aunty Samira this chappy is for  you nd you alone,  kiyi ynda kike so dashi ba me ce maki don me.*_

*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*

*Page 18*

Haka zaman ya koma na kurame don tunda Ummi tayi Najwa take ta kumbure-kumburenta, ko ta kanta Ummi bata bi ba daga k'arshe ma tashi tayi ta wuce d'akinta tayi kwanciyarta. Duk sai Najwa taji babu dad'i,  zaman ta gundureta gashi Nusaiba sarkin surutu ta tafi islamiyya balle ta rage mata wannan zaman kadaicin, "mtsw " taja d'an guntun tsaki , wai sbd wannan k'addarar auren shine Ummi ta canja mata, gsky  ita kam an cuceta "wannan shine a dakeka a hanaka kuka, babu abinda zance ga Usman sai dai Allah ya sakamin" ta k'arasa zancen a fili don da duk zance zuci take. Wayar ta dake gefenta ta d'auka tayi dialing number Rumaisa,  ta kira kusan sau uku amma bata dauka ba,  haka ta hak'ura itama,  mik'ewa tayi ta nufi d'akin da tayi zama a lokacin tana gida tayi kwanciyanta tana buga game a wayanta. Wayar da take hannunta ne ta soma ruri "mtsw" taja tsaki ganin Rumaisa ce ke kiranta,  k'in d'auka tayi saida itama Rumaisa ta kirata kusan sau biyu a na ukun ne ta d'auka.

"Assalamu alaikum! Kinga daman d'auka?" Cewan Rumaisa

"Wa alaikumussalam! Sai na katse abuna" kwafa Najwa tayi sannan ta k'arasa zancen da fad'in " 'yar raini hankali kawai."

"Hhh! Yi hak'uri..." Rumaisa tace tana dariya.

"Nayi ba don halinki ba" cewan Najwa.

"Toh nagode,  amma gaskiya wannan babyn yasa duk kin zama masifaffiya."

"Fad'i kawai zaki kai tsaye kice na zama masifaffiya ba wai ki fake da wani babyba. That aside kina gida?" Najwa ta k'arasa zance da tambaya.

"Eh ina gidan hala kin shigo anguwar tamu ne?" Cewan Rumaisa.

"Eh yanzu haka ina gidan don na kusan awa a nan anguwar,  amma I tot kina islamiyya ne don naga ba'a taso ba ko" Najwa tace.

"Wallahi yau banje ban bana jin dad'in jikina ne shiyasa."

"Subhanallah! Sannu meke damunki ne?" Najwa ta tambaya cike da kulawa.

"Malaria ce kimanin sati guda kenan ina fama, amma Alhamdulillah da sauki yanzu tunda ina sha magani" cewan Najwa.

"As alullahil azeem,  rabbil arshil azeem,  aiy yashfik...." cewan Najwa.

"Ameen nagode,  zaki shigo ne?"

RAYUWAN NAJWAWhere stories live. Discover now